← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 89

Sashe 8

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Duk da shakkar da takeyi amma ta dake, Sir,... Sae kuma ta kasa ce masa komae, Jin shirun yae yawa yasa yace "Zainab idan bakida abin cewa tou dan Allah ku tafi kuban guri"
Sae tae saurin fadin "sir, da'ma alfarma naxo nima" duk da yasan me bakinta ke shirin furtawa bae hana shi tmbyrtaba, "alfarmar me knn Zainab?
Sae tace," inaso ne ka taimakeni kamin nawa test din don Allah karka cemin a'ah plss sir"
Kauda kae yayi daga kallon dayake mata yace "Zainab am sorry" baxan iya makiba sabida ba ke kadai bace baki rubutaba, kuma idan na maki ke kadae na yaudari kaena, this is not the first time dana fara advising dinki da kidaina xuwa late Amma kinkiji ynxu wa gari ya wa'ya, hawaye ne keta bin kuncinta ya tausaya mata kasancewar sa mutum ne wanda yakeda tauheed Amma baeda daman mata, aikinsa yake kan gsky,so indae yae mata baewa sauranba baeyi adalciba, ynxu kinga ranar xuwa sch da wuri, jiki ba kwari suka fita daga office din
Suna fita maryam tace "afeefah anya yau lecturan nan lfyarsa lau kuwa?, afeefah da bakin ciki ya gama rufeta tace" kalau yake, maybe yau mulkinsa ta lecturorine ya tashi sae wani babbatsewa yake", maryam tace " a'ah afeefah inaganin dae an bata masa raene don wlh bawan Allah nan yanada mutunci, ki tunafa idan bakixo da wuriba saeya rambayeki dalilin rashin xuwanki da wuri, afeefah ta yamutsa fuska tace" yo ai bani kadai yake tambaya ba duk wanda yaxo late saeya mashi tambayar ", Oho dai koma miye yanadai tambaya" cewar maryam , kawai dae inaga sun sami matsala ne da matarsa
Da sauri afeefah ta juyo
Mata? Ke ynxu wannan yai maki kama da mai aure, maryam tace dalla matsa mi kika sani game dashi bare kisan yanada aure ko baida
Afeefah tace ke inafa jin yanda yammatan sch dinnan ke bibiyarsa, suna cewa gashi gaye har gaye Amma bayyida mata, Sam mata basu gabanshi a halin yanxu, don haryau baisami macen da tadaace da rayuwarsaba, afeefah tace maryam mubar gurinnan, masallaci suka nufa sunyi kusan minti talatin sannan maryam tace ke nifa ko ruwa bansha ba nafito don haka tashi xakiyi muje kirakani, cafeteria suka wuce don ya xama joint dinsu, lipton tace a dafa mata sae indomie da kwai plate daya, bae bata lokaci ba wurin kammala mata ya kawo mata, tana kurba so daya call din *Ahmad*ya shigo, da sauri ta ajiye cup din ta dauki wayar, cikin yar siririyar murya tae sallama, soyayya suke ynda kasan suna kusa da juna, bangaren afeefah kam mamakin maryam kawae takeyi ynda taga cikin dan kankanin lokaci ta sauya murya sae rangwada takeyi tana kashe murya uwa tana gabanshi, saeda ta kammala wayanta tsaf sannan ta dubi afeefah wacce har lokacin kallonta takeyi
Maryam tace "ke lfy irin wannan kallon hka, yau aka fara soyayya a gabanki
Afeefah tae murmushi tace" ai dole inkalleki irin wannan karairaya kamar kina kusa dashi, kuma batun soyayya a gabana ban taba ganin anyi ba saeyau, sanin kankine Abba bae barinmu kula samari ballantana har mukaega hira dasu
Taaap! Ki tsaya kallon ruwa kwado ya maki k'afa, sae kin gama sch ki rasa mijin aure, ba gara ka kama dahir ba ana kammala sch din sae aure, amma saekin gama sch ne xaki fara kula samari, kinada aiki babba a gabanki
Ummm! Nidae mubar wannan maganar, kici abincinki mu kara Wuta, tana kammala wa suka koma masallaci don yin sallah, karfe biyu xasu koma class
Tou haka dae suka gama da lectures din ranar
Misalin karfe 9 na dare ta kira yayanta, saeda ya katse baidaukaba sannan ya kirata back

Eeshatullah Goni 😘😘

🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 🌸👩🏻

A true life love story

By Ashmaad

13.....

Sallama tae cikin muryar shagwaba, shima cikin tattausan lafaxi ya amsa
Yaya nayi fashi dakae tunda baka nimeniba throughout,
Murmushi yae kamar yana gabanta
Haba my little sister, kina raina, bandae sami tym din kiranki bane coz aiki yamin yawa,
Tou shikenn yaya, ya aiki?
Lfy lau afeefah, hope kina kulamin da kanki
Sae ta tabe baki "hmm! Ai dole yaya na"
Yaya kasan me?, yace Mata saekin fada
Yaya lecturan nan.... Bae bari ta karasaba ya katseta da tsawa saeda ta kauda wayar daga kunnanta sabida kara
Zainab! Zainab!! Zainab!!! Kinji na kiraki sau uku, wlh idan baki fita hanyar lecturoriba sae ranki yae mugun baaci, uban me ya kuma hadaki dashi
Gabaki daya jikinta yai sanyi, yaya Aliyu sanda naje sch ne na tarar da yabada test harnae missing banyi ba shine na Bishi in bashi hakuri yamin
A fusace yace "meya hanaki binshi gida ki bashi hakurin" Mahaukaciya wlh idan baki fita harkarshiba saena hadaaki da Abba, ince masa kin fara tara samari sai muga karyar iskanci
Haba yaya wlh bbu abinda ke tsakaninmu, hasalima koda nabishi ceman yai baxaiminba tunda ba nikadai bace banyi ba
"oho dae na fadamaki wlh ki kiyaye tunda test din ba na barin duniya bane" kinajina?? A tsawace ya fadi, hawaye kawai takeyi tace "naji yaya na daina"
Yace "good girl", so gayamin mai kikaci a sch yau, tace yaya ba abinda naci sabida banji yunwa ba, ya kuma tambayrta taci abinci dare? Sae tace masa "a'ah banjin yunwa"
So kike muyi fada ko? Matukar bakiso muyi fada to kije kici in yaso na kiraki anjima, tou kawae tace masa ya katse wayar
Kitchen ta shiga ta hada tea mae kauri sannan ta koma daki, wayar jiddah ce ta soma ringing bugu biyu tae ta dauka ganin wacce ta kira, sunan aunty nusaibah ne yae appearing
Auntyna ta kaina ina yini ina gajiya??, bayan sun gaisa take tambayrta Sadiya da afeefah,tace gasu kusa dani, sai tace a sata a hands free, hakan tae kamar yadda ta umur ceta, my one and only sister cewar aunty nusaibah, afeefah najin haka tasan da ita take, haba aunty ai fushi nake dake, yaushe rabanki da kirana kiji yadda nake
Lallaima afeefah ae gabaki dayanku kallonku nake, bbu wacce tace bari taxo tamin kwana biyu ko xuwa ma ynxu kundainayi
Sadiya ce tae mgn "kema aunty kinsan baccin skul bbu abinda xai hanamu xuwa gidanku"
Jiddah tace "insha Allah muna samun hutu xaki ganmu duka kafinnan kinga su *Rahma* sun dawo hutu saimu barsu da ma'mi mu kuma muxo gurinku keda aunty safiya
Aunty nusaibah tace tou Allah ya kaimu..... Ina labarin samarinku? Gabaki dayansu suka xaro ido," samari kuma aunty? "dukkansu suka hada baki, rufamana asiri karkisa Abba yaji yae tunanin munada su
Dariya tai sosae tana fadin" Munafikai nasan is hardly kuce baku da samari saedae kuce bakuda daman tsayuwa dasu
Afeefah tace "sister wlh nidaikam bandashi Amma su ki tuntu6esu baxasu rasaba, Sadiya tace" halan ke kika mana samarin ", jiddah kam sai kifta Mata ido take
Aunty nusaibah tace" Saekunyi hakuri Abba nada matukar tsauri inba haka ba aeda tuni Kuna taad'ih, baccin adnaan wlh da kunyi abunku a boye ina dalili
Afeefah tace "kedai aunty hakanan xamu ququta mugama mubishi a yanda yakeso", tou shikenan Allah ya xaba mafi alkhairi cedar nusaibah, duk suka ansa da "Ameen" nan tae masu sallama ta katse wayar
Da misalin karfe goma na daren Kiran yaya Aliyu ya shigo, yaeta ringing ba'a daukaba don lokacin tae nisa a bacci

Eeshatullah Goni 😘

🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸

A true life love story

By *Ashmaad*

14......
Chapter 8 · 0% Book details