← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 89

Sashe 14

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washegari da safe Afeefah ta je gaida Abba bayan tayi shirin sch kmr ynda suke yi duk safiya, xaune ta tadda duk yan gidan a falon Abba bnda Mami da ya Aliyu, ta xauna gefen su bayan ta gaishesa ya amsa fuskarsa a daure, Mami ce ta shigo snn ya Aliyu, Afeefah ta ki bari su hada ido da ya Aliyu, sae wasa da fingers dinta take, sunanta taji Abba ya kira, ta dago kai da sauri yace "Wani lecturer ne a sch kike xuwa office dinsa yake baki abu ki ci?" Xaro ido tayi a tsorace tana kallonsa, Abba ya daka mata tsawa "ba magana nake maki ba kike kallona hka, meye tsakanin ku, kuma a ina kika san shi? Kin mance doka na ne" Kuka ta fashe da tana kallon Aliyu da ya wani hade rae, Abba ya mike a fusace yace "au kuka xa ki yi min don kaniyar ki don ban sa an xane min ke ba?" Sunkuyar da kai tayi ta hadiye kukan da sauri, Abba yace "today shud b d first nd last day da za ki sake kula lecturer a sch, na hane ki da sake kula ko wani namiji a makaranta, hka kika ga yayyinki suna yi, to na sake jin hka sae nayi mugun Saba maki wllh, tashi ki ban waje sha shasha kawae" mikewa Afeefah tayi da sauri ta fice daga falon da gudu. Abba ya juya kansu Jiddah yace "ku kuma ban ga amfanin ku ba a tare, ku tashi ku ban waje" sum sum suka fice daga falon su ma.

Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸

A true life love story

By *Ashmaad*

Dedicated to my kawalliya romon jaa6a(khaleesat haiydar) 😘😘

20....

Afeefah bata yi wani break din kirki ba tsabar kukan dake cin ta ga shi bbu daman yi, Mami da ya Aliyu na falo, bbu abinda take sae jujjuya Fork din hannunta, Da kyar ta iya yi ma Mami sallama don har wani rawa muryarta yake, ya Aliyu kam ko kallonsa bata yi ba, driver na barin gidan ta rushe masu da wani matsanancin kuka cikin mota, Driver yyi parkin da sauri yana kallonta da mmki yace "kai! me ya faru" tsaki su Jiddah suka yi suka ce "Da' alla baba mu je iskanci ne kawae" har suka isa makaranta bbu Wanda ya kalli inda take, Duk suka nufi faculty dinsu, ita ma ta nufi faculty dinta, Bakin lecture Hall ta ga Maryam tsaye suna magana da wasu yan ajinsu, Maryam ta saki baki tana kallonta har ta karaso snn tace "Ni kam kina bn mmki Afeefah, bbu ranan da xae wuce baxa ki yi kuka ba, kukan ma mara reason? Haba ki dinga maintain mana, ke fa ba yarinya bace don Allah ki bari, ni baxan boye maki ba gskya haushi kike ban, abu kadan kuka kmr wata yar shekara uku" tabe baki tayi ta ci gaba da xancenta da yan matan ajin, Afeefah tayi tsaki ta bar wajen ta koma karkashin bishiya tayi xamanta. Har lecturer su ta iso Afeefah bata shiga aji ba, yan ajinsu da dama sun yi mata mgna lecturer fa na class sae dae ta ce ta sani, Tun daga nesa ta hangosa yana tahowa, gabanta yyi mugun faduwa taji kmr ta tashi ta falla a guje amma ta kasa, wasa da hijab dinta ta shiga yi gabanta na faduwa, dago ido tayi suka yi ido hudu da shi, ta sunkuyar da kai da sauri, har ya wuceta bae ce komae ba ita ma bata gaishesa ba, mikewa tayi da sauri ta bar wajen kmr munafuka. Da yamma tana xaune cafeteria ita kadae amma ba wnda suka saba xuwa ba, kwata kwata ranan bata shiga lecture ba a cafeterian ta yini, ko Maryam bata san inda take ba, juyawa tayi jin student din cikin cafeterian na gaisuwa don ganin Wanda suke gaisar wa gabanta ne yyi mugun faduwa ganin sa da tayi ya shigo cafeteria, tayi saurin sunkuyar da kai ta jawo hijab dinta ta dan rufe fuskarta, kujerar dake kallon nata ta ga ya ja ya xauna, mikewa tayi da sauri xata bar wajen yace "if I shud slap yhu! Koma ki xauna" kallonsa ta tsaya yi ya watsa mata harara yace "sit" komawa tayi ta xauna ta sunkuyar da kanta, fuskarsa a daure yace "me ya hana ki shiga lectures yau?" Kin dago kai tayi bare ta basa amsa, waiter din dake cafeterian ne ya ajiye ma Dr Aliyu soft drink a table da pack din straw, ya xare straw daya snn ya bude chill coke din gabansa ya saka straw din yyi sip din kadan snn ya dago kai yana kallonta yace "Answer my question B4 i slap yhu" kin dago kanta tayi, a dan tsawace yace "Zainab!" Dago kanta tayi lkci daya hawayen da ke makale idonta ya gangaro, yyi mata mugun kallo yace "oh kuka kike min?" girgixa masa kai tayi ta share hawayen da sauri, ya hade rae yace "me ya hanaki shiga lecture yau" a hnkli kanta a kasa tace "an min fada a gida ne" jin yyi shiru bae ce komae ba yasa ta dago kai tana kallonsa, ta ga wani mugun kallo yake mata, ta dauke kai, a nutse yace "fadan me aka maki?" Shiru tayi bata ce komae ba, ta ji yace "Zainab!" Kallonsa tayi snn tace "Ni ma bn san me nayi ba" Maryam ce ta shigo cafeterian da alamar Afeefah take nema, hango hijab dinta tayi ta karasa table din da sauri tace "kin kyauta Afeefah daga na fadi maki gskya shine har da wani kin shiga lecture...." Harara Afeefah ta watsa mata tace "ehh ban shiga ba" tana kai wa nn ta mike ta fice daga cafeterian sae a snn Maryam ta lura da Dr Sharif da ya bi Afeefah da kallo, ta dan kirkiri murmushi tace "sir ashe kana nn, ina yini" yace "lfya lau" ta juya kmr munafuka ta fice daga cafeterian. Mikewa Dr Sharif yyi ya ciro kudi ya mika ma waiter din snn ya fita, parking space ya nufa ya shiga motarsa yyi reverse ya nufi main gate, tafiya kawae take tana share hawayen idonta taga mota ya tsaya daga kusa da ita, ya bude motar ya fito yana mata mugun kallo yace "yhu walked out of me ina maki magana koh?" Xaro ido tayi tace "Sir Maryam ce..." Dakatar da ita yyi yace "meet me at my office yanxun nn" yana kai wa nn ya bude motarsa ya shiga ya bar wajen.

Eeshatullah Goni 😘😘🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

21....
Chapter 14 · 0% Book details