← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 89

Sashe 34

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

44.....
Afeefah ta fasa ihu a tsorace ta durkushe wajen tana kallonsa lkci daya ta fashe da wani matsanancin kuka ta daura hannu a ka tana kiran Mami, da kyar Aliyu ya iya jan kafarsa ganin tsayuwar ya gagaresa ya koma can gefen gado ya rike kansa da yyi masa nauyi ssae, Adnaan ne ya shigo dakin da sauri ya kalleta snn ya kalli Aliyun, su Jiddah ma suka shigo suka yi cirko cirko a bakin kofa su kalleta su kalli Yayanmu, Mami ce ta shigo dakin ita ma tace "me ya faru? Wa ke min ihu a gida?" rasa me bata amsa aka yi, Afeefah kam sae kuka take daga durkushen da take, kallon Aliyu dake xaune gefen gado har lkcn yana rike da kai Mami tayi ta ja tsaki ta juya ta fice daga dakin, Adnaan ya karaso cikin dakin ya karasa kusa da Aliyu yace "me ya faru bro? Me tayi maka" ganin Aliyu bae da niyar tanka sa yasa ya juya ya fice daga dakin shima, su Jiddah suka bi bayansa. Mikewa Afeefah tayi ta fice ita ma da sauri jikinta na rawa, dakin Adnaan ta shiga ta xube gabansa cikin kuka tace "ya Adnaan ka taimake ni yayanmu xae kashe ni yau" Yace "me kika yi ne wae?" Muryarta na rawa tace "Ni ma bn sani ba" hka tayi ta xama dakin Adnaan taki fita sae kuka take. Ganin gyangyadi take daga xaunen da take yasa Adnaan yace "ki kwanta Zainab" bude ido tayi, tayi shiru tana kallon bakin kofa can ta mike kmr warce kwai ya fashe ma ta fice daga dakin ta nufi dakinsu, su Jiddah na shirin kwanciya Afeefah ta shigo dakin ta nufi kan gado a sanyaye, duk suka bi ta da kallo, sae da ta kwanta snn Jidda ta karasa kusa da ita ta xauna tace "Afeefah me kika yi ma yayanmu" hawaye ne suka gangaro mata bata ce komae ba, daga karshe ta kauda kanta, mikewa jiddah tayi ta bar wajen. Har asuba Afeefah bata wani rintsa ba, ta rasa me ke mata ddi a duniyar, tasan a da ko da wasa bata tsallake duk umarnin da yayanmu ya bata amma tun da ta fara higher institution take disobeyin dinsa ta rasa dalili, sae da su Jiddah suka dawo daga gaida Abba snn ta mike jiki ba kwari ta fita don xuwa gaishesa, Abba na xaune falonsa ya Aliyu ma na xaune falon daga kasa gefensa, Afeefah ta karasa a sanyaye ta xauna daya gefen Abba murya can kasa tace "Ina kwana Abba" Abba yace "lfya lau mamata, kin tashi lfya" gyada masa kai kawae tayi kanta a kasa, Abba yace "an koma makaranta yau ko?" Kai ta gyada masa nn ma, yace "to Ma'sha Allah, sae a maida hnkli kin ji mamata" tace "toh Abba" juyawa yyi yana kallon Aliyu da ya sunkuyar da kansa yace "yauwa ina jin ka Ali" Afeefah ta tsura masa ido lkci daya hawaye ya taru idonta, dago kai yayanmu yyi suka hada ido da ita, ya dauke kai da sauri, da kyar ta iya bude baki tace "ina kwana yayanmu" Ba tare da ya kalleta ba cikin sanyin murya yace "lfya lau" kallon Abbansa yyi yace "dama Abba ina son xan koma can gida na ne, sbda Akwae wani case da muke dubawa ni da abokai na kafin in koma lagos, so we have to stay togeda don mu yi aikin tare" Abba yace "toh shknn Allah ya taimaka" yace "Ameen" snn ya mike ya fita daga falon, bin sa da kallo Afeefah tayi snn ita ma ta mike a sanyaye tace "Abba na tafi" Abba yace "bbu matsala dae koh" kai ta gyada masa tace "bbu Abba" ya sallameta ta fita. Hawaye ne suka shiga bin kuncinta ta nufi dakinsu ta fada kan gado ta dinga rusa kuka, kukanta ya tsananta jin fitar motar Aliyu, su jiddah dae na ta shirin sch abunsa bbu Wanda yace mata komae, gajiya tayi da kukan ta mike daga karshe ta shiga bayi ta wanke bakinta tayi wanka ta fito, duk sae ta ji kmr xaxxabi na neman rufeta, ta fiddo da kayanta da kyar ta sa bayan ta shafa mai ta koma kan gado ta kwanta, Mami ne ta shigo dakin tace "wato Zainab ni kike jira in shigo in gaida ki koh" mikewa tayi da kyar don kanta yyi mata nauyi a sanyaye tace "Mami kaina ne ke min ciwo" Mami tace "ki sakko kiyi breakfast sae ki sha magani" saukowa tayi daga kan gadon ta daura dankwalinta ta bi bayan Mami, tea kadae ta iya sha, Mami ta dauko Mata magani ta bata ta sha snn ta koma falo ta kwanta kan kujera, Driver ne yyi horn alamar yana jiransu, Jiddah da sadiya suka dauki jakarsu suka yi ma Mami sallama, Afeefah ta mike da kyar tace "Anty jiddah don Allah ki dauko min jakata da hijab a sama" Mami tace "kina da lecturen safe ne?" Afeefah ta gyada kai tace "Umm" Mami tace "ki bari kawae su tafi ko da rana sae ya kai ki tunda baki jin ddi" girgixa kae Afeefah tayi ta mike da sauri tace "A'a ni xan tafi ynxu Mami" sama ta nufa ta dauko hijab da jakarta ta sakko tayi ma Mami sallama suka bar gidan. Driver na ajiye su ko wannensu ya nufi department dinsa, Afeefah kam karkashin bishiya ta samu ta xauna duk da tasan tana da lecture din safe, gaba daya tunaninta na gun ya Aliyu, duk ta rasa sukuni, Muryar Maryam ta ji a bayanta tana cewa "uhm Afeefah me kirki ko kira" Afeefah tace "ae ke naga kin yi kiran" murmushi Maryam tayi tace "wayata ce ta lalace, amma ai na shigo duba mana result, nayi niyar karbar lambarki gun Dr sharif ranan amma na manta," Afeefah tace "hka yace maki yana da nmbr na" Maryam ta dan yi murmushi tace "tashi mu shiga lecture an kusa shiga" girgixa mata kai Afeefah tayi tace "akwae abinda nake jira, ki shiga kawae" Maryam tace "toh" snn ta nufi lecture hall, Afeefah na nn xaune har bayan kusan awa daya ta hango Dr Sharif yana tahowa da wani student, dauke kai tayi da sauri har suka karaso, ta dan sata kallonsa suka hada ido don shima kallon nata yake, sunkuyar da kanta tayi har suka wuce. Mikewa Afeefah tayi da sauri ta bar wajen don bata ma son ya dawo ya ganta, rasa inda xata tayi lkci daya hawaye ya cika idonta ta nufi gate kawae, tsaye tayi tana share hawayenta ta tsayar da adai daita, shiru tayi duk da taji tambayar da yake Mata na cewa ina xata, a hnkli ta samu kanta da cewa "Nasarawa G.r.a xa ni" bata jira cewarsa ba ta shiga adai daitan.
Suna isa nasarawan tayi masa kwatancen inda xata, dai dai bakin gate din gidan ya ajiye ta ta fito ta bude jakarta ta mika masa duba daya ya bata canjin dari biyar, bata damu ba ta nufi gate din ta gaida mai gadin dake xaune kan benci a sanyaye tace "yana ciki" yace "ehh yana nn" tura gate din tayi ta shiga gidan, sae da ta isa bakin kofar shiga gidan taji gabanta na faduwa, kmr tana tsoron handle din kofar ta murda a hnkli ta ji shi a rufe, tsoron danne bell ta ji, kawae ta nufi back yard, kofar kitchen ta murda ta ji a bude ta shiga snn ta rufe ta nufi falo, bbu kowa falon sae Ac da plasman dake aiki, a sanyaye ta nufi stairs ta haura sama, ta dde tsaye bakin kofar dakin daga bisanni ta tura a hnkli tare da yin sallama can ciki ta shiga.

Eeshatullah Goni
😘😘
[5/23, 08:34] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 34 · 0% Book details