← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 89

Sashe 81

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

100.....
Da kyar Zainab ta iya mikewa ta fita daga bangaren ta nufi dakinta duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ta rasa gane me yake nufi da hkn, k'asa daurewa tayi ta xube kan gado ta shiga kuka a hnkli, ta kusa awa daya kwance kafin ta mike jin xa a tada sllhn Azahar ta nufi bayi tayi alwala, tana ji shi ma ya fita xuwa masallaci. Bayan minti talatin ya shigo gidan ya hauro sama taji ya kirata yana tsaye daga corridor, mikewa tayi da sauri ta nufi kofar ta bude tana kallonsa tace "Na'am" ba tare da ya kalleta ba yace "Ga abinci an kawo downstairs" daga hka ya bude kofar falonsa ya shiga. Tsaye tayi bakin kofar kmr an dasa ta, juyawa tayi da sauri ta koma dakinta ta fada gado ta shiga rera kuka, daga hka bacci ya dauketa, saukan numfashi taji kan fuskarta cikin bacci, ta bude ido a hnkli ta ga fuskarsa dab da nata, mirginawa tayi da sauri daga gun ta mike xaune tana murxa ido, murmushi yyi yace "Ba abinci nace ki xo ki ci ba!" Sunkuyar da kai tayi bata ce komae ba, ya mike ya d'ago ta yana rike da hannunta suka fita daga dakin, tsakar falo ya xaunar da ita inda abincin da su fadila suka kawo ke ajiye, ya xauna shima ya bude kulan ya ga jollof rice ne da chicken sae coslow, dibar masu yyi a plate daya ya mika mata spoon shi ma ya dauka, snn ya fara ci, a hnkli ta shiga cin abincin ita ma, tana yi tana kallonsa, shi kam kansa a kasa yake, bae wani ci da yawa ba ya ajiye spoon din yace "akwae farfesu idan xaki diba" bata ce komae ba ya mike ya koma 3 sitter yyi kwanciyarsa bayan ya dauki wayarsa. K'asa ci gaba da cin abincin tayi, a hnkli ta tura plate din daga gabanta ta koma jikin kujera ta jingina, bayan kusan minti goma ya kalleta yace "Kin koshi ne" kin cewa komae tayi sae wasa da xoben hannunta take, ya sakko daga kan kujerar ya xauna kusa da ita yana kallonta yace "Wat happened?" Hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa taki cewa komae, lumshe ido yyi ya jawo ta jikinsa cikin sanyin murya yace "Me ya faru kuma princess" a hnkli tace "Ni ban san me na maka ba yayanmu" dago kanta yyi yace "Haba me kuwa xa ki min princess, baki min komae ba" daga hka ya lumshe ido ya manna mata kiss a goshinta, ta rufe ido da sauri ya ja hancinta yyi dariya yace "Ke dae kice through out yau baki yi kuka ba shi sa yhu are restless," bata fuska tayi tace "Ni ae na daina kuka fa yayanmu" mikewa yyi ya kwashe kwanukan da suka ci abinci ya nufi kitchen, sae da ya wanke su kafin ya fito ya sameta tana game da wayarsa, ya xauna gefenta tace "Yayanmu wanke wanke kayi?" Yace "Yea!" Tace "Da sae ka kira ni in taya ka ae" yace "A'a daxu kinyi mopping ae." Mikewa yyi ya nufi stairs ta mike da sauri ita ma ta bi bayansa, har suka shiga bedroom dinsa, kallo daya yyi mata ya dauke Kai ya shiga fiddo kayan da xae sa, tace "Yayanmu ina xa ka?" Ya ajiye kayansa gefen gado yace "Ba dde wa xan yi ba, am goin out" b'ata fuska tayi tace "Ni xan bika toh" kallonta yyi kafin yace "Idan tsohon mijin ki xae fita kina binsa ne" shiru tayi cikin sanyin murya tace "Ni bana cewa xan bi sa" wani kallo yyi mata ta gefen ido kafin ya cire jallabiyan jikinsa ya nufi bayi, bin sa tayi da sauri kan ya shiga bayin tace "Xan hada maka ruwan wankan yayanmu" daga hka bata jira cewarsa ba ta raba ta gefensa xata shiga bayin ya fixgota ya fitar da ita yace "Dnt wrry xan yi da kaina" yana fadin hka ya shige bayin yyi banging kofar, still tayi bakin kofar duk jikinta yyi sanyi, a hnkli ta juya ta fita daga dakin ta nufi dakinta, kwanciya tayi kan gadonta ta lumshe ido, tana jin fitarsa daga gidan bayan minti ashirin bae kuma shigo yace mata ya tafi ba, kuka taji na son taho mata amma ta dannesa.

Da daddare ta fito daga wanka daure da towel tana xaune gaban mirror tana shafa lotion duk tayi wani sanyi ya shigo dakin, tun shidda ya shigo gidan amma sae lkcn ta gansa, gefen gadonta ya xauna, k'asa kallonsa tayi sbda kunyan ba kaya jikinta, da kyar ta iya cewa "Yayanmu Hijab dina a bedside drawer ka bani plss" ya dau kusan minti uku kafin yace "Tashi ki dauka mana" shagwabe murya tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Ni baxan iya tashi ba" yace "Gidan tsohon mijin ki wa ke dauko maki hijab idan ya shigo dakin ki" ta dan yi shiru sae kuma a hnkli tace "Ae baya shigowa wllh"

Manage plss, xuwa after nine to ten xa ku ji ni. One love.

Shatu Lol.

🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad
Chapter 81 · 0% Book details