← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 89

Sashe 74

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Eeshatullah

[6/29, 20:41] ‪+234 703 716 4670‬: 'Ya mace kyautar Allah
By Ashmaad
90___91
kankamesa tayi ta fashe da kuka, ya ja ta ya nufi bedroom dinsa don baya son wani ya gansu a hka, gefen gado ya xauna bayan ya janyeta jikinsa da kyar, cikin sanyin murya yace "Kina da hnkli kuwa Zainab, kin mance ke matar aure ce" jin bata ce komae ba yasa ya sakar mata murmushi yace "Me ya kawo ki gida da safe hka," shiru yyi yana kallon idanunta kafin yace "wat happened to ur eyez," kin cewa komae tayi sae hawayen dake sakko mata, takardar hannunta ya kalla ya karbe takardan yana kallo kafin ya warware, cikin 'yan sakwanni ya gama karanta content din, lkci daya yanayinsa ya canxa ya shiga kallonta da alamar tambaya, can cikin sarkewar murya yace "Ya sake ki?" A hnkli ta gyada masa kai hawaye na bin kuncinta, yafi minti biyu yana kallonta kafin ya mike ya dauki wayarsa ya mika mata yace "sa min nmbrsa" da sauri ta girgixa masa kai tana kuka tace "A'a yayanmu ka kyalesa" a tsawace yace "Ki sa min nmbr nace" muryarta na rawa tace "Ni bn xo da waya ba, kuma bni da nmbr a kai" juyawa yyi ya fice daga dakin, ta mike da sauri ta dauki takardan ita ma ta fita ta nufi dakin Mami, har lkcn Mami na xaune kan darduma tana Azkhar, da mamaki take kallonta har ta karaso cikin dakin, tace "Zainab, me ya faru? Daga ina da sassafen nn" kuka ta fashe da ta sulale nn k'asa ta dinga rusa kuka, hnklin Mami ya tashi ssae ta mike ta shiga tambayarta ina mijinta, jin bata da niyar bata amsa yasa ta karbi takardan hannunta ta bude tana kallo, lkci daya ta saki salati ta sake takardan a raxane tace "Saki Zainab? Me ya hada ku" da kyar tace "Nima ban sani ba" salati Mami ta dinga yi tana nanata wa, Shigowar Aliyu dakin yasa tayi shiru, ya karaso ya dauki takardan, sae a snn Mami ta fara hawaye, Aliyu ya durkusa kusa da Zainab yace "Me ya hada ku da shi?" Girgixa kai tayi da sauri tace "Bbu komae yayanmu" Aliyu ya mike yana kallon Mami yace "Am sueing him in'sha Allah, sae yyi regretting actions dinsa." daga hka ya fice daga dakin Mami na kiransa ko juyowa bae yi ba.
Abba ya nisa yana girgixa kai yace "kin tabbata bbu abinda ya hadaku da shi Zainab," tana hawaye ta gyada ma Abba kai, shigowar Aliyu yasa duk suka juya suna kallon kofar har Mami dake xaune tayi jigum falon, Karasowa falon yyi cikin shigarsa ta suit rike da makullin mota, ya risina yana kallon Abbansa yace "Gani Abba" Abba yace "Ina xa ka?" Ya sunkuyar da kai yace "Xan dan fita ne" Abba yace "Na dae isa da kai koh Ali" Shiru yyi bae ce komae ba, Abba yace "Toh kar ka fita gidan nn, ka bari xa a bi komae a hnkli ayi magana ta fahimta, sae aji dalilinsa na aikata hkn" cikin bacin rae Aliyu yace "Magana ta fahimta kuma Abba, Haba ko me tayi masa bata cancanci hka ba, shi bae da kanni mata ne, y xae saketa at her young age, plss Abba ka bari in bashi lesson of his life" Abba yace "Ni dae na hane ka da barin gidan nn, Alhaji Mukhtar xae iso xuwa anjima, shima iyayensa da shi kansa za su xo don hka kayi hkuri Abi komae a hnkli" Afeefah taji hanjin cikinta ya kada jin abinda Abba yace, mikewa Aliyu yyi ya fice daga falon. Karfe sha daya tana kwance dakin Mami tana jin kmr xaxxabi zae rufeta yayyinta ma na xaune dakin ko wannensu ya tausaya mata ba kadan ba sae dae sun yi mamaki don Dr Shariff bae yi kama da mutumin da xae iya aikata hka ba, Mami ce ta shigo dakin tace Zainab ta sa hijab ta xo, da kyar ta mike ta sa hijab ta fita, Mami na gaba tana biye da ita suka shiga falon saukan baki, gabanta yyi mugun faduwa ganin dad na Kaduna da wani abokinsa, snn ga Dr Shariff da dad dinsa da uncle dinsa, Abba ma na xaune falon sae Aliyu dake xaune kasan lallausan carpet din falon, Dr Shariff ma na zaune kasa daga gefen uncle dinsa, da kyar ta sulale kasa ta xauna gefen ya Aliyu ta ji xufa na tsatssafo mata, Addu'a aka fara da gaishe gaishe kafin dad din Kaduna ya kalli Dr Shariff da kansa ke kasa har lkcn yace "Ali" da kyar Dr Shariff ya daga kai yana kallonsa, dad yace "ya aka yi hka Ali, me ya hada ka da matar taka har ya kai ka ga aikata mummunan aikin nn gare ta, wani laifi tayi maka hka Aliyu" Dr Shariff ya juya ga dad dinsa dake ta jifansa da wani irin kallo hka ma uncle dinsa, girgixa kai yyi ya k'asa cewa komae lkci daya hawaye ya shiga sakko masa ya rike kansa, jikin Abbansa yyi sanyi don yasan halin d'an nasa, baya kuka hka sae in cutar sa aka yi kuma da wuya ka ga hawayensa, har dad ma sae da jikinsa yyi sanyi hka ma Abba, Afeefah kam bnda rawa bbu abinda jikinta yake sae shigewa jikin ya Aliyu take don tasan idan Dr Shariff ya tona ta Yau me rabata da Mami sae Allah, dad yyi karfin halin cewa "muna sauraran ka Ali, me ya faru sanar da mu ka ji" kin dago kansa yyi har lkcn hawaye na sauko masa cikin sanyin murya yace "Dad kuyi hkuri ku gafarce ni, ni kam baxan iya cewa komae ba don ya wuce a guna, in dae na cuce Zainab duk xaman mu da ita ina neman gafarar ta, duk da nasan ban taba cutar ta ba, ni na yafe mata duniya da lahira, ku gafarce ni don Allah Abba" daga hka ya mike ya nufi kofa ya fita daga falon, jikin iyayen nasu yyi sanyi ssae, Mami kam da yake ita ta haifi abunta tun da ta ga reaction din 'yar tata ta gane bata da gskya kuma akwae abinda bata son ya fada ganin ynda take mutsu mutsu daga xaune, bata san lkcn da ta mike ta fixgota cikin xafin rae ta kai mata mari masu lafiya ba tace "Don uwarki me kika yi masa ki fada kar na sumar da ke" ya Aliyu ne ya kwace ta hannun Mami don kin sauraran maxan dake falon tayi, ya fice da ita daga falon da sauri tana kuka bakin rae, dakinsa ya nufa da ita, ya xaunar da ita gefen gado yana kallonta yace "Tun shigowar ki falo na lura baki da gskya Zainab, duk duniya nafi kowa sanin halin ki, ko Mami baxata gaya min ke ba, ki gaya min gskyan me kika yi ma mijin ki" kin cewa komae tayi, ya kuma san baxata ce din ba, ya mike a hnkli ya koma jikin window ya tsaya yana kallon waje, kwanciyarta tayi kan gadonsa ta ja bargo.
9 mins · Khaleesat Haiydar...
[6/29, 20:42] ‪+234 703 716 4670‬: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad
Chapter 74 · 0% Book details