← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 89

Sashe 16

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

23/24....
Da sallama Afeefah ta shigo office din ita kadae rike da coke din da straw ta karasa table dinsa ta ajiye tace "Sir ga shi" ba tare da ya kalleta ba yana ci gaba da danna wayarsa yace "Thnk yhu" ajiye masa change dinsa tayi ta nufi jakarta ta dauka xata fita ya dago da sauri yace "Ina maryam din?" Juyawa tayi tana kallonsa tace "tana waje tana jira na" yace "OK, ku baxa ku sha coke din ba" ta girgixa masa kai tace "Aa mun sha daxu" yace "OK" har ta isa kofa yace "Zainab!" Juyawa tayi tana kallonsa yace "Waye ku ka je shop rite da shi jiya?" Ta wara ido tace "Shine yayanmu ae" gyada mata kai yyi yana kallonta yace "Cousin brother koh" ta girgixa kai da sauri tana dariya tace "lah Abbanmu daya wllh fa Sir" shiru yyi yana kallonta snn ya gyada mata kai, ta juya ta fice daga office din.

Ana gobe xa su tafi mid semester break Afeefah ce xaune da su Maryam da Rukayya inda suka saba xama bayan sun fito daga lecture tana masu explaining wani topic a course dinsu BiOC 312 da suka ce ba su gane ba, Maryam sae kallonta take don bata taba tunanin Afeefah na da maida hnkli hka ba ka rantse kace lecturer ce ynda ta xage take fahimtar da su da turanci, duk ajin anyi xaton kuka ne kadae abinda ta fi iyawa, Muryar lecturen Course din suka ji a bayansu da alamar ya gama lecture da yan 200lvl yace "Ashe bayan kuka ma kina da kkri wajen karatu Zainabu" Afeefah ta rufe fuskarta da sauri da littafin hannunta tana dariya da yake sun dan saba da lecturan tana yawan ganinsa office din Dr Sharif ko a department wani lkcn, su Maryam suka fara dariya suna kallonta, shima yyi dariyan ya wuce. Da yamma suna dawowa daga mosque Afeefah ta nufi cafeteria da Maryam suna tafe suna hira Maryam tace "kin ga yan matan nn basu sake xuwa gun mu ba" Afeefah tace "Allah ya taimake mu don ni tsoronsu ma nake, kila sun...." Maryam ta xabga mata harara tace "Da'alla, matsoraciya kawae to me suka isa su mana, ae Dr Sharif ya kirani a ranan ban san wnda ya gaya masa ba, muka je har department dinsu da shi na nuna su" Afeefah ta xaro ido tace "ba ki ji tsoro ba Maryam? To me ya ce masu" Maryam ta tabe baki tace "oho, kawae yace in tafi, nayi wucewa ta" drinks Maryam tayi masu orderin bayan sun xauna. Biyar saura suka fito daga cafeterian Afeefah tace "ni gida xan tafi Maryam, sae mun hadu next wkk, xan sha bacci wnn break din da muka samu" Maryam tace "wae meyasa kika daina jiransu Anty jidda, kuma fa Abdul na tutorial a class tun daxu kuma course din Dr sharif" Afeefah tace "sbda wani lkcin ina riga su gama lecture sae in ta jiransu har in gaji" Maryam tace "to mu shiga tutorial din" Afeefah tace "A'a ni baxan shiga ba xan yi karatuna a gida, byee" tana kai wa nn bata jira cewar Maryam ba ta kama hanyar main gate, Maryam ta tabe baki ta nufi Department don shiga tutorial, tafiya kawae Afeefah take ko rabin main gate din bata yi ba ta hango yan matan da suka samesu da Maryam a cafeteria ranan da kawayensu su kusan uku suna tafe suna hira da shewa. ta xaro ido a tsorace ganin tahowa suke ta inda take tafiya, rawa jikinta ya dau yi ta fara kalle kallen inda xata buya kan su iso inda take, wani cafe dake wajajen ta shige da gudu ta labe kmr munafuka xuciyarta na bugawa, bayan kusan minti Uku taji muryar matan a cafe din sun shigo da alamar xa suyi photocopy, saura kiris ta fashe da kukan tsoro ganin basu lura da ita ba yasa ta fice da gudu ta kama hanyar gate, mota taga ya ja burki gefenta, har xata falla a guje ta ga Dr Sharif ne, tsayawa tayi tana share hawayen fuskarta da sauri tana kalle kalle kmr munafuka don bata yi wani nisa da cafen ba, yana fitowa daga motar ya hade rae yana kallonta yace "Meyasa baki shiga tutorial ba?" Girgixa masa kai tayi muryarta na rawa tace "gida xan tafi" ya galla mata harara yace "kukan me kike?" Ganin xata fashe masa da kuka yasa ya daka mata tsawa ba shiri ta hadiye kukan har lkcn bata bar waige waigen da take ba ta ga ko yan matan sun fito, ya juya yana kallon inda take kallo, dae dae lkcn da yan matan suka fito daga cafen, bayansa ta nufa da sauri muryarta na rawa tace "Sirrr," kallon yan matan kawae yake su ma kallonsa suke lkci daya kuma duk suka dauke kai suka fara tafiya suna isa dai dai inda yake tsaye Afeefah na bayansa kmr munafuka suka gaishesa, bbu yabo bbu fallasa ya amsa suka ci gaba da tafiyarsu kmr sun hada baki suka juyo gaba daya suna kallon Afeefah sae kuma suka kwashe da dariya suka yi gaba da sauri, Afeefah ta fito daga bayansa tana share hawaye ya daka mata wani mugun tsawar da ya raxanata yace "kuka kike min?" ba shiri ta hadiye kukan tana girgixa masa Kai, ya bude mata front seat bata jira yace ta shiga ba ta shige da sauri, ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver snn ya tada motar ya nufi main gate, hanyar jan bulo taga ya nufa da ita, ita dae sae wasa da fingers dinta take, "kina jina?" Dago kai tayi tana kallonsa ta mayar da kanta kasa da sauri ganin ynda ya hade rae, "Seriously daga yau, i mean daga yau na kuma ganin kina kuka a sch xaki sha mamaki na, yhu re not a kid I c no reason xa ki dinga yi ma mutane kuka unnecessarily, kar in kuma ganin hawayen ki a sch" a dan tsawace ya kare maganan, ta gyada masa kai a hnkli, yace "kin ji ni da kyau kuwa?" Kai ta gyada masa nn ma, yace "to me nace?" a hnkli tace "kace kar in kuma kuka a sch" yace "good! Repeat after me" dago kai tayi tana kallonsa yace "ki ce, ke Zainab," murya can kasa tace "Ni Zainab," yace "kinyi alkawarin" nn ma a hnkli tace "nayi alkawarin," yace "baxa ki sake kuka a sch ba da ma ko ina!" Sunkuyar da kanta tayi ta maimaita abinda yace a hnkli, yace "yhu promised fa kika ce?" Kai ta gyada masa tace "yes sir" ya galla mata harara yace "da wani katon idonta a gurin" boye fuskarta tayi da tafin hannunta ta fara dariya a hnkli, dan murmushi yyi ya mayar da hnklinsa gaba daya kan tukin da yake, a hnkli dan kanta ta xame hannunta daga fuskarta. Nesa da gidansu ssae yyi parkin ya juya yana kallonta, ta dan wara ido tace "Sir dama kasan gidanmu?" Da sauri ta ba kanta answer tace "ohh Maryam ta taba xuwa da kai na manta" murmushi kawae yyi, tace "na gode sir" snn ta bude motar ta fice, "Zainab!" Taji ya kirata a nutse, ta juya da sauri tana kallonsa, a hnkli yace "Read ur books, dnt sleep too much during d break, ur exam is around the corner, nd I will b conducting my last test on Tuesday" Kai ta gyada masa tace "OK sir xan yi karatu," kai ya gyada mata ta kulle masa motarsa ta nufi gate dinsu shi kuma yyi reverse ya bar anguwar, tsaye ta ga Ya Aliyu a gate da alamar shigowarta yake jira, xuciyarta ya kusa shigewa cikinta, cikin rawar Murya tace "yayanmu"

Eeshatullah Goni😘😘🌸👩🏻 'Ya mace Kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 16 · 0% Book details