← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 89

Sashe 46

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

61....
Karfe sha daya saura duk yan gidan suka hallara a falon Abba, Aliyu kadae ne baya falon duk da kiran da Jiddah taje tayi masa, bayan kusan minti biyar kowa ya nutsu a falon, Mami ta kalli Adnaan tace "ina Ali?" Mikewa yyi ya fita, ba a dau lkci ba Adnaan ya dawo falon yace yana xuwa, da sallama can ciki Aliyu ya shigo falon yana sanye da jallabiya milk colour ya nemi gefen Safiya dake ta binsa da kallo ganin ynda yayan nata ya rame, ba ita ba duk kanninsa kallonsa suke hka ma Abba, Abba ya fara gaidawa snn Mami duk kansa a kasa don tunda garin Allah ya waye bae fito ba sae ynxu, Afeefah kam na xaune kasa daga gefen Mami, ita kadae Aliyu ya daga kai ya kalla suka hada ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ta boye fuskarta jikin Mami, ya kuma sunkuyar da kansa kasa, Adnaan ne ya bude wajen da Addu'a bayan 'yan mintuna Mami ta fara magana kmr hka "Na so ace, ko kuma ince na sha fatan kadda Allah ya nuna min rana irin ta yau da ma abinda nake shirin fada ma kowa ynxu, sae dae am mistaken, ya xama dole in bude ma kowa wnn sirrin yau, Da farko dae ina san ku san na shigo gidan Mahaifin ku a shekara ta 1986, lkcn Aliyu na da shekaru uku a duniya, ran da na cika shekara daya a gidan aka haifi Adnaan kuma a ranan Allah yyi ma Mahaifiyar su Aliyu rasuwa, Wanda hkn yasa rikon marayun ya dawo hannu na, na kwashi shekaru fiye da uku ban haihu ba, daga karshe Allah ya bani 'ya ta ta fari Safiya, bayan shekara biyu na haifi Ummi, daga Ummi kuma na haifi Suhaila warce Allah yyi ma rasuwa ran da na haifi kanwarta Sadiya, to dama tun a haihuwar Suhaila na fara fuskantar matsala da mahaifin ku, inda yake nuna min shi fa yafi son 'ya ya maxa, ana dae xaune a hka har Allah ya kuma ban wata 'ya macen Wanda ba karamin canji naga daga gun Mahaifin ku ba, anyi suna da sati daya jaririyar Maryam ta koma ga Allah, bayan shekara daya da wani abu na haifi Jiddah," Shiru Mami tayi da dukkan alaman bata son ba yaran nata tarihin irin wahalar da tasha gun Mahaifinsu don tana haifan 'ya 'ya mata, hawaye ne kawae ke sakko mata, daga karshe ta ci gaba cikin sanyin murya tace "Jiddah na da wata Shidda Mahaifin ku ya kara aure, wato ya auro warce xata haifa masa 'ya 'ya maxa, bae san duk _YA MACE KYAUTAR ALLAH_ ce ba," hawaye ssae Mami take hka ma duk yaran nata mata dake kallonta a sanyaye, da kyar ta saita kanta ta ci gaba "Jiddah na da shekara daya cif a duniya na rabu da Mahaifin ku, wato ya sauwwake min, bae kuma yarda na tafi da ita ba bare yayyinta duk da naso yin hkan don nasan irin wahalan da xa su sha gun matar ubansu don bata da imani matar kuma ita ce sanadin rabuwa na da Mahaifin ku, amma bbu ynda na iya na tafi na bar ku" Kallonta kawae duk yaran nata mata suke suna hawaye, barin Zainab, Aliyu da Adnaan da Safiya sae ummi ne kaddae basu yi mamakin jin lamarin ba don da alamar sun san lbrin sae dae su ma duk jikinsu yyi sanyi, Mami ta ci gaba a sanyaye, "Ina fita idda da 'yan watanni Allah ya hada ni da Mahaifin Zainab" Mike Afeefah tayi da sauri hawaye na bin kuncinta xata bar falon Mami tayi hanxarin rikota ta mayar da ita ta xaunar tace "bbu inda xa ki Zainab" kuka ssae Afeefah take me ban tausayi, su Jiddah, Sadiya da Sumayya ma duk kukan suke, Abba dae har lkcn bae iya ya dago kansa ba, Mami tace "Ina auran Alhaji Umar da shekara daya da watanni biyu Allah ya bani Zainab, wata 'ya macen dae, tana kuma da shekara daya a duniya Allah yyi ma Mahaifinta rasuwa a hatsarin mota," Hade kai Afeefah tayi da gwiwa tana kuka kmr an aikota, Mami ma hawayen take har lkcn, don da kyar ta iya ci gaba tace "Ni baxan bada lbrin ynda rayuwar yayyinku ya kasance hannun matar uba ba kuma baxan ce nasan dalilin rabuwar ta da Mahaifin ku ba, sae dae nasan bayan rasuwan Mahaifin Zainab Mahaifin ku ya dawo yana min magiya yana ban hkuri in koma in rike 'ya ya na, dake Allah yyi xaman mu bae kare ba kuma akwae sauran rabo hka ba don na so ba na koma gidan Mahaifin ku, inda Allah ya kuma axurta ni da 'ya 'ya matan har biyu," Mami ta rungumo Afeefah jikinta ganin ynda take kuka, tana kallon duka yaran nata cikin sanyin murya tace "Kin ji matsayin ki a gidan nn Daughter, kuma Kaduna da kike xuwa sune dangin Mahaifin ki, Alhaji Mukhtar shine yayan Mahaifin ki uwa daya Uba daya" kin cewa komae Afeefah tayi sae boye fuskarta da tayi jikin Mahaifiyarta tana kuka ssae, bayan kusan minti uku Mami tace "Jiya Aliyu ya bullo min da wani lamari da ban taba xato daga gare shi ba, ban kuma taba kawo hkn a ka ba," Shiru tayi snn ta cigaba tana kallon yaran nata "wae 'yar uwarsa Zainab yake so da aure" kallon mmki Adnaan ya juya da sauri yana ma Aliyu da kansa ke kasa, hka ma su Safiya da Ummi, su jiddah kam kusan kallon tsoro suke masa, Mami tayi murmushin takaici tace "Ehh kwarae kuwa akwae aure tsakanin sa da Zainab na sani, amma get this Aliyu: Ni Zuwaira baxan taba baka auren 'ya ta ta xo tana haifa maka 'ya 'ya mata ka walakanta min ita ba, Neva!" kallon mmki Abba ya dago kai yake mata, hka ma Aliyu da ya dago da sauri yana kallonta da idonsa da ya kada ssae, su Safiya ma kallon mmkin suke mata, ita kam ko a jikinta ta ci gaba "gobe idan Allah ya kai mu xan tura Zainab gun dangin Mahaifinta su aura mata Wanda suka yi niyya tun farko, Wanda suka kuma ga ya dace da ita don nasan baxa su cuceta ba, amma da in baka auren Zainab Ali gwara ta xauna ba aure" Mami na kai wa nn ta mike ta daga Zainab suka fice daga falon.

Eeshatullah 😂😂

Chaii Mami kin burge wllh.

[5/22, 07:57] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

62.....
Aliyu ne ya fara karfin halin mikewa ya bar falon bayan fitan Mami da Zainab, snn Adnaan, daki ya nufa ya dauki makullin motarsa ya fita daga gidan gaba daya. Bbu Wanda ya samu fuskar yi ma Mami magana yinin ranan, don a daki ta yini da Zainab, duk kayan da tasan Afeefah xa ta bukata ta hada mata a jaka don gobe da sassafe xata je ta sa ta a motar kaduna, da daddare misalin takwas da wani abu Jiddah ta shigo dakin Mami, tana kallonta tace "Mami wae Abba yace in kira Afeefah" Mami tace "Tana xuwa" juyawa jiddah tayi ta fita, Mami ta mike tana kallon Afeefah tace "tashi mu je" da kyar Afeefah ta mike ta bi bayan Mami suka nufi falon Abba, tsayawa kallon Mami Abba yyi da mmki, Mami ta nemi gu ta xauna tace "Ga ta" wani murmushin takaici yyi yana kallon Afeefah yace "Je ki Zainab" juyawa Afeefah tayi ta fita daga dakin a sanyaye, Abba yace "Wato kin ban mamaki ne Zuwaira, ko ance min xa ki iya yima ni, da 'ya yan ki cin fuskar da kika mana da safe baxan yrda ba, dama laifin wani yana shafan wani Zuwaira, naga ko Allah ka nemi gafara wajensa yana yafe maka, balle mutum, ynxu ki dubi tsabagen idona kice baxa ki ba Ali auren 'yar ki ba, kin kyauta min da 'ya yan ki knn" Mami tayi murmushi tace "Ban kyauta ba nasani, amma dats d last thing I will do on earth in ba Aliyu Zainab, Allah ya xaba masa warce ta fi ta don ita ma nasan karshenta 'ya 'ya matan xata je tayi ta haifo masa" tana kai wa nn ta mike ta fita. Xaune ta samu Safiya da Ummi a bedroom dinta, Mami ta xauna tana kallonsu tace "ya aka yi?" Duk da irin shakkarta dake bayyane a fuskokinsu hkn bae sa Safiya tayi kasa da gwiwa ba tace "Mami don Allah magana ta fahimta xa mu yi" Mami ta hade rae tace "wace maganar ce ta fahimta? Ina jin ku" Safiya ta sunkuyar da kai tace "Mami ki dubi girman Allah ki mance duk wani abinda ya faru a baya, Mami don mu 'ya yanki xa ki yi hkn, don Allah ki yi hkuri ki ajiye batun da kika yi daxu a falon Abba, kin fi kowa sanin halin Yayanmu tunda...." Dakatar da ita Mami tayi ta hanyar cewa "Ku bar min daki na" ganin basu da niyar tashi yasa ta daka masu tsawa, Mikewa suka yi kusan a tare jiki a sanyaye suka bar dakin, Mami ta ja tsaki ta shiga bayi.
Chapter 46 · 0% Book details