← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 89

Sashe 36

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

46___48
Shiru Afeefah tayi tana kallonsa, sae kuma tayi murmushi tace "Um na gama" ledan hannunta ta ajiye ta fiddo kulan ciki da drink da plate da spoon tace "I brought this for yhu sir" bata jira cewarsa ba ta bude kulan abincin, dauke kai yyi ya shiga danna wayarsa yace "Abincin yayan naki xa ki kawo min?" Ta girgixa kai tace "ae da yawa na dafa sir" ganin xuba masa take son yi a plate ya dakatar da ita da sauri "No! ni am OK" tsayawa tayi tana kallonsa, yyi kmr bae san tana yi ba, can ta rufe kulan ta mayar da shi cikin nylon da plate din snn ta dauka ta nufi kofa, bin ta yyi da kallo har ta fice ta rufo masa kofar sa. Cafeteria ta nufa ta samu Maryam xaune da drink a gabanta, Maryam tace "har kin dawo?" "Um" kawae Afeefah ta ce mata, Maryam tace "ina ce office din sir kika tafi" hade rae Afeefah tayi tace "hka nace maki" bata jira cewarta ba ta bude leda ta fiddo abincin tana kallonta tace "Bismillah" Maryam ta dan yi murmushi tace "A'a ni na koshi" Afeefah tace "OK" diban abincin tayi cikin plate ta dauki spoon ta fara cin abun ta, jin wayarta na vibrate a jaka ta bude jakar ta fiddo wayar, jiddah ta ga ke kiranta, ta daga Jiddah tace "wae ina kika je yau Afeefah?" Afeefah tace "wajen yayanmu" Jiddah tace "shine kika ki shiga lecture?" Afeefah ta hade rae tace "to wae wa ya gaya maki bna sch? Ni ynxu ma ina nn kusa da dept dinmu," katse wayar Jiddah tayi Afeefah ta mayar jakarta, Ba tare da ta kalle Maryam ba tace "ke kika ce ma Anty Jiddah bn shiga lecture ba?" Maryam tace "No!" Afeefah na gama cin abincin gabanta ta mayar da plate din da spoon cikin leda ta kalli agogon cafeteria ta ga har biyu, mikewa tayi tace "Baxan iya jiran lecture har 4 ba, ni na tafi gida" Bin ta da kallo kawae Maryam tayi har ta fice abun ta, ta kama hanyar main gate. Afeefah na isa gida ta bi ta kofar kitchen ta lallaba ta wanke kulan abincin hannunta snn ta dauki ginger drink ta nufi sama, dakin Mami ta shiga Mami tace "har kin dawo, ina su Jiddah?" Afeefah tace "basu gama lecture ba su" gaisheta tayi Mami tace "ya ciwon kan?" Afeefah tace "Da sauki Mami" juyawa tayi ta fita daga dakin ta shiga nasu tayi kwanciyarta, biyar saura Mami ta kirata ta sakko kasa ta taya ta girka Supper, Afeefah na slicing Pumpkin leaves tace "Mami xa kiyi abinci da yayanmu koh?" Mami tace "a ina kika ga yayanku?" Afeefah tace "Ba yana gidan sa ba" Mami tace "to gidan nasa xan kai masa abincin" a hnkli tace "Kinga Mami bashi da lfya fa" Juyawa Mami tayi ta kalleta tace "shi ya gaya maki bae da lfya?" Afeefah ta gyada Mata kai, Mami tace "Adnaan baya nn ban san Wanda xae Kai masa ba sae dae ya xo ya karba da kansa," Afeefah kmr xata yi kuka tace "Mami ba sae ni in kai masa ba, bashi da lfya fa" harara Mami ta watsa Mata tace "idan naki ba ki fa?" Shiru tayi bata ce komae ba, Mami ta ci gaba da abinda take, Mami na kwashe tuwo Afeefah ta juya xata bar kitchen din ita a dole fushi take baxa a kai ma yayanmu abinci ba, Mami tace "ina xa ki? Ni xan wanke maki kwanukan can" kmr xata yi kuka ta nufi sink ta soma wanke kwanukan da suka bata, tana gamawa ta bar kitchen din ta haura sama. Wayarta dake jakarta ta ciro dae dae lkcn da ya fara vibrate, Dr Sharif ta ga ke kiranta, da kmr baxata dauka ba har ya kusa katsewa sae ta dauka tayi shiru, tana jin yyi murmushi snn yace "Dama mutum na cin abincin da ba da sunansa a girka ba Zainab?, ae kwadayi knn" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "Zainab" murya can ciki tace "Na'am" yace "yhu ran away frm my lecture yau koh? Nasan maganin ki" turo baki tayi bata ce komae ba yace "Gidan yayan naku kike koma knn!" Girgixa masa kai tayi tace "gida na dawo" a hnkli yace "Toh am srry dear in dan ban ci abincin ki bne, am just nt hungry a lkcn coz i finished drinking coffee kika shigo office," Shiru tayi bata ce komae ba yace "kin hkura?" Dan murmushi tayi yace "Gud almost tym 4 sallat will call yhu ltr" katse kiran yyi dae dae lkcn da su Jiddah suka shigo, Jiddah tace "ke dae ki daina abinda kike Afeefah, kwata kwata yau ba ki shiga aji ba wllh" Afeefah ta Mike fuuu ta fice daga dakin, a stairs suka hadu da Mami tace "ki shirya ke da Sumayya ku kai ma Aliyu abinci" ta wara ido tace "toh Mami" snn ta juya da sauri ta koma daki, Wanka ta shiga tana fitowa ta dauki kaya mara nauyi ta sa snn ta saka hijab ta dauki wayarta ta fice daga dakin, falo ta tadda Sumayya na jiranta, Mami tace "saura in yi biyan bashi da ku" Afeefah tace "ae baxa mu dde ba" a dai daita sahu suka samu a bakin titi, suna isa Afeefah ta basa kudinsa tace ma Sumayya ta karbo canji ta nufi cikin gidan, bbu kowa falo hkn yasa ta haura sama ta bude dakinsa da sallama ta shiga, Yana xaune gefen gado da wani abokinsa dake rike da mug din tea yana sha, fadawa kansa tayi tace "yayanmu ya jikin" wani tsawa abokin ya daka mata yace "ke dalla ja can, baki iya sallama bne xaki fado ma mutane daki hka" daga kai tayi tana kallonsa lkci daya ta hade rae, Aliyu ya juyo fuskarta ya sakar mata murmushi yace "Da sauki little sis daga ina da magrib hka?" Mikewa tayi tana hararan abokin ta gefen ido ta fice daga dakin da sauri, Aliyu ya juya yana kallonsa yace "kaga ba fa na son hka khabir," khabir yace "ae ni haushi take bn tunda har ta kasa gane sonta kke 4 ol dis while, toh wae ma ni 4 God sake meye amfanin boye ma wnn yarinyar the truth abou everything, she is matured enuf, a fada mata matsiyinta a gidanku ka fito fili kace sonta kke, hka kawae tun yarinya bata san kanta ba kke wahala da ita kawae daga karshe duk abun nn ya tashi a aikin bnxa, ni in ma baxa ka iya gaya mata ba sae ni in mata bayani wllh" girgixa Kai Aliyu yyi yace "akwae dalilin da yasa ake boye mata ba hka nn kawae ba, its a long story yhu knw" mikewa Aliyu yyi ya fita daga dakin dae dae bakin kofa ya hadu da Sumayya rike da basket din abinci ta gaishesa tace "yayanmu Mami tace mu kawo maka," yace "to ngd shiga da shi daki" dakin ta shiga shi kuma ya sauka kasa ya samu Afeefah xaune a falo kiris ya rage ta fashe, ya karaso kusa da ita yana murmushi ya xauna gefenta ya jawota jikinsa tun kan yace komae ta fashe masa da kuka har da shessheka tace "yayanmu ni bna son wnn abokin naka ka gaya masa bbu ruwansa dani ya daina min mgna idan ba hka ba xan gaya sa da Abba" murmushi Aliyu yyi yace "yi hkuri Zainab, amma me yasa ba kiyi sallama ba" cikin kuka tace "Allah nayi kunnensa dae ne bae ji ba" Aliyu yace "toh ya isa hka nn princess xan ja masa kunne" shiru tayi ya shiga share mata hawayen fuskarta tace "Nace ma Mami baka da lfya shine ta ba mu tuwo mu kawo maka ni da Sumayya," murya can kasa yace "to ngdd little sis" a hnkli tace "ya ciwon kan yayanmu?" Ya dago kanta yace "Alhmdllh ya daina" tayi murmushi tace "Allah ya sauke," yace "Ameen" saketa yyi ya Mike yace "tashi ki je kiyi alwala mu xamu tafi mosque" tace "to yayanmu" snn ta mike. Suna idar da sllh ya Aliyu yace su xo su tafi tunda dare yyi, ba dan Afeefah ta so ba ta sa hijab dinta ya basu kudin transport snn ya rakasu har bakin titi suka hau a dai daita ya koma gida. Hka rayuwa ta ci gaba da kasancewa kullum son Afeefah na kara wahalar da Aliyu amma bnda abokinsa khabir bbu Wanda yasan halin da yake ciki, ko kaninsa Adnaan bae sani ba, a hka ya karaci kwanakinsa a kano kullum cikin tunanin Zainab har ya koma Lagos bakin aikinsa, Afeefah kam shakuwarsu ya 'da da karfi da Dr Sharif, har Maryam da take boye ma sarae tasan soyayya suke da Dr Sharif kai hatta 'yan ajin gaba daya sun dago don duk ran da xae shigo masu lecture ya ga bata front seat xae bata umarnin ta dawo gaba, gashi duk tambayar da xae yi a aji ita xae ma Kashi 60 cikin dari, idan bata amsa dae dae ba kuma ya korata daga class din, a can Kaduna kuwa Dad na ta Shirye shiryen hada bikin su ilham da Afeefah ba tare da yyi shawara da kowa ba don a tunaninsa gwara yyi komae kafin ya sanar da iyayenta na kano, shi kansa Dr Sharif bae san shirin da dad ke yi ba. Yau ya kasance laraba ana saura yan kwanaki a fara exams, Zainab dake xaune gefensu Maryam da ke ta karatu da wasu kawayensu ta mike da kyar ta dauki jakarta tace "Kunga ni na tafi Cikina na min ciwo wllh" Maryam tace "to kin sha magani?" Afeefah tace "nasha da safe!" Allah sauwake sauran Kawayen nasu suka mata snn ta bar wajen, Office din Dr Sharif ta nufa don xuwa ta ce masa xata wuce gida, yana xaune yana duba assignment din yan 400l, ta karaso ta xauna kmr xata yi kuka tace "Sir xan tafi gida" ba tare da ya kalleta ba yace "Ba inda xa ki, xa ku yi tutorial yau" "wayyo sir ka ga fa bni da lfya ne" sae a snn ya daga kai yana kallonta ya cire siririn farin glass din idonsa yace "me ya same ki?" Kmr me shirin kuka tace "Allah ka tambayi su Maryam na ma kasa karatu, shi sa xan tafi gida" yace "to ina ke maki ciwo?" Kin gaya masa tayi hkn yasa yace "to bbu inda xa ki, ni bnga rashin lfya a idon ki ba" "Sir don Allah kayi hkuri kaina ke min ciwo" drawern sa ya ja ya fiddo paracetamol yace "gashi ki sha xa ki samu relief kafin tutorial" kuka ta sakar masa tace "ni baxan sha ba gida xan wuce" yyi murmushi yace "next semester ba lallai ki gan ni ba ma bare in dinga damunki ki shiga karatu kina cewa A'a" tace "Sir ina xa ka?" Yace "inda na fito mana, I came to lecture for sometimes a nn, nd my period is over xan koma clinic, I have passed d knowledge I was ordered to, don hka xan koma bakin aikina" Afeefah tayi shiru tana kallonsa ba tare da ta shirya ba murya can ciki tace "xan yi missin dinka sir!" Ya wara ido yace "Really!" Rufe ido tayi da sauri don bata san lkcn da ta fadi hka ba, ya mike ya xagayo ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta har lkcn fuskarta a rufe, a hnkli yace "Zainab!" Ba tare da ta bude fuskar ba tace "um" yace "da gske xa kiyi missin dina?" A hnkli ta gyada masa kai, yyi murmushi yace "to sauke hannun" ba musu ta xame hannunta daga fuskarta, abinda bae taba furta mata ba ya furta mata ranan murya can kasa yace "I love yhu Zainab" shiru tayi tana kallonsa lkci daya ta sauke idonta kasa, a hnkli yace "Am srry Zainab!" Yana fadin hka ya kamo fingers dinta bata ankaraba sae ji tayi ya saka mata wani ring din axurfa karami me kyau yana kallon fuskarta yana murmushi yace "Will yhu Marry me!" Shiru tayi tana kallonsa, can ta sunkuyar da kanta, cikin sanyin murya yace "Zainab" kmr me tsoron magana tace "uhm" ya kuma maimata tambayar da yyi mata, ta gyada masa kai a hnkli cike da jin kunya, ya wara manyan fararen idonsa yace "da gske Zainab" murmushi tayi ta dauke kanta, murya can ciki yace "Allah sa har xuci" ya kusa minti biyu durkushe gabanta yana kallonta daga karshe ya mike ya koma table dinsa ya dauki makullin mota yace "Mu je in siya maki magani, tunda kina kunyar gaya min Dysmenorrhea (Menstrual cramps) ne matsarki" ba karamin kunya Afeefah ta ji ba ta mike da kyar kanta a sunkuye ganin kallonta yake, ta nufi kofa, yyi murmushi ya bi bayanta. Wani pharmacy a wajen sch ya tsaya, ya siya mata mugunguna snn ya nufi gida da ita. Dai dai gate dinsu yyi parkin ya dauki ledan maganin ya mika mata ya gaya Mata ynda xata sha, kanta a kasa ta karba tayi masa gdya ta bude motar ta fita da sauri, bin ta da kallo yyi yana murmushi har ta shiga gida.
Chapter 36 · 0% Book details