← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 89

Sashe 31

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

41.....
Sae da suka hau main road ba tare da Dr Sharif ya kalleta ba yace "Ina kike son in kai ki Zainab?" Shiru tayi bata ce komae ba, can kuma a hnkli tace "nima bn sani ba" yace "Ma'aruf bae taba fita dake bne duk xuwan ki hutu kd?" Ta girgixa masa kai tace "ae shi ba nn yake ba" Dr Sharif yace "yea hka ne na manta, bari mu je to ki ga state university din kaduna, da polytechnic dinsu, ko kin taba xuwa?" Girgixa masa kai tayi, ya nufi hanyar unguwar rimi, har cikin kasu ya shiga da ita, sae a snn Afeefah tace "Sir wae nn ne?" Dariya yyi yace "da fa, ga dayan a gaba shima xan shiga dake" tabe baki tayi tace "ko kyau, North west din mu ya fi kyau!" Dariya yyi ssae yace "kai bari yan Kaduna su ji ki bbu ruwana" dariya tayi tace "to ni ina ruwana da su daga na fadi gskya?" xagawa da ita cikin kasu yyi gaba daya, sae tabe baki take, ita a dole bae mata ba daga karshe tace "ni dae sir na gani, mu tafi kawae" yyi murmushi yace "to mu je tudun wada ki ga polytechnic dinsu na science?" Tabe baki tayi tace "ni bn san wajen ba" yace "ae nuna maki xan yi" tace "tohm mu je" polytechnic din art dake unguwan rimin ya fara nuna mata yace "akwae wani a barnawa ma, but ynxu na tudun wada xa mu" suna isa junction road yace "kalli can ki ga stadium dinsu" juyawa Afeefah tayi da sauri tana kallon inda yake nuna mata ta xaro ido tace "wnn dan wurin sir?" Dariya yyi ssae yace "don baki shiga bne" ta tabe baki tace "um ni dae dan karami ne" kwafa yyi yace "bbu ruwan sir dae, bari yan kd su ji ki su kama ki" dariya tayi tace "ni ina ruwana da su" ta sardauna crescent ya shiga sbda traffic, ta ce "Sir Dubi fa titin mu ma ya fi nasu girma da kyau ssae" yyi murmushi yace "eh mana" cikin mintunan da basu wuce goma ba suka isa poly road, Afeefah ta xaro ido tace "Sir nn ne polyn nasu?" Yace "yea" tace "kai shine yayanmu ke wani cewa makarantun kd sun fi namu ashe ba hka bne" dariya kawae Dr Sharif yyi ya nufi main gate din k.p.t, ya karbi gate pass ya shiga, dariya kawae Afeefah ta dinga yi ita a dole ta raina polyn, Dr Sharif ya girgixa kai yace "kin san shekaran polyn nn nawa?" Ta girgixa kai, yace "uhm ki bar raina sa, babban makaranta ce yarinya," tace "bn yadda ba, ka gaya min shekaran sa nawa!" Yace "this polytechnic was founded in 1956! Ki lissafa shekarunsa ki ga tun kan Independence, ya fi north west din nn naku da kike brag da iyakacinsa shekara biyar, kin manta slogan din kadunan ne wae? 'Center of education! Let me remind yhu" Afeefah ta saka dariya tace "kai Sir" murmushi yyi ya xaga da ita cikin polyn gaba daya snn suka fita ya shiga da ita ostrich bakery dake wajajen ya siya mata snacks kala kala, suka kama hanyar U.rimi, ya juya yana kallonta yace "its almost 6 pm da mun shiga gamji in ji cmmnt din ki, nd beside ma it's nt decent mu shiga da yamma" Shiru tayi bata ce komae ba, murya can kasa ba tare da ya kalleta ba yace "Mu je muyi hoto?" Shiru tayi kmr me naxarin abinda yace, sunanta taji ya kira, ta dago manyan idonta tana kallonsa a hnkli yace "Mu je studio muyi hoto nace?" Dauke kanta tayi, sae kuma tayi murmushi ta gyada masa. Hadadden studio ya nufa yana gama parkin ya juya yana kallonta yace "mu je" bude kofar tayi ta fito shima ya fito, yana gaba tana biye da shi suka shiga studio din, Afeefah taji baxata iya hoton ba bayan Sun shiga sbda kunya, ma'aikatan wajen duk a tunaninsu pre wedding pics suka xo yi, Dr Sharif yyi murmushi yace nml pic suka xo dauka, da kyar Afeefah ta iya tsayawa suka yi hoto da Dr Sharif tsabar kunya sae wani rurrufe fuska take, kala hudu kawae suka yi ya biya kudin suka ce su dawo gobe su karba bayan sun tura ma Dr Sharif a wayarsa, kasa kallon Dr Sharif Afeefah tayi har suka shiga mota, Eatry taga yyi parkin ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar ya mika mata ledan hannunsa, ta karba ba tare da ta kallesa ba, ya tada motar suka nufi gida, Dr Sharif na gama parkin bayan sun isa gida Afeefah ta bude motar ta riga sa fita da sauri tayi cikin gida, Amina dake kitchen ta fito tace "sannun ku da dawowa" Afeefah tayi murmushi kawae ta ajiye ledan hannunta tace "ina Fadil Anty?" Amina tace "tare mu ke girkin a kitchen ae, gashi can cikin kekensa" dariya Afeefah tayi ta mata sannu da aiki ta nufi sama da sauri kafin Dr Sharif ya shigo.
Bayan isha Ma'aruf yace da Dr Sharif "ya mgnr daxu Dr, mu tafi gun dad din ne ynxu? naji kace gobe xa ka koma!" Dr Sharif yace "to mu tafi frnd" takwas da kusan rabi suka isa can gidan, Dr Sharif yace "look captain kunyan dad nake wllh, just go in and explain to him" Ma'aruf ya hade rae yace "kaga matsala ta da kai koh" Dr Sharif ya marairaice masa yace "don Allah ka rufa min asiri kai ka shiga I just cnt go in" tsaki Ma'aruf yyi ya bar sa cikin motar ya nufi cikin gidan, ba karamin farin ciki dad yyi da xancen da Ma'aruf ya xo masa da ba, dad yace "ae wnn ba matsala bne in har uwar tawa tana so, kaga sae a hada da nasu jamila kawae, ka xo min da ita gobe mu ji ta bakinta" Ammi dake xaune falon tayi shiru dae tana kallonsu bata ce komae ba, dad ya juya yana kallonta yace "ko ya kika ga Uwar gida?" Sauke ajiyar xuciya tayi tace "Amma kuma Alhaji naga ae yana da kyau a fara jin ra'ayin iyayenta na kano ka ga ba wajen mu take ba bare kayi saurin yanke hukunci hka!" Dad ya hade rae yace "ji wani xance don Allah, da nan da can din ba daya ba mne, kuma nasan baxa su ce don me ba, don duk abinda na yanke tamkar su suka yanke ne" Ammi tace "To Allah rufa asiri, amma Dr Aliyu kam mutum ne, Allah dae ya xaba abinda ya fi alkhairi" Dad yace "yauwa xancen knn, Ameen ya Allah" Ma'aruf ya sallami iyayen nasa ganin ya bar Dr Sharif a waje snn ya bar gidan, Yana shiga motar ya sakar ma abokin nasa murmushi yace "In'sha Allah kmr ka samu Zainab frnd" murmushi Dr Sharif ya mayar masa yace "I trust yhu captain" goma saura suka isa gida, Amina tayi masu sannu da xuwa snn ta dauko masu abinci ta ajiye masu tsakiyar rug din falon ta nufi sama, Afeefah na shirin kwanciya Amina tace "kaddai har xa ki kwanta" Afeefah tayi murmushi tace "um bacci xan yi" Amina tace "to baki tafi kin ma Sir sae da safe ba yace baxae kwana nn ba" Afeefah ta kauda kanta a hnkli tace "toh" dariya Amina tayi ta fita daga dakin, Afeefah ta mike ta sa hijab dinta har kasa snn ta fita daga dakin ta sauka downstairs. Xaune ta samesa da Ma'aruf, ta karaso cikin falon kanta a kasa ta xauna daga kasa, cike da xolaya Ma'aruf yace "kin sakko fira knn" bata fuska tayi tace "A'a" yyi dariya ya mike yace "bari to in baku waje." Sae dae Ma'aruf ya haura sama snn Dr Sharif ya juya yana kallon Afeefah yace "har kin gama jin Kunyan" rufe fuskarta tayi da sauri yyi murmushi yace "to dawo nn" bata masa musu ba kanta a kasa ta dawo gefensa ta xauna daga kasa. Wayarsa ya mika mata yace "kin ga hoton da kika ki gani daxu" murmushi tayi ta karbi wayar tana kallon hoton nasu, ba karamin kyau suka yi ba barin Dr Sharif, tace "um bayan ka fini kyau!" Yace "kin dae fini" sunkuyar da kanta tayi tace "bn yarda ba" Ma'aruf ne ya sakko downstairs ya shigo falon da sallama yana mika ma Afeefah waya yace "ga yayanki" ba karamin faduwa gabanta yyi ba, ta karbi wayar da kyar, juyawa Ma'aruf yyi ya koma sama, sarae Dr Sharif ya lura da halin da Afeefah ta shiga, wayar na soma ringing ta daga a sanyaye tace "yayanmu!"

Eeshatullah Goni😘

🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 31 · 0% Book details