← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 89

Sashe 24

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yau ya kasance laraba kuma ranan da su Afeefah xa su kare exams dinsu, sanye take da atamfarta red colour da blue ta daura farin lab coat kan kayan nata tayi rollin kanta da black gyale karami ta sa flat shoe fari, ba karamin kyau tayi ba ranan duk da bata yi make up ko kadan ba don bata taba shiga skul ba hijab ba sae ranan, shima kuma don practical xa suyi na exams, Maryam ma sanye take da lab coat din da alamar laboratory xa su da safen, Maryam da ke ta kallonta tace "gskya Afeefah kin cije ni yau" Afeefah ta harareta bata tanka ta ba, wani faduwar gaba ne ya xo mata ganin Dr Sharif shima da alamar laboratory xa shi don sanye yake da white lab coat din shima, sak likita idan ka gansa, sunkuyar da kai tayi ta rasa dalilin da yasa duk lkcn da xata gansa sae ta ji faduwar gaba ba kadan ba, Maryam kam kasa daina kallonsa tayi, ba ita kadae ba har 'yan matan dake wajajen, wasu sae gaishesa suke yana sakar masu murmushi yana amsawa. Da kyar Maryam ta iya bude baki ta gaishesa ganin kusan a tare suke tafiyar ya amsa yana kallon wrist watch din hannunsa yace "so early hka xa ku lab?" "Um" kawae Maryam tace ba tare da ta kallesa ba, shi kam sae satan kallon Afeefah yake, dai dai lkcn da ta dago ita ma ta saci kallonsa suka hada ido, dauke kai tayi da sauri tana murmushi kmr munafuka murya can kasa tace "Gud morning sir" bae tanka ta ba yana kallon Maryam yace "hope yhu guyz are ready for the exam?" Maryam tace "in'sha Allah sir" yace "dats gud, Allah bada sa'a" ta amsa da Ameen, ya kuma kallon Afeefah ya dauke kai snn ya bar su nn suna jan kafa ya nufi lab, Maryam tace "ina son maki tambaya Afeefah" Afeefah ta dago tana kallonta tace "ina jin ki" Maryam ta dan yi shiru, har sae da Afeefah tace "kin yi shiru kuma" Maryam ta kirkiri murmushi tace "ki gaya min tsakanin ki da Allah meye tsakanin ki da Dr Aliyu Sharif" Afeefah ta dan hade rae tace "kmr ya" Yake maryam tayi tace "ko kuma ma dae mu je lab, am only joking" Afeefah bata tan ka ta ba har suka isa lab din. Karfe sha daya suka fito daga exam, Afeefah ta nufi cafeteria Maryam dake bin ta a baya tace "ya exams din?" Afeefah tace "Alhmdllh," Maryam tace "to Allah ba mu sa'a" a takaice Afeefah tace "Ameen" bayan ta xauna kujera ta fiddo wayarta, text din Dr Sharif ta gani, ta bude ta karanta content din, "Yhu look awful bbu hijab yau Zainab, Hijab rufin asirin 'ya mace, kar ki kuma irin shigar nn ki xo sch plss" dan tabe baki tayi, dai dai lkcn da wani text din nasa ya shigo wayar kuma, "ina maki magana daxu a lab shine kika yi ignoring dina koh?" Reply ta mayar masa kmr hka, "ae nayi xaton da 'yan matan nn naka kke shi yasa," bae mata reply ba ta yi tsaki ta mayar da wayarta jakarta, Maryam da a tunaninta tun tambayar da tayi ma Afeefah daxu ne yasa ta daure fuska tace "me xa ki ci?" Afeefah ta girgixa kai tace "A'a na koshi ni" ko rufe baki bata yi ba Dr Sharif ya karaso cafeterian yan matan da tace yana ma mgna a lab daxun na biye da shi a baya, kujera ya ja ya xauna gefen Maryam yace "Ya exams Maryam?" Maryam ta kirkiri murmushi tace "Alhmdllh," yace "Ma'sha Allah, wishing u ol success, no carry over in'sha Allah" murmushi kawae Maryam tayi tace "Ameen" yan matan guda biyu dama duk sun xauna, ya juya yana kallon su yace "wani drink xa a kawo maku?" Duk suka ce fanta, Afeefah dae sae Satan kallonsu take tana yin kmr tana danna wayarta don yan matan ba karamin haduwa suka yi ba, fanta hudu yasa aka kawo na roba da snacks ya mika ma matan biyu ko wanne daddaya snn ya ba Maryam ma, Afeefah kuma ya ajiye mata gabanta, dauka tayi da sauri ta mayar masa ba tare da ta kallesa ba tace "Thanks bna jin yunwa" murmushi yyi ya bude shi ya fara sha, fira kawae yake da 'yan matan dake ta basa lbri, Afeefah ta Mike ta saka wayarta a jaka ta xuge snn ta gyara blck veil din kanta don har lkcn lab coat na jikinta tana kallon Maryam tace "sae mun yi waya" tana kai wa nn ta fice daga cafeterian yan matan suka bi ta da kallo, ta nufi inda ta saba xama ta jira su jiddah, bayan minti biyu da fitan ta Dr Sharif ya mike yana kallon yan matan da Maryam yace "excuse me, xan dan yi makin phone call" ya fice daga cafeterian ya nufi inda yasan xai ganta, xaune ya sameta tana danna wayarta kamshin turarensa kadae yyi announcin mata presence dinsa a gun, "Zainab!" Juyawa tayi tana kallonsa, ya xauna dan nesa da ita yace "me na maki kike fushi?" Hawaye ne ya taru idonta ta ki cewa komae sae jujjuya wayar hannunta take, yyi shiru yana kallonta, mota ne yyi parkin dan nesa da inda suke xaune, Afeefah ta kafa ma motar ido ganin kmr motar ya Aliyu, to amma ae bae dawo ba, wayarta ne ya fara ring a take, taga Aliyun ne ke kiranta, ta daga yace "Am in ur sch Zainab," wara ido tayi tace "Da gske yayanmu ka dawo ne" inda yyi parkin kawae ya gaya mata, ta juya tana kallon Dr Sharif tace "kaga motar yayanmu na Lagos ne can, he came to pick me," Dr Sharif yace "OK in je mu gaisa?" Shiru ta dan yi sae kuma tace "to" mikewa tayi ta nufi motar gabanta na faduwa Dr Sharif ya bi bayanta.

Eeshatullah Goni😘😘

🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 24 · 0% Book details