← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 89

Sashe 75

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

92___93
Tun daga wnn rana Zainab ta fara tunanin anya Mami ce ta haifeta kuwa dama, don kusan kullum sae ta sa ta kuka ta kuma hana 'yan uwanta rabanta wae kar ta koya masu mugun hali, don ma Ya Aliyu baya bari wani lkcn, gaba daya ta tattara ina ta inata ta koma dakin ya Aliyu, dare ne kawae ke raba su ko bae nn hka xatai ta xama ita kadae a dakin, kwata kwata abinda Mami ke mata a gidan bae fiye damunta ba tunda ga ta ga yayanta. Tun bata fita idda ba take son komawa schh ba dama har dae ta fita amma Mami taki bari ta koma, abun ya dameta ssae, bbu ynda Aliyu bae yi da Mami ba amma tace bata san xance ba. Hatta Abba bae jin ddin abinda Mami ke ma Zainab a gidan, yyi mata magana har ya gaji ya kyaleta, har Zainab bata fatan yayanmu ya fita don kafin ya dawo sae tayi kuka fiye da sau biyar, Adnaan kam ko a jikinsa don bae ma bin ta kanta, hkn yasa duk inda ya Aliyu xa shi wani lkcn yake tafiya da ita. Da sallama Mami ta shiga falon mai gidanta ta nemi guri ta xauna don amsa kiran da ya aika Adnaan yyi mata, Abba ya gama danne dannen laptop dinsa yace "Zuwaira kan maganar Zainab ne, wae fisabillilah me yasa kike nuna min bni da iko kanta ne, nace ki barta ta koma boko kinyi kunnan uwan 'yan shegu da ni" Mami ta fara hawaye a sanyaye tace "Ba hka bne Alhaji, kaga har yau bamu san laifin da tayi ma yaron nn ba taki fada, da ganin ba karamin abu bne, ni ins tsoron komawarta makaranta kuma gskya gwara tayi ta xama har Allah ya fito mata da wani mijin" Abba ya dan yi murmushi yace "Wnn ba hujja bace Zuwaira" Mami tace "Ni dae don Allah kayi hkuri ba wae naki taka bane, amma gskya Zainab tsoro take bn ynxu, kwata kwata bata da gskya naga alama, idan tayi wani auren ta ci gaba da karatun amma ynxu kam mu yi ta xama" Abba yace "Toh shknn, Allah ya fiddo mata da na gari" Mami tace "Ameen, bari in karasa abinda nake" daga hka ta fita daga dakin. Da daddafe Afeefah na xaune gefen yayanmu tana kallon abinda yake a laptop, fadila ta shigo tace "yayanmu Abba yace ka je," yace "OK kin gama assignment din ne kike chat" ya fadi hkn yana kallon wayar da ya gani hannunta, tace "A'a ba chat nake ba wllh, koya min ake online" hararanta yyi yace "Keep quiet an taba karatu online, kwashe kwanukan can ki fita da su," ajiye wayar hannunta tayi ta kwashe plates din da kula dake dakin ta fita da su, Afeefah ta juya tana kallon wayar taga kan whtspp take, tace "Karya take yayanmu dubi chatting fa take" daukar wayar tayi tana kallon da wanda take chat din, ga mamakinta sae ta ga kmr nmbr Dr Shariff, ae ko taga shi din ne, ta bude chat din ta shiga dubawa, taga yawanci duk karatu yake mata na Biology da Chemistry, ynxun ma ans din biology yake tura mata, a lkcn ma yake typn din, ajiye wayar tayi da sauri ta ci gaba da kallon abinda yayanmu ke yi jin fadilan na hauro wa sama, ta shigo dakin ta dauki wayarta xata fita yayanmu yace "Ki ajiye wayar nn ki yi assignment kar in bata maki rae fadila" a hnkli tace "Toh" kafin ta fita, Aliyu ya mike yace ma Afeefah yana xuwa Abba na kiransa tace "Toh" snn ya fita ya bar mata laptop din, kasa ya xauna yana kallon Abbansa yace "Gani Abba." Abba ya ajiye remote din hannunsa bayan ya rage volume din kallon da yake ya maida hnklinsa ssae kan Aliyu yace "Wani laifi Zainab tace maka tayi ma mijinta tsakanin ka da Allah Ali?" Aliyu ya daga kai yana kallon Abbansa yace "Wllh bata gaya min ba Abba, tace ita bata yi masa komae ba" Abba yyi shiru na kusan minti uku kafin ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta" Aliyu yace "Ameen" Abba bae kuma cewa komae ba, hkn yasa Aliyu ya maida hnklinsa kan tv, bayan wasu mintunan Abba ya nisa yace "Ali kana da ra'ayin auren Zainab har ynxu" da sauri Aliyu ya juya yana kallonsa, sae kuma ya girgixa kai yace "A'a Abba bni da wnn ra'ayin ynxu" Abba yace "Koh saboda me?" K'asa ba Abbansa amsa yyi lkci daya yaji wani takaici ya rufesa ga tukukin da xuciyarsa ya shiga yi masa, me kuma xae yi da Zainab, cikin dakewar murya yace "Sbda nayi ma wata alkawarin aure Abba" Abba yyi shiru yana kallonsa kafin yace "Baxa ka hada su ba Ali, ba don Mahaifiyar ku xaka aura Zainab ba sae don ni" girgixa kai yyi yace "kayi hkuri Abba ka min uxuri, bni da ra'ayin hada mata biyu, da ma ban ma wancan alkawari bne xan iya hakura da ita," Abba yace "Toh shknn Allah tabbatar da Alkhairi Ali" Da kyar Aliyu yyi cewa Ameen, Abba yace "Shknn xaka iya tafiya" mikewa yyi ya masa sae da safe snn ya fice daga falon, Kwance ya same Zainab kan gadonsa har ta fara bacci, kallo daya yyi mata ya dauke kai ya kashe laptop dinsa ya rufe ya ajiye snn ya shiga tashinta, mikewa xaune tayi da sauri tana murxa ido tace "Na'am" ba tare da ya kalleta ba ya wani hade rae yace "Tafi ki kwanta" shiru tayi tana kallonsa, sae kuma ta dawo kusa da shi ta xauna cikin sanyin murya tace "Abba ya maka fada ne, me kayi masa yayanmu?" Sae a snn ya juya yana kallonta ya dan mata murmushi ya Girgixa kai yace "A'a kawae bacci nake son in yi little sis am tired" sakkowa ta daga kan gadon ta kuma gyara masa bedsheet tace "Toh ka kwanta yayanmu" kwanciya yyi kan gadon ta dauki hijab dinta tace "Gudnyt!" Bae tanka ta ba har ta isa kusa da switch ta juya tana kallonsa tace "In kashe maka wuta yayanmu?" Yace "Yes" kashe wa tayi ta kuma yi masa sae da safe ta fita ta kulle masa kofar, yyi rub da ciki ya runtse ido xuciyarsa na xugi, ko kadan bae ji ddin xancen da Abba yyi masa ba don shi kam ya hakura da Zainab, daren ranan bae yi bacci ba maganan Abba ya tsaya masa duk ya tuna sae ransa ya baci, shi da yana da xuciya ma ae baxae kuma xama gidan ba, mikewa yyi misalin sha daya ya koma bangaren Abba ya shirga masa karyar akwae aikin da yake a UK gobe yana son komawa amma baxae dde ba, dad yyi masa fatan alkhairi snn ya fita, sae a snn hnklinsa ya kwanta don yana son ya nisan ci Zainab kada a tursasa shi aurenta.
Washegari har Karfe goma da wani abu Zainab bata shigo dakinsa ba which ix vry unusual of her, hka kawae ya damu da son sanin halin da take ciki don yasan kila bata jin ddin ne amma ya ki xuwa dubata stil, kasa daurewa yyi daga karshe don ko breakfst ya kasa don tare suke yi da safe, gashi duk yaran gidan sun tafi makaranta bare yace su dubo mashi ita, mikewa yyi ya fita daga dakinsa ya nufi nasu, kwance ya sameta cikin bargo ta takure waje daya idonta lumshe, ya yaye bargon yana kallonta ya daura hannu goshinta a hnkli, da sauri ta bude ido ganinsa ta mike xaune tace "Yayanmu" da damuwa yace "Baki da lfya ne little sis?" Bata fuska tayi kmr xata yi kuka a hnkli tace "Cikina ke ciwo yayanmu" yace "on ur period?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, ya xauna gefenta ya kamo hannunta da damuwa yace "ohh Sorry kin sha xaki dayawa month din knn koh?" Ta shagwabe masa tace "Ni ba abinda na sha yayanmu ae kana gani" yace "Toh naji sakko mu tafi kiyi breakfast sae mu je in siyo maki magani koh" daure mata gashinta da ke kwance bayanta a barbaje yyi ya taimaka mata ta sakko daga kan gadon ta dauki xani ta daura kan kayan baccin jikinta suka fita daga dakin, ya shiga nasa da ita, tea ya lallaba ta tasha da kyar kafin ya mike ya dauki makullin motarsa yace "Mu je" tace "Ka fara yin breakfast tukun yayanmu" dago ta yyi yace "No muje in siya maki magani tukun little sis" daga hka ya kama hannunta suka fita daga dakin bayan ta sa hijab, Mami dake gyare gyare a falo ta bi su da harara har suka fita. Tun a mota ya bata maganin ta sha bayan ya siya snn suka dawo gida ya sa ta kwanta a dakinsa, ta dde tana juye juye yana mata sannu kafin bacci ya dauketa. Ko da Afeefah ta farka da yamma tsaye ta gansa yana hada kaya, mikewa xaune tayi da sauri tana kallonsa tace "ina xa ka yayanmu?" Ya Juya yana kallonta ya sakar mata murmushi yace "Am travelling princess, ya cikin ya daina?" a sanyaye tace "ina xaka?" Ya dauke idonsa daga kanta yace "UK xan tafi wani aiki" hawaye ne ya cika idonta tace "Plss kar ka tafi ka bar ni ni kadae yayanmu" juyawa yyi yana kallonta sae kuma ta fashe da kuka, ya karaso jiki ba kwari ya xauna gefenta yace "Kiyi hkuri Zainab, aiki xan tafi ba ddewa xanyi ba" bata ce komae ba sae share hawayen da yaki tsaya mata take tana kallonsa, duk jikinsa yyi sanyi tausayinta ya rufe shi don yasan shi kadae ne farin cikinta a gidan, shi kuma sbda maganar da Abba yyi masa yake son barin kasar don takaici, da ya tuna xancen Ahmad na cewa me xae yi da ita ko da sun rabu da mijinta sae ya ji wani bacin rae don yasan gskya Ahmad ya fadi, ya harde hannunsa da nata ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Baxan dde ba princess" kai kawae ta gyada masa hawaye na sakko mata. Karfe biyar saura ya gama shirinsa ya juya yana kallonta ganin ynda tayi tagumi tana kallonsa ya sa shi murmushi, ya dawo kusa da ita yace "kiyi xaman ki dakina har in dawo, kuma ki dinga hkuri da kowa kin ji" kae kawae ta gyada masa hawaye cike idonta, ya mike cike da tausayinta ya bar dakin don xuwa yi ma Mami sallama, duk ynda ya so ta fito ta rakasa ko bakin gate kin fitowa tayi sae kuka take, ya bata kudi me yawa ya kuma ce ta dinga shan maganinta har cikin yyi mata sauki, sae da ya isa bakin kofa ya daga mata hannu, ta mike ta isa inda yake da sauri ta shige jikinsa, rungumeta yyi ya lumshe ido, sun kusa 3 min a hka kafin ya banbareta jikinsa ya fita daga dakin rike da jakarsa. Hka kawae ya K'asa tafiya airport ya nufi gidansa na Nasarawa, yasan har ynxu yana son Zainab ga tausayinta da yake amma bae jin xae iya aurenta, tunanin hkn ya sa shi hawaye ssae, hka ya kwana ranan bae da sukuni ga shi ya kasa daina tunaninta ko wani hali take ciki, ita ma hka tun tafiyarsa take kuka taji gidan yyi mata xafi, bbu me shiga tsabgarta don Mami ta hana, hka tayi ta xama dakinsa kmr mayya, bbu wnda ya damu ya kawo mata abinci ko yace taje ta xuba, don hka bata ci komae ba, har kwana uku Aliyu na Kano bae tafi ba sae dae duk ya kashe wayoyinsa, ya rasa gane me yasa ya kasa barin Nigeria. Mami kasa daure ci gaba da share Zainab tayi bayan tafiyar Aliyu don tasan ynxu bbu me sa ta farin ciki har ta dinga shanye abinda ake mata, da can ma abinda yasa ta fita harkarta gaba daya sbda tasan yana nn ne ta kuma san baxae barta cikin damuwa ba, da kanta ta dinga kai mata abinci tana sa ta tana ci, ta kula bata da aiki sae na kuka duk da bata yi gabanta sae dae da ganin idonta xa ka gane, bayan kwana biyu da barin sa gidan ta fara rashin lfya, rashin lfya da ya daga ma Mami hnkli ssae ganin ynda take jin jiki, kwanansu biyu asibiti ranan Mami na xaune da ita a ward tayi tagumi, ita ko tana xaune ancire mata drip din hannunta tana cakalkala abincin gabanta, Mami ta kira sunanta, a hnkli ta dago tana kallon uwar tata, cikin sanyin murya Mami tace "ki gaya min me ke damun ki Zainab" shiru tayi tana kallon uwar tata kafin ta sunkuyar da kai hawaye ya xubo mata a sanyaye tace "Yayanmu ya tafi ya barni Mami, ku ce masa ya dawo don Allah"
Chapter 75 · 0% Book details