Sashe 78
Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kirasa ya je, duk ynda ya so ta koma dakinsu ta kwanta kin yadda tayi wae idan ta tafi xae wuce, Mami na shigowa bangaren mijinta yyi mata bayanin xancen da Ali ya xo masa da shi, Murmushi tayi ba tare da ta kalli mai gidan nata ba sbda nauyin da ta ji tace "Allah tabbatar da alkhairi" ya kula da hkn, yyi murmushi kawae yace "Ameen, gobe sae in je kaduna in masu bayani". Washegari Mami ta kira manyan yaranta mata tayi masu bayani kmr ynda Abbansu yyi mata, ssae suka yi farin ciki da xancen gaba dayan su, nn take suka fara fadin ynda xa a shirya abubuwa, Mami dae shiru tayi tana kallon 'ya yan nata, duk wnn abinda ake Afeefah bata sani ba, a ranan Abba ya bi flight ya tafi Kaduna, iyayenta na Kaduna ma suka yi murna da jin hka barin dad din ma'aruf, nn take ya bada sadakin Aliyu dubu dari biyu, Abba yyi masa gdya ya bar Kaduna bayan sun sa daurin auren sati biyu daga ranan. Abba na sauka gida ya sa aka kira masa Aliyu ya gaya masa ynda abubuwa suka tafi a can Kaduna ya kuma ce ya kira dad din Ma'aruf yyi masa gdya. Ranan friday da yamma da ya kama saura sati daya bikin yana xaune dakinsa da Zainab dake kwance tayi rub da ciki gefensa tana game a laptop dinsa, ganin ynda yake kallonta yasa ta Mike xaune tace " Me ya faru yayanmu?" Sauke idonsa yyi daga nata yyi murmushi ya kamo hannunta yace "Nothing" ta langwabar da kai tace "Toh tunanin me kake" ya dan wara ido yace "Nothing" daga hka ta juya xata kuma kwantawa ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Ina son maki tambaya Zainab" dawowa kusa da shi tayi tana kallonsa tace "Na me yayanmu?" A hnkli yace "Xa ki iya aure na?" Still tayi na kusan second talatin tana kallonsa ko kiftawa bata yi, kmr me rada yace "Zainab" boye fuskarta tayi da sauri a kirjinsa, yyi shiru yana kallonta, a hnkli ya shiga dago kanta amma taki bari, murmushi yyi yace "Kin yi shiru" mikewa tayi da sauri xata gudu ya rikota, ta boye fuskarta jikin gado kmr munafuka, dariya ta basa ya duka dab da ita yace "next friday xaki min bayanin ma'anar kunyar nn da kika ji idan an kawo min ke gidana" kwace kanta tayi da gudu ta fice daga dakin ta nufi na su, kwata kwata bata san me ke faruwa gidan ba, taga dae ana ta siye siyen kayan abinci, ta kuma ji wae Anty Safiya ta fita Dubai siyayya, kusan kullum kuma sae sauran Aunties dinta sun tafi kasuwa amma bata san me xa ayi ba kuma bata tambaya ba, bbu wanda ya gaya mata kuma, dakinsu ta shiga taga wasu ubansun lace kusan kala takwas duk iri daya red da ratsin silver da ash a jiki, da gani anko ne, snn ga atamfofi ma duk iri daya biyu kadae ne daban, juyawa tayi cike da son sanin me ke faruwa gidan nasu ta fita ta nufi dakin Mami, xaune ta sameta ita da aminiyarta Hajiya fatee suna xuba turarurrukan wuta masu ddin kamshi cikin lafiyayyun kwalaben da aka yi domin su, suka amsa sallamarta, ta karaso kusa da Maminta ta xauna, a hnkli tace "Mami me xa ayi naga ana siyo kaya, Mami ta daga kai tana kallonta kafin tayi murmushi tace "Je ki tambayi yayanki" ta dan yi shiru kafin tace "Me xance masa?" Mami tace "Tambayar da kika min xa ki masa mana" bnda dariya bbu abinda hajiya fatee ke yi, bata kuma cewa komae ba ta mike a hnkli ta fita daga dakin ta koma nasu, Mami tayi murmushi ta ci gaba da abinda take, Hajiya Fatee tace "Allah sarki". Afeefah na kwance dakinsu don ta ki komawa gun yayanmu su Anty baby suka dawo, sun yi Mamakin ganinta a dakin don bacci kadae ke shigo da ita da daddare gaba daya dakin yayanmu take yini duk kayanta ma suna can, gashi kuma sun ga motarsa alaman yana gida, to ko bae nn ma bata shigowa cikinsu, ta mike xaune da sauri tace " Anty wae me xa ayi a gidanmu?"