← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 89

Sashe 54

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Afeefah ce xaune gefen gadon ta xuba uban tagumi tana kallonsa, Saleem ya shigo dakin da sallama Dr Faisal na biye da shi a baya, yana kallonta yace "Zainab ki tafi ki kwanta in ji momy sha biyu fa ya kusa, mu xa mu kwana a nn" kmr xata yi kuka tace "Ni don Allah ya saleem a bar ni a nn, ni ba bacci xan yi ba wllh" Saleem yace "Ance maki bacci yake ynxu ki tafi ki kwanta Zainab, ni da Dr xa mu tsaya da shi a nn" hawaye cike idonta tace "Don Allah fa nace," kallon Drip din jikin Dr Sharif Saleem yyi snn ya kalli Dr Faisal yace "nn da awa nawa ruwan xae kare?" Dr Faisal yace "xuwa karfe uku da wani abu idan Allah ya kai mu" Saleem ya kalleta yace "Xan dawo anjima, kuma ina dawowa xa ki tafi ki kwanta," shiru tayi bata ce komae ba ya fita dakin tare da Faisal, kan su rufo kofar tayi saurin cewa "Ya saleem, ya Aliyu fah?" Saleem ya juya yana kallonta yyi murmushi yace "Sae ynxu kika tuna sa, muna fitowa daga asibiti yace gidan abokinsa xae tafi ya kwana, amma gobe xae shigo da safe" kai kawae ta gyada masa snn ya rufe kofar. bayan kusan minti goma dad ya shigo dakin yana kallonta cikin tautasa murya yace "Mamata ki tafi ki kwanta kinga shi ma bacci yake" kmr xata yi kuka tace "Don Allah dady a bar ni in tsaya da shi ni ba bacci nake ji ba wllh" hawaye cike idonta ta kare maganar, yyi shiru yana kallonta snn ya mayar da dubansa ga Dr Sharif ya dde tsaye dakin daga bisanni ya juya ya fita rae a dagule, duk wnn abinda suke gaba daya Dr Sharif na jinsu sae dae bae bude ido ba, bae kuma nuna alaman ya tashi ba. Sha biyu da kusan rabi Afeefah dake xaune gefen gadon taji ta fara jin bacci ssae, kallon Dr Sharif tayi idonsa a lumshe har lkcn, a sanyaye ta daura kanta gefen pillon da yake kwance ta takure waje daya ta lumshe ido. A hnkli ya xame kansa daga kan pillon da ya gane tayi bacci, da kyar ya mike xaune ya tuge alluran drip din hannunsa ya sakko da kafafuwansa kasa ya dafe kansa da yyi masa nauyi lkci daya hawaye ya taru idonsa. Firgit Afeefah ta farka ta mike xaune da sauri tana kallonsa, da sauri ta xamo kasa daga kan gadon tana ci gaba da kallonsa tace "Sir ka tashi?" Kasa dago kai yyi bare ya tanka ta, hkn yasa ta kuma kiransa nn ma shiru, kmr xata yi kuka ta mike ta dago kansa a dan tsorace tana kallon fuskarsa, lkci daya hawayen dake makale idonsa ya xubo fuskarsa, rudewa tayi muryarta na rawa jin xafin jikinsa snn ga hawayen da ya ke tace "Sir me ya same ka? Dama baka da lfya ne" Kasa bata amsa yyi sae hawayen dake xubo masa ssae, yyi saurin rike kansa, hkn yasa ta fada jikinsa ta fashe da wani matsanancin kuka tana kiransa, ya runtse ido don har xuciyarsa yake jin kukan nata, a hnkli ya yakice ta jikinsa, ya rike kansa sun kusa minti uku a hka har lkcn bata bar kuka ba ya dago a hnkli yana kallonta ya bude baki da niyyan lallashinta amma ya nemi voice dinsa ya rasa gaba daya ga bakinsa yyi masa nauyi, gnin irin kukan da take yasa ya xamo kasa a hnkli gabanta yana kallonta, ba don musulinci bae yarje masa ba da ya rungume abarsa tsam jikinsa ya lallasheta, amma ba shi da daman yin hkan, da kyar yyi karfin halin nemo voice dinsa cikin raunanniyar murya yace "Am in pain Zainab, shi ya sa kika ga ina hawaye" mikewa ta yi da sauri a rikice xata fita tace "Bari in kira maka Dr yana dakin ya Saleem" dakatar da ita yyi ya riko hijab din jikinta cikin sanyin murya yace "No! I wil b OK idan na maida drip din, kar ki tashe su" ta juyo tana kallonsa, wani lallausan murmushin da ya kwantar mata da hnkli ya sakar mata yana kallon kwayar idonta, a sanyaye ta mayar masa snn ta dawo ta durkushe gabansa tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Toh ka tashi ka mayar da drip din sir," sunkuyar da kai yyi don wasu sabbin hawayen ya ji na shirin xubo masa, lkci daya ya mike ya koma kan gadon, ita ma ta mike ta xauna daga gefensa, a hnkli tace "In je in hado maka tea sir?" Girgixa mata kai kawae yyi cikin dakiya yace "Bacci nake ji" gyara masa pillon kan gadon tayi tana kallonsa ya kwanta a hnkli tare da lumshe idonsa, ta matso dab da shi cikin sanyin murya tace "Sir baka sa drip din ba kuma" ba tare da ya bude ido ba yace "Anjima xan sa, ki tafi kiyi kwanciyar ki" ta dan bata fuska tace "Sir ni nn xan tsaya in dinga duba ka plss, baxan iya tafiya in bar ka ba" kmr xata yi kuka ta kare maganar, ya girgixa mata kai cikin sanyin murya yace "Addinin mu bae yarje mana kwana waje daya ba Zainab, ni ba muharramin ki bne ki tafi kiyi kwanciyar ki I will b alryt in'sha Allah" hawaye ya cika rinannun idonta muryarta na rawa tace "Amma sir ae Allah ma ya san lalura ne, its nt intentional don Allah ka bar ni in tsaya da kai plss sir" hawaye na bin kuncinta ta karashe tana kallonsa, bude ido yyi a hnkli yana kallonta lkci daya ya mayar ya lumshe don wani tukuki xuciyarsa ke masa ba kadan ba, tagumi tayi gefensa idonta a kansa, sun kusa minti talatin a hka idonsa a rufe, a tunaninta bacci yyi, shi kam bbu abinda yake sae kukan xuci wanda ya gwammace da ma na idon yyi ko xae ji saukin abinda xuciyarsa ke masa, bae taba sanin hka ake ji a other side of love ba, so da yawa a kan kawo masu cases irin hka a clinic bae kuma taba ba irin cases din muhimmanci ba hasali ma haushin victims din yake ji sae ga shi shima yau yyi falling victims of such circumstance, yyi daya sanin sanin Zainab, yayi da ya sanin fara sonta without notice, bae taba soyayya ba sae a kanta, nd he can sew they are much prepared to break his heart, a hnkli ya ji ta daura kanta gefen pillon da yake kwance duk da hijab din da ke jikinta hkn bae hanasa jin 'dad'da'dan kamshin da gashinta ke yi ba, bayan yan mintoci ya ji saukar numfashinta a hnkli alamar ta yi bacci, cikin dubara ya xame kansa daga kan pillon ya mike xaune snn ya sauko kasa ynda baxae tada ta ba, ji yyi jiri na neman kada sa da ya mike tsaye, yyi saurin dafa bango yana kallon agogon dakin, Karfe uku ya dan gota, button din shirt din jikinsa da ke bude ya shiga buttoning cikin rashin kuzari, yana gama wa ya kwashi wayoyinsa da Atm ya nufi kofa yana hada hanya ya bude a hnkli snn ya fice daga dakin ya sauka falo, ba karamin daurewa ya dinga yi ba don jiri yake gani ssae har ya fito compound ya nufi gate ya bude ya fice daga gidan, yana gnin dishi dishi ya isa bakin titi, da ka gansa kasan kiris ya rage yyi collapse, ya dan jima tsaye bakin titi yana layi kmr wani mashayi kafin ya samu dan sahu, ya shiga ya rike kansa da ke neman rabewa, jin tambayar da dan sahun ke masa yasa ya dago da kyar yace "Airport xaka kai ni"
Chapter 54 · 0% Book details