Sashe 86
Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Dr Sharif bae samu courage din gaya ma iyayensa ynda suka yi da Abba ba don yasan da wuya su goyi bayansa, ko sanin xuwansa gidan ma ba su yi, shi dae baxae ce yana son Fadila ba sae dae tana burgesa sbda nutsuwarta da wayonta ga respect, ga kokari both ilimin addini da boko, sae dae bae jin yana da ra'ayi na aurenta, yasan sun gano abinda Afeefah tayi shi sa Abba ya kirasa ya kuma basa hkuri. Bayan sati biyu da xuwansa kiran Abba mahaifinsa Alhaji Shariff ya kira sa falonsa, ya dde xaune yana jiran jin abinda mahaifin nasa xae ce, kafin Alhaji Sharif na kallonsa yace "Ya ku ka yi da Alhaji Mahmoud, ina nufin sirkin ka a da, wato mahaifin tsohuwar matar ka" Shiru Dr yyi yana kallon dad din nasa, Alhaji Shariff yace "Kayi shiru Aliyu" shafa kansa yyi a sanyaye yace "Dama kirana yyi ya kuma ban hkuri kan abinda ya faru, yake kuma nuna xae ban kanwarta in yi shawara da ku in ji ta bakin ku, nasan kuma da wuya ku ban goyon baya shi sa na bar xancen kawae" Alhaji Shariff ya sauke ajiyar xuciya yace "Kai kana da ra'ayin koma masu knn, kuma it doesn't make sense in anyway ka saki yaya ka koma wa kanwa, sam ko kadan abun ba tsari, bae ma kamata ba, shi ma Alhaji Mahmoud din da yyi wani naxari kafin ya bullo da hkn" shiru Dr yyi don ya gano inda maganar mahaifin nasa ya dosa, kawae dae yana kame kame ne bae son fitowa fili, a hnkli yace "Ae Abba bbu abinda ya taba shiga tsakani na da ita na auratayya" Shiru dad dinsa yyi yana kallonsa fuskarsa dauke da mamaki, Dr Sharif ya ci gaba a sanyaye yace "Shine ma yasa ya bullo da hkn" Mahaifin nasa bae kuma cewa komae ba, bayan kusan minti biyar yace "Toh Allah shi kyauta, amma baka ji ddin ta ba sae kanwarta?" Dr Sharif ya sunkuyar da kai yace "yayansu take so, shi yasa ta ke min hka, ni kuma na sauwake mata don raba ta da xunuban da take kwasar ma kanta a kullum, kuma ga shi ynxu ta auri wanda take son" Alhaji Sharif yace "toh ban baka shawarar kuma koma masu ba Ali, ita kanwar Ca tayi tana son ka da har ake neman lika maka ita" a sanyaye yace "Yarinya ce Abba, baxata wuce 16 ba, koh secondary bata gama ba" Alhaji Sharif yace "Toh Allah bada sa'a, tashi ka je, sae dae duk abinda xa ka kuma fuskanta bbu ruwana, ban kuma yarje maka da saki ba, tun da kai ka ga xaka iya." Jikin Dr Sharif yyi sanyi ssae, sae dae bae kuma cewa komae ba.
🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
By Ashmaad
105....
A week ltr
🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
By Ashmaad
105....
A week ltr