← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 89

Sashe 57

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Karfe biyar saura na yamma Afeefah na daki kwance ta tsura ma Tv ido, tun bayan maganar da su jiddah suka mata daxu taki komawa dakin ya Aliyu, har abinci bbu ynda Mami bata yi da ita ta kai masa ba tace ita kanta na ciwo, duk da ma bacci yake tayi bayan fitarta don sae lkcn ya samu bacci. Fadila ce ta shigo dakin tace "Ya Ma'aruf ya xo" da sauri Afeefah ta mike tace "Da gske," bata rufe baki ba ya shigo dakin, murmushi tayi tace "lah Ya Ma'aruf" ya mayar mata murmushin yace "Kina ta bacci ko kasa" murmushi ta kuma yi tace "wllh ba bacci nake ba kallo nake, ya su Fadil" yace "su Fadil na gida, ya jikin yayanku" ta sunkuyar da kai tace "Da sauki," yace "na shiga yana ta bacci, bari in je in dawo" tace "Ina xa ka ya Ma'aruf?" Yace "Gidansu Dr Aliyu xan tafi, bashi da lfya" mikewa tayi sa sauri tace "Don Allah ya Ma'aruf mu je tare" kmr xata yi kuka ta kare maganan, yace "Ae Mami baxa ta yrda ba," hawaye cike idonta tace "Ka tambayar min ita plss yaya" ya dan yi shiru snn yace "To ina xuwa" ya fita daga dakin, Hijab dinta ta dauko da sauri tana Addu'ar Allah yasa Mami ta yrda, ba a dau lkci ba ya dawo yana kallonta yace "Mami bata yrda ba, idan naje I wil extend ur greetings kin ji" bata sauraresa ba ta fice daga dakin xata dakin Mami har hawaye ya cika idonta, yyi dariya yace "Ke wasa nake maki, ki je ki sallameta ina jiran ki a waje" dan murmushi tayi ta sa hijab dinta snn ta nufi dakin Mami, ta sameta ita kadae, ta durkusa gefenta tace "Mami xan raka ya Ma'aruf" Mami tace "Ya gaya min amma kada ku dde Zainab, ku yi masa sannu, Allah kara lfya" mikewa tayi tace "To Mami" snn ta fita daga dakin, Su Anty Safiya dake girki a kitchen tayi ma sallama, suka ce "Ina xa ki?" Tace "Ni da ya Ma'aruf xamu fita xan rakasa ya duba..." Hararan da suka watsa mata yasa ta yin shiru, Anty baby tace "Maxa ki je ku dawo ina neman ki, sha sha sha kawae wae bare ya fi dan uwanta" a sanyaye Afeefah ta juya ta fita daga kitchen din, horn ya Ma'aruf ya danna mata, ta nufi motar ya Aliyu, ta bude front seat ta xauna, ya ja motar suka bar gidan yana cewa "Shine kika shanya ni"murmushi kawae ta kirkira. Sae da suka hau main road snn ba tare da ya kalleta ba yace " Kinsan musabbabin ciwon Aliyu?" Ta dan yi shiru snn a hnkli tace "Yayanmu?" Ya girgixa mata kai yace "Yhur lecturer" da sauri ta girgixa masa kai tace "A'a" yana kallon titin gabansa yace "Sbda ke ne Zainab" dafe kirji tayi a dan tsorace tace "Ni kuma Ya Ma'aruf? Me nayi masa?" Yace "Baki yi masa komae ba, amma ana neman raba sa da ke ne" ta xaro ido tace "Kmr ya yaya?" Yana tukin sa a nutse yace "Dad ke son hada ki da yayanku Aliyu, shine ya kirasa yake gaya masa wae ya hakura da ke, sae a basa sistern ki," kasa cewa komae tayi sae hawayen dake bin kuncinta, Ma'aruf ya dan tabe baki yace "Ke ynxu kina son yayanku?" Girgixa kai tayi cike da takaici tana hawaye ssae tace "Wllh bana sonsa, bana sonsa kuma ni baxan yrda da aurensa ba, shi din a matsayin yayana na daukesa, idan ma aka tilasta ni wllh sae in gudu kawae" Ma'aruf yyi murmushi yace "Ae ba sae kin gudu ba Zainab, fitowa xakiyi kice baki sonsa ke ga wanda kike so," ta fashe da matsanancin kuka tace "Sau nawa zan gaya hkn, sun ki fahimta ta, Wllh bna son yayanmu ni baxan iya aurensa ba" lallashinta Ma'aruf ya shiga yi yace "Ba sae kinyi kuka ba Zainab, stop those tearz, just be bold idan aka tunkare ki da maganan Aliyu kice ke baki sonsa period" shiru tayi bata kuma cewa komae ba, hkn yasa yace "Dr Aliyu abokina ne ssae, na kut da kut kuwa, kuma tunda muke da shi a iya sanina bae taba soyayya ba, infact baya ma kula mata, sae a kanki ya fara Zainab, don't break his heart plss kada ki bari a canxa maki ra'ayin ki, idan kika samu Dr Aliyu a matsayin mijin ki ina assuring dinki kin gama samun komae a rayuwar ki, coz bbu abinda ya rasa tun daga ilimin addini har xuwa na xamani, ga dukiya nasa na kansa" Afeefah ta jinginar da kanta jikin kujeran da take tana hawaye ssae, bae kuma ce mata komae ba har suka iso gidansu Dr Sharif.

Eeshatullah
[6/29, 06:20] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad
Chapter 57 · 0% Book details