← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 89

Sashe 72

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki gaya min?" Tace "Ka kirani in gaya maka plss" "Hm" ya mayar mata kafin ya sauka, ta xuba ido ta ga kiransa amma shiru, tafi minti talatin tana jira amma shiru still, kmr xata yi kuka ta kuma logging ta tura masa emoticon na fushi, taga ya ma kashe data, kuka ta saki kmr karamar yarinya kafin ta tura wayar daga kusa da ita. Washegari Sunday ta tada fitinan ta ita gida xa ta, ya share ta bae tanka ta ba, daga karshe bangarensa ya koma ya bar ma ta falon, ta bi bayansa tana hawaye, a falonsa ya kwanta yana ganinta yace "Yhu are disturbing me Zainab, let me rest plss" cikin kuka tace "To ni nace maka xan je gidanmu" mikewa yyi ya bar mata falon ya shige bedroom, ta bi sa da sauri, bude baki yyi yana kallonta, ta rungume hannayenta tana kuka, murmushi yyi ya jawo study desk dinsa ya dauki medicated dinsa ya sa kafin ya dauki wani babban text buk yasa gaba yana dubawa. Ta fi minti ashirin a tsaye har sannan a dakin, ya mike kmr xae dauki abu a gaban mirror ya fixgota, ta xaro ido tace "Don Allah kayi hkuri xan tafi wllh" bakinsa ya hade da nata, da kyar ta samu ta kwace kanta ta fice da gudu. Da yamma kmr wasa tace bari tayi tryn kiran Aliyu da nmbrsa ta UK da sabon sim dinta don a shi kadae take da airtym, ga mmkin ta taji ya shiga, ta xaro ido ta mike xaune gabanta na faduwa, ya dan dau lkci kafin ya daga, cikin sanyayyan muryarsa yyi sallama, amma ta kasa amsawa tsabar murnar jin muryarsa kuma tana tsoron kadda ya katse idan yaji ita ce, yace "Hello" nn ma ta ki cewa komae ya dan yi jim kafin ya katse wani tsalle ta doka cike da jin ddi dae dae nn Dr Sharif ya shigo dakin ya kalleta gnin mood dinta yace "Duniyar ta maki ddi knn koh?" Turo baki tayi bata ce komae ba, yace "ki shirya sae ina kai ki gidan amma baxa ki dde ba" mikewa tayi tace "Toh" wasu kayan ta fiddo ta nufi bayi ya bi ta da kallo har ta shiga ta sa key, murmushi yyi ya juya ya fita daga dakin. Grocery suka fara biyawa ya siya fruits da za su kai can gidan kafin su kama hanyar gidan, Karfe biyar suka shigo falonsu ya xauna kan kujera ta haura sama don bbu kowa falon, dakin Mami ta shiga, ta sameta ita da su jiddah ta rungume ta cike da jin ddin ganinta, Mami tace "Daga ina kike?" Tace "Shi ya kawo ni Mami yana falo" Mami tace "Sannun ku da xuwa" tace "Mami yayanmu fa?" Mami ta mike tace "waye kuma yayanku?" Kmr xata yi tace "Ya Aliyu mana" hararanta Mami tayi ta dauki hijab tace "Baki lura da shi a bayana ba knn" tana kai wa nn ta fice don xuwa su gaisawa da sirkin nata, Afeefah tuni har hawaye ya cika idonta tana kallonsu jiddah tace "Anty jiddah kuna waya da shi?" Jiddah ta girgixa kai tace "A'a amma yana UK, kuma muna chat da shi" jin hka ta warce wayar jiddah da sauri ta fice daga dakin ta shige nasu tuni jiddah ta mike tana cewa ta bata wayarta, Afeefah ta sa key a dakin kafin ta bude wayar ta hau whtspp da sauri, chat din ta shiga dubawa tun daga farko, ssae ta ga yake chat da 'yar uwar tasa kusan kullum, ga mamakinta sae ta ga kusan kullum din sae ya tambayi Jiddah ko sun hadu da ita a sch, jiddah tace suna haduwa kuma ko da yaushe tana tambayarsa, murmushi ya tura mata yace tana masa text ko da yaushe amma bae fiye mata reply ba yana daurewa yyi ignoring dinta, tambayarsa jiddah tayi "Sbda me" ya mayar mata yace "Sbda tana fama min ciwon da yaki warkewa a xuciyata, I just can't bear it sister, i alone knws wat am going through ynxu, all d same ina jin ddi idan na ga text dinta, it soothe me, jiddah ta tura masa fuskar tausayi tace "Kawae kayi blockn dinta yayanmu xae fi" yace "Koh?" Ta mayar masa tace "Allah kuwa" yace "OK I will giv dat a try" jikin Afeefah yyi sanyi ssae, lkci daya hawaye ya cika idonta, A chat din su na jiya ne taga Jiddah na tambayarsa lkcn da xae dawo don Allah, ya mayar Mata yace "Xan dawo amma sae nn da shekaru bakwae idan Allah ya yrda, kafin nn No pain, no scar a xuciyata, yea duk sun goge in'sha Allah, but tsakanina da ke ne wnn kar ki gaya ma ko Mami" Jiddah ta tura masa emotion na rashin jin ddi tace "Kayi hkuri yayanmu, kar kace har seven years Plss, just forget ur pass nd face future plss ka kaddara dama Zainab ba matar ka bace a rubuce, Allah xae maka musanyar alkhairi, kila ma ita din ba alkhairi bace gare ka shi sa Allah bae baka ba, Allah xae baka Wacce ta fita, plss yayanmu ka dawo gida, its high time kai ma kayi auren ka ynxu kayi settle down, Zainab ta xama past tense gare ka tunda tana xaune gidan mijinta lfya ynxu" ya mayar mata yace "tnx sister, sae ki xaba min matar da kika ga ta dace da ni, I wil accept don ban san ta inda xan fara neman mata ba ynxu" wurgi da wayar Afeefah tayi kan gado ta dinga rusa kukan bakin ciki, bnda bubbuga kofa bbu abinda yayyin nata suke suna kiranta amma ta ki budewa sae kara sautin kukan ta da tayi, muryar Mami da taji ita ma tana kiranta yasa ta mikewa tana kuka ssae ta bude kofar, Mami tace "Lfya me ya same ki?" Rungume Maminta tayi tana kuka ssae tace "Mami kina ganin Anty jiddah take ce ma yayanmu a chat ni ba alkhairi bace gare sa shi sa bae aure ni ba, wae ya manta da ni yayi blocking dina, kuma yyi aurensa kawae" muryarta na rawa ta kare maganar cikin kuka ssae, daga sadiya har Mami suka juya suna kallon jiddah da hanjin cikinta ya kada, Mami tace "Toh sae me, sa ji da munafurcinsu daga ita har shi," wani mugun kallo Mami ta shiga yi ma Jiddah tace "Algunguma kawae munafuka, dole ku nuna mata ba ubanku daya ba, nasan akwae rana irin ta yau da xae xo" daga hka ta ja hannun Zainab suka fice daga dakin tana kuka, ta nufi dakinta da ita ta shiga lallashinta, da kyar ta hadiye kukan, Mami ta Mike ta fita daga dakin bayan ta tabbatar tayi shiru, kwanciya tayi kan gadon Mami tana sauke ajiyar xuciya. Bayan isha Dr Sharif ya dawo tafiya da ita, tana xaune dakin Mami bayan ta dan cakalkala tuwon gabanta Mami ta shigo tace "Tunda baxa ki ci ba tashi ki wanke hannun ki ku tafi mijin ki ya dawo" bata fuska tayi tace "Ni a nn xan kwana Mami" wani kallo Mami ta watsa mata tace "Kin tashi ko sae nayi kwallo da ke, ki kwana ki min me" mikewa tayi hawaye cike idonta ta shiga bayi ta wanke hannu ta fito, Mami tace "Ki tafi ki sallami Abban ku, sae ki deban maku abinci a kitchen" wayarta da jaka da hijab ta dauka fuu ta fice daga dakin ta nufi falon Abba, xaune ta samesa da Dr Sharif, ta sallame Abban suka fito tare da Dr Sharif din, sae da suka sakko downstairs snn fuskarta daure tace "wae xaka ci abinci" girgixa mata kai kawae yyi suka fita daga falon. Tara saura suka isa gida bayan ya biya ya siya gasassun kaji da fura, yana gama parkin ya juya yana kallon jajayen idonta yace "Kukan me kike?" Kmr jira take ta fashe da wani kukan tace "kaga sir ko ba Anty jiddah bace take ce ma yayanmu ta whtspp wae ni ba alkhairi bace gare sa shi sa bae aure ni ba, kuma ya manta da ni, yyi blocking dina a whtspp" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, tabe baki yyi ya kashe motarsa ya xare key kafin ya bude mota ya fice ya nufi cikin gida rike da ledarsa, sae da ta kuma cin kukanta a motar kafin ta fita ta rufe ita ma ta nufi cikin gidan, falo ta samesa xaune ya xuba kajinsa a plate yana ci yana kallon news, fuuu ta haura sama kmr xata tashi sama, yyi yar dariya ya dauki drink dinsa ya sha. Tana shiga dakinta wayarta ta fiddo ta bude whtspp, voice note ta shiga yi ma ya Aliyu kmr hka tana kuka, "yayanmu Shine Anty Jiddah xata ce maka ni ba alkhairi bace gare ka ka yrda ko, har da wani cewa kayi blocking dina a whtspp ka mance dani koh, dole dama wataran xa ku nuna min ba ubanmu daya da ku ba, kuma yau yau kayi blockin dina kuma bana kara maka magana in ma baka yi ba ni xan yi blocking din ka wllh" tura masa tayi ta jefa wayar ta fada kan gadon tana ci gaba da kuka, gajiya tayi da kukan ta mike ta nufi bayi daga karshe tayi wanka ta fito ta canxa kaya xuwa nighty ta kwanta tayi jigum, sae kuma taji cikinta na kugi, mikewa xaune tayi tana kallon agogo taga sha daya ya wuce har da rabi, ta mike ta dauki hijab dinta ta sa ta fita daga dakin ta sauka downstairs, kwance ta samesa falo ya kure Ac, yana kallon wani American movie with interest, ta karaso falon tana kallon plate din da ya xuba kaza ta ga dan kadan ya rage naman, kallonsa tayi tace "Sir ina nawa yake?" Ya juya ya dan kalleta kafin ya ci gaba da kallonsa yace "Ban san xa ki ci ba na ba masu gadi" ta xaro ido tace "Furan fa?" Yace "Har shi, but ga wanda na rage can" hade rae tayi tana kallonsa kmr xata yi kuka, ya shafa kai idonsa na kanta yace "Gasu can ki dauka" juyawa tayi a fusace ta nufi stairs ya maida dubansa ga kallon da yake, kwantawa tayi amma bacci ya
Chapter 72 · 0% Book details