← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 89

Sashe 56

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari Afeefah ta ji duk damuwarta ya dauke ganinta a kano, taxi ta samu ya kai ta har gida ta basa kudinsa snn ta fito tayi cikin gidansu da sauri bayan ta gaida mai gadinsu, Anty Safiya da Anty baby ta samu falo ko wannensu bbu wani annuri a fuska, Jiddah na kitchen tana wanke wanke, da gudu ta fada kan yayyin nata a dan sanyaye ta gaishesu, suka amsa suna tambayarta hanya da murmushin su, tace "Lfya lau, ina Mami fa?" Anty baby tace "Mami na sama, ya su dad da mum na Kaduna" tace "Suna lfya, wae in gaisheku" Jiddah ce ta fito daga kitchen tana kallonta, karasawa kusa da ita Afeefah tayi tana kallon idonta ganin ynda yyi ja alamar tayi kuka, da damuwa tace "Me ya faru Anty jiddah" Jiddah ta girgixa mata kai tace "Bbu komae, ya hanya" a sanyaye Afeefah tace lfya, snn ta nufi sama, dakin Mami ta shiga ta samu bata nn, ta fito ta shiga nasu dakin, Sadiya ce xaune da ganinta kasan tana cikin damuwa, Sadiya ta dan kirkiri murmushi tace "Zainab" Afeefah ta karaso da sauri da damuwa fuskarta tace "Anty sadiya me ya faru?" Sadiya tace "Bbu komae, yaushe kika iso" bata 6ata amsa ba tace "Mami fa" Sadiya tace "bata dakinta?" Mikewa Afeefah tayi da sauri ta fita, Adnaan ne ya fito daga dakin Aliyu, kallo daya yyi mata ya kara gaba abun sa, jikinta yyi sanyi ssae, dakin Aliyun ta nufa ta tura a hnkli, kwance ta gansa cikin bargo ya rufe har kansa, Mami na edge din bed din xaune rike da cup din tea alamar fiffitawa take, Mami ta dan mata murmushi tace "Har kin iso, ya hanya" murmushin ta mayar mata amma a sanyaye snn ta karaso cikin dakin ta gaisheta tana kallon Aliyu tace "Mami ashe yayanmu ya dawo, bacci yake ne?" Mami bata 6ata amsa ba, ta hau kan gadon ta xauna kusa da shi ta yaye bargon jikinsa tana kallonsa, ba karamin tashi hnklinta yyi ba jin temperature dinsa, da damuwa tace "Mami bashi da lfya ne kuma?" Ba tare da Mami ta kalleta ba tace "Ehh, kar ki tashe sa" hawaye ne ya cika idonta ta daura hannunta a goshinsa a hnkli tana kallon kyakkyawan fuskarsa da yyi haske ba kadan ba lebbansa yyi ja ssae, lkci daya ya bude rinannun idanunsa jin hannu a goshinsa ya daura kan nata, ganinta yasa ya mike xaune da sauri yace "Zainab" shigewa jikinsa tayi hawayen idonta ya gangaro a hnkli tace "Har ynxu baka da lfya ne yayanmu?" Girgixa mata kai yyi ya rungumeta ssae, ya runtse ido cikin sanyin murya yace "Na fara jin sauki little sis, flight kika bi?" muryarta na rawa tace "To ni na ji jikin ka da xafi ssae ae" a hnkli yace "Na sha magani ne" bata kuma cewa komae ba tayi lamo jikinsa tana jin irin ynda xuciyarsa ke bugawa kmr xae fito, duk wnn abinda suke Mami bata kalli inda suke ba sae fiffita tean hannunta take a hnkli, can ta ajiye cup din tea'n ta mike ta fita daga dakin. Daga kai Afeefah tayi tana kallonsa ta ga idonsa a lumshe, lkci daya ya budesu yana kallonta shi ma ya sakar mata murmushi, da damuwa tace "Yayanmu ina ke maka ciwo?" Kirjinsa ya nuna mata kawae, ta xame jikinta daga nasa ta sakko daga kan gadon ta dauki cup din tean da Mami ta ajiye ta dawo gabansa tace "Ga shi yayanmu ka sha, sae Ka kara shan magani koh" ba musu ya karba ya kai baki ya shiga sha a hnkli, tayi tagumi gefensa tana kallonsa har ya sha fiye da rabi snn ta karbi cup din tace "Ka koshi yayanmu" kai ya gyada mata yana goge bakinsa, ta shanye sauran snn ta ajiye cup din tace "Kayi wanka yayanmu?" Girgixa mata kai yyi, ta mike tace "Bari in hada ma ruwa" bin ta yyi da kallo har ta shige bathroom, bayan 'yan mintuna ta dawo tace "Na hada maka ruwan yayanmu" mikewa yyi ya sakko daga kan gadon a hnkli snn ya cire rigan sanyin jikinsa tana kallonsa ta ga ya rame ba kadan ba, milk jallabiyan jikinsa ya cire ya rage masa singlet da 3 qtre ya nufi bathroom kmr me counting steps dinsa don tun jiya bae iya tashi, sae gashi ynxu ko jirin bae gani ba, cups da plates din dake dakin sae cans din malt da robobin drip duk ta kwashe ta fita daga dakin ta sauka kasa, har lkcn yayyinta na xaune falo, duk suka bi ta da kallo ta shiga kitchen ta ajiye cups da plates, cans din malt kuma ta xubar cikin shara snn ta dawo falo, Anty Safiya ta kalleta tace "Ya tashi ne?" Afeefah tace "Ehh ya tashi" Anty baby tace "Ke kika shanye tea'n cup din" girgixa Kai tayi tace "A'a shi ya sha ya rage kadan" shiru suka yi duk suna kallonta, ta juya ta koma sama, bedroom din ta shiga gyarawa ta canxa bedsheet snn ta sauka kasa ta dauki sweeper ta koma ta share dakin tayi tidyn din shi duk da fez dakin yake, tana kkrin kunna burner ne Mami ta shigo dakin, gadon ta kalla kafin tace "Ina Aliyun?" Afeefah tace "Wanka yake yi" shiru Mami tayi ta kasa cewa komae, can tace "Tea'n fa?" Afeefah ta ce "Ya sha na kai cup din kitchen" da mmki Mami tace "Ya sha da gske?" Afeefah ta gyada kai, Mami bata kuma cewa komae ba ta juya a sanyaye ta bar dakin, Anty baby da Safiya ne suka shigo dakin su ma, Anty baby ta kalli kan gadon tace "A'ah Ina yayan namu" Afeefah tace "wanka yake yi" Anty baby tace "Da gske?" Kai kawae Afeefah ta gyada mata, Anty Safiya tayi murmushi ta juya ta bar dakin, hka ma Anty baby, kananan kaya Afeefah ta fito masa da ta ajiye gefen gado, dai dai nn ya fito ta juya tana kallonsa tace "Yayanmu kayan nn yyi maka" Shiru yyi ya kasa bata amsa tuna da da yyi, kusan kullum ita ke fito masa da kayan da xae sa tun tana k'an k'anuwarta, Karasowa gabansa tayi tana kallonsa a hnkli tace "Yayanmu!" Firgit ya dawo da sauri yace "Yyi mana little sis" tace "To ka sa kayan bari in wanke bathroom" bin ta da kallo yyi har ta shiga bathroom din duk da ita ma jikinta yyi sanyi, Aliyu ya isa bakin gado da kyar ya xauna ya rike kai sae ga hawaye, me yyi ma Mami xata yanke masa danyen hukuncin nn hka, don me baxata yi la'akari da ynda ya rainan mata Zainab ba har ta kai matsayin da take ynxu, tun Zainab na cikin tsumma yake wahala da ita har goyonta ya sha yi, ta kuma yi bacci a bayansa, tun tana karamarta bbu wanda take yrda da a gidan bayan Mamin sae shi, komae shi ke mata, ya kuma fi fiffita ta kan wa enda suke uba daya, kwata kwata bae san laifinta a gidan har yau har gobe, me yyi ma Mami da xata yi masa hka, tamkar uwar da ta haifesa a cikinta ya dauketa, hawaye ssae yake, gnin numfashinsa na yin sama kmr jiya yasa ya saita kansa, ya kusa minti goma kafin ya dan dawo nml ya tashi da kyar ya saka kayansa snn yyi kwanciyarsa kan gado ya lumshe ido.

Afeefah na gama wanke bayin ta fito tana kallonsa, gnin idonsa a lumshe tayi tunanin ko bacci yake ta fita daga dakin, dakinsu ta nufa lkci daya Dr Sharif ya fado mata, duk sae taji damuwar ta ya dawo, tana jan kafa ta shiga dakinsu, ta samu Jiddah da Sadiya xaune dakin, gefen gado ta xauna tace "Su fadila fa?" Jiddah tace "Sun tafi sch" Afeefah tace "Abbana fa?" Sadiya tace "Daxu ya tafi abuja" kwanciya tayi ta juya masu baya, Sadiya ta dawo kusa da ita tana kallonta a hnkli tace "Afeefah" mikewa Afeefah tayi tana kallonta, Sadiya ta kwantar da murya tace "sbda me kika ce baki son yayanmu" kallonsu Afeefah ta tsaya yi lkci daya mood dinta ya canxa, a sanyaye Jiddah tace "Baki masa hallaci ba Afeefah, duk irin son da yake maki ki rufe ido kice baki son sa" mikewa tayi hawaye cike idonta tana kallonsu tace "Kmr ynda bbu xancen aure tsakanin ku da shi, to nima bbu, don a matsayin Yayan da muka fito ciki daya na daukesa, don hka ku kyaleni" tana kai wa nn ta fice daga dakin hawaye na bin kuncinta, dakin Mami ta shiga ta sameta xaune tana waya, ta fada kan gadonta ta shiga rera kuka a hnkli, Mami ta kammala wayar ta juya tana kallonta da mmki tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Ko ba su Anty jiddah bne suke min magana wae me yasa nace bna son yayanmu, ni kice masu su daina min irin maganan nn bna so, don matsayin yayana na daukesa kuma ni ba aure tsakaninmu" Mami bata ce komae ba sae danna wayarta kawae take amma da ganinta kasan jikinta yyi sanyi, mikewa tayi ba tare da ta tanka ta ba ta fita daga dakin, Afeefah ta ci kukanta daga karshe bacci ya dauketa.
Chapter 56 · 0% Book details