← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 89

Sashe 68

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da irin yunwar da take ji, daga karshe fridge dinta ta bude ta dauki hollandia drink ta sha, Karfe goma ta yi wanka ta shirya ta kwanta, sae dae har sha biyu k'asa bacci tayi ga wani mugun ciwo da kanta ke mata, a hnkli ta mike ta dauko wayar dake gaban madubi ta dawo gefen gadon ta xauna ta shiga trying line din ya Aliyu har Karfe daya tana abu daya amma switch off, ta fada kan gado ta dinga rusa kukanta na tsiya, a hka bacci barawo ya sace ta. Washegari kusan da xaxxabi ta tashi, hka ta daure ta yi shirin makaranta don takwas da rabi take da lecture, tana jin fitar motarsa ta mike da kyar ta fita daga dakin sanye da hijab tana rike da jakar makarantar ta sakko falon, tsaye tayi tana kallon plate din d'anwaken jiya dake tsakar falon har lkcn, a sanyaye ta karasa falon ta duka ta dauke plate din ta nufi kitchen ta bude kofar kitchen din ta xubar cikin waste bin snn ta rufe kofar ta wanke plate din ta fita daga kitchen din. Drivern dake xaune da mai gadi yana ganinta ya mike ya tafi fito da mota dafa garage. Suna xaune da Maryam a cafeteria bayan sunyi azahar kafin su shiga lecture, hira kawae Maryam ke mata amma gaba daya hnklinta baya kan hirar tayi xurfi a tunanin da take, jin Maryam tace Xata sa rana ta xo gnin gida ya sa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, tayi mata murmushi tace "Toh ina xuba ido sae kin xo" daga hka Maryam tace su tafi aji, suka mike suka fita daga cafeterian, tunani ta shiga yi ko dae ta tafi gida tun da yau kusan watan ta daya da aure, ta kalli agogo ta taga biyu ya kusa, yanke shawarar tafiya gidan kawae tayi ta kalli Maryam tace "kin ga Maryam ni fa gida xan tafi kawae, sae mun hadu gobe sae ki ban handout" da xolaya Maryam tace "Xa ki je ki yi ma sir girki knn" murmushi kawae Afeefah tayi ta mata sallama ta nufi gate da sauri. Cike da murnar ganinta kofar gidansu ta sauka daga adai daita ta basa kudinsa ta shige gida da sauri, bbu kowa falonsu ta haura sama, dakin ya Aliyu ta fara budewa da saurinta ta shiga, sae dae bbu kowa falon kuma bata ga alamar ana amfani da dakin ba don ya dan yi kura, hawaye ne ya cika idonta ta fito a sanyaye, dai dai lkcn da Mami ta fito daga dakinta, da mmki ta tsaya kallonta tace "Zainab? Daga ina hka?" Afeefah ta karasawa da sauri ta rungume uwar tata, Mami tace "Ikon Allah, daga ina kike?" Tace "Daga makaranta" Mami tace "Shi yace ki xo?" Turo baki tayi tace "Nayi kewarku ne Mami shi sa na xo, yayanmu fa?" Mami ta hade rae tace "Ban san baki da hnkli ba sae yau Zainab, to maxa juya ki bar min gidana sha sha sha kawae a ina aka taba hka" shiru tayi jiki a sanyaye tana kallon Mami, lkci daya hawaye ya taru idonta tace "Ae ba dde wa xanyi ba Mami, yayanmu fa?" Mami tace "Ki bar min gida Zainab tun ban bata maki rae ba" hawaye ya shiga bin kuncinta tace "To Mami xan tafi, amma yayanmu fa?" Mami tace "Ban sani ba ki kama hanyar gidanki" kuka ssae take tace "Don Allah ki gaya min Mami Allah xan tafi ynxu, ni shi na xo gani wllh" Mami tace "Baya nn to" a sanyaye tace "Ina ya tafi Mami, me sa layinsa basa shiga idan na kirasa" Mami tace "Me xae maki kike kiransa," tace "Ina son in ji muryarsa Mami nayi missing dinsa, idan ya canxa layi ne ki ban plss" Mami da ta dan fara shan jinin jikinta tace "Ke ban fa son shashanci baya Nigeria kiyi tafiyar ki gida, idan ya dawo ae xae je ya gan ki" kuka ssae ta dinga yi tana girgixa ma Mami Kai tace "Mami ina yace xe tafi, kuma yaushe xae dawo" wani tsawan da ya raxanata Mami ta daka mata tace "Fice min a gida kada ki ja ma kanki duka Zainab" tana kuka ta juya da sauri ta sauka ta fita falon. Karfe uku ya wuce ta shigo gida, ko kallon drivern ta da ke tambayar ta ya bata kira sa ba bata yi ba don wani duhu duhu take gani ga kanta dake neman rabewa biyu, last strength dinta tayi amfani da ta shiga falon kafin duhu ya mamayeta ta xube nn bakin kofar falon a sume, Dr Sharif dake kwance falo yana kallon wani American Movie ya mike da sauri ya karasa bakin kofar, durkusawa yyi gabanta ya dago ta a sume, mikewa yyi da sauri ya dauketa ya nufi sama da ita ya shiga part dinsa, kan gado ya kwantar da ita ya shiga bata taimakon da ya kamata. Can Karfe takwas na dare yana xaune kan darduma ya idar da isha ya ga tana juye juye har ya mike xae karasa kusa da ita jin sunan wanda take kira yasa ya koma yyi xamansa, ta kira yayanmu ya yi sau uku kafin ta xabura ta mike xaune, tana bin ko ina na dakin da kallo, gninsa yasa gabanta ya fadi, a hnkli ta xamo daga kan gadon ta nufi kofa da sauri, bin ta yyi da kallo har ta fita. Dakinta ta shiga ta kwanta kan gadonta tana jin ciwon kae ssae, har bacci ya soma daukarta misalin Karfe tara da rabi ya shigo dakin rike da cup din tea, gefen gadon ya xauna yana kallonta yace "Tashi ki sha tea sae in baki magani" a hnkli ta mike xaune ta karbi cup din ta kai bakinta don dama yunwa take ji, goshinta yyi feel ya ji xafi hka ma jikinta yace "Ina ke maki ciwo" kanta ta nuna masa ya mike ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo dauke da allura da magani, yana nn xaune ta gama shan tean ta mike yace "Ina xa ki" da kyar tace "Ina son inyi wanka" yace "OK" hijab ta dauka ta shiga bayin, ko da ta fito ya kunna tv yana kallonsa, yyi mata kallo daya ya dauke kai, ta nufi gaban madubi ta dauki mayyukan ta da turare snn ta bude wardrobe ta fiddo rigarta na bacci me dan kauri har kasa kafin ta koma bayin, bin ta da kallo yake har ta shiga ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, ta kusa minti sha biyar kafin ta fito, tana tafiya a hnkli ta koma can edge din gadon ta xauna, juyawa yyi yana kallonta cikin gatse yace "Sannu!" Turo baki tayi ta dauke kai, ya mike ya koma inda take ya ajiye mata magungunan ya gaya mata ynda xata sha, kai kawae ta gyada masa, yace "Are yhu ready for the injections?" Xaro ido tayi tace "Wae ni xa ka ma alluran sir?" Girgixa mata kai yyi yace "A'a kai na xan yi ma wae da" murmushi tayi ta dauke kai, can kuma kmr xata yi kuka tace "Plss sir ni dae maganin ya ishe ni ka mai da alluran" wani kallo ya mata kafin yace "in xubar knn xaki ce" shiru tayi bata kuma cewa komae ba, can tace "To a hannu xaka min?" Murmushi yyi yace "Aa gwiwa xan maki" xaro ido tayi, sae kuma ta fara dariya, yace "Xan tafi in kwanta answer me" hannun ta mika masa, ya harareta yace "C'mon" kmr xata yi kuka tace "To wae a ina xaka min sir" yace "Xo in nuna maki" make kafada tayi tace "A'a ni ka min a hannu ae ana yi" bata ankara ba ya fixgota ya d'aga doguwar rigar jikinta, kuka ta saki tana turasa ya danne ta, gnin har jikinta ya soma rawa yasa ya saketa yana dariya yace "Wae alluran kike ma kuka ko ni?" Gnin gudu take son yi yasa ya kama hannunta ya kwantar da murya yace "A hnkli fa xan maki wllh" ta girgixa kai tace "xafi xae min" yace "No baxae miki ba wife" yana fadin hka ya jawo ta jikinsa, hawaye ta shiga yi tana kallonsa, ya kwantar da ita, da sauri ta mike tace "Sir kayana dogo ne to ae" yace "Eh hka xan d'aga" xaro ido tayi tace "Don ka gan ni?" Mikewa tayi ta dauki xaninta ta koma bayi ta daura bayan ta dage nyt gown din, ta fito ta karaso kusa da gadon ta kwanta, murmushi yyi, yyi k'asa da xanin kafin yyi mata alluran, yana gamawa ya dagota ya rungumota jikinsa yace "Ya maki xafin?" Hade rae tayi kafin ta girgixa masa kai, ya ja kumatunta inda beauty point dinta yake yace "Idan kika yi hka da fuskar ki ba kya kyau" xata yi magana ya hade bakinsa da nata, a yau kam bae yi niyar sarara mata ba duk koke kokenta sae dae jin wanda ta dage tana kira masa iya karfinta ya sa shi turata har sae da ta fado d'aga kan gadon, ya bi ta yana mata wani mugun kallo da rinannun idanunsa, ta fara ja da baya gabanta na faduwa fixgota yyi cikin tsawa yace "me nace maki Zainab" toshe bakinta tayi jikinta na rawa, ya kuma yi mata wani tsawan, ta fashe da kuka a tsorace.
Chapter 68 · 0% Book details