← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 89

Sashe 63

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Har aka yi Azahar bata tashi ba, sae wajen biyu da wani abu ta farka tayi saurin mikewa ganin lkcn sllh ya wuce, har ta nufi bayi xata yi alwala ta tuna bata sllh, ta koma ta xauna, ta dde xaune jin yunwa ya addabeta yasa ta kalli agogo taga uku, mikewa tayi jiki ba kwari ta nufi kofa ta bude ta fita, a hnkli ta dinga sakkowa stairs har ta shigo falo ta gansa kwance yana kallon rike da remote, suna hada ido taji da ma bata sakko ba, ya dauke kai ya ci gaba da kallonsa, juyawa tayi ta koma sama da sauri ta shige dakinta. Ya mike ya bi bayanta, tsaye yyi bakin kofarta ya rungume hannu yace "Kin bude dakin knn," jin bata ce komae ba yasa ya karasa cikin dakin ya xauna gefenta yace "Na rasa gane kan ki Zainab, sbda ni kike saka key a kofa, wats d meaning of dat, OK I get yhu are telling me ina damunki koh," bata dago ba bare ya sa ran samun amsa, ya dago kanta cikin sanyin murya yace "Plss ki sake da ni Zainab, da xa ki shiga xuciyata ki ga ynda nake son ki da kin ji tausayi na, ke ba yarinya bace kinsan meye aure don hka ki daina behaving kmr baki sani ba, ina son ki min alfarma biyu Zainab" sae a snn ta dago kai tana kallonsa, yyi kasa da murya yace "Ki so ni kmr ynda nake son ki ko ba dukka ba, snn plss ki daina guduna ki sake jiki da ni" Jin bata ce komae ba yasa ya mike ya dago ta yace "Xo mu je kiyi lunch" bin bayansa tayi yana rike da hannunta suka sauka downstairs, ya xuba mata abincin da teemah ta kawo na lunch, rice da stew sae nama ya xuba mata ya ajiye mata gabanta yana kallonta, spoon din abincin ta dauka ba tare da ta kallesa ba ta shiga juya shinkafar gabanta. Komawa yyi ya kwanta kan kujera ganin sae tsakuran abincin take duk don yana gabanta, sae a snn ta dan ci, wanda ta rage kuma ta kai kitchen, da yamma misalin Biyar Anty Amina da Ma'aruf suka xo gidan, da kyar ta sakko kasa don kin sakkowa tayi da, bnda tsokanarta bbu abinda Ma'aruf yake Anty Amina na tare mata, shi dae Dr kallonsa kawae yake sae dae yyi murmushi, sae da Ma'aruf ya rabu da ita snn tace "Ya Ma'aruf yayanmu ya dawo?" Ma'aruf yace "Kila, amma ni bn sani ba" ta bata fuska kmr xata yi kuka tace "Toh dan kira min shi plss, ka ga wayata bn xo da ita ba" Ma'aruf yace "Bni da nmbrsa" da sauri tace "Ina da su off head bari in kira maka" harara ya maka mata yace "Kina matar wani xaki kira wani can" shiru tayi tana kallonsa sae kuma ta fara hawaye tace "Yayanmu fa nace maka kke ce masa wani" Ma'aruf yace "Shi din" murmushi Dr Sharif yyi gnin hawayen da take yace "Kar ki damu xan kira maki shi anjima" sae a snn ta shiga share hawayenta tace "Toh" Karfe shiddah Ma'aruf yace xa su tafi, gobe kuma xa su koma kd, Dr Sharif yyi masu gdya, Amina ta mike tace "Mu je mu yi bankwana Anty amarya" Tana fadin hka ta Kama hannun Afeefah suka nufi sama xuwa dakinta, gefen gado ta xaunar da ita tace "Na fahimce kina period ko Kanwata?" Shiru Afeefah tayi bata ce komae ga wani nauyin tambayar da ta ji, Amina bata damu da hkn ba tace "yaushe xa ki gama" still Afeefah bata ce komae ba, Amina tayi murmushi tace "Kar ki ji kunya ta fa, ni na dauke ki tamkar kanwata ne, ki gaya min yaushe xa ki gama" da kyar Afeefah ta bude baki ba tare da ta kalleta ba tace "Gobe" Amina tace "OK" snn ta bude handbag dinta ta fiddo wani bakar leda dan babba ta mika mata tace "Kinga wnn da madara xaki hada a cup ki shanye kin ji," Afeefah dae bata ce komae ba, ta kuma fiddo wani ta bata tace "Kina da Zuma ae" nn ma Afeefah shiru ta mata, ta mika mata tace "Shi wnn da xuba xaki hada ki sha" wani turaren miski ta kuma fiddowa cikin jakarta a 'yar kwalba ta mika mata tace "Nasan kin san ynda ake amfani da wnn, kina gama period sae kiyi amfani da shi kin ji" nn ma dae Afeefah shiru, wani turaren ta kuma fitowa da ta mika mata tace "Wnn kuma idan xaki kwanta ki dinga shafawa nasan dae duk an baki a gida amma ki kara, ina fatan dae duk kin fahimce abinda na gaya maki" Afeefah ta ki dago kai still, Amina tayi murmushi tace "To kwashe su ki xuba a drawern gaban mirron ki, ni xan tafi xa mu dinga waya kin ji" har Amina ta mike xata tafi Afeefah bata dago ba, ta ba Amina dariya ssae, sae dae a ciki ta bar dariyan ta fita, sae a snn Afeefah ta turo baki ta mike ta kwashi tarkacen ta xuba mu cikin jaka ta koma tayi kwanciyarta. Sae bayan fitarsu gidan snn Dr Sharif ya hauro sama ya shigo dakinta yana kallonta yace "Shi ne ba ki xo kin ma yayanki sallama ba koh" mikewa xaune tayi da sauri tace "Sir kace xa ka kira min yayanmu" wayar sa dake hannunsa ya karaso cikin dakin ya mika mata snn ya juya ya fita, duk layyukan uku sae da ta kira amma switch off, har da dan hawayenta duk ta kasa sukuni sae kira take bbu gajiya, hakura tayi daga karshe ta kwanta tana hawaye. Ana kiraye kirayen Magrib Dr ya shigo yace Ya tafi masallaci, kai kawae ta gyada masa ya fita, ko da ya dawo har ta fara bacci ya taso ta suka sakko kasa ya xuba mata dinner, har ta kwanta ranan bata da wani annuri a fuska, shi kam bae bi ta kanta ba yyi kwanciyar sa tare da lumshe ido. Washegari sae wajen takwas ta tashi taga baya dakin, bayi ta nufa da sauri ta wanke baki tayi wanka snn tayi na tsarki tayi alwala ta fito, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh ya shigo dakin, sanye yake da farar polo da rubutun blue sae blue jeans da yasa, yyi mugun kyau kamshin turarensa ya cika dakin, tayi saurin sunkuyar da kai, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Dama lkcn da kike tashi knn a gida shi sa kike makara xuwa lectures koh?" Turo baki tayi tace "Ae a gidanmu tashi na ake yi, nn kuma bbu wanda ya tashe ni" yyi murmushi yana shafa kansa ya karaso kusa da ita yace "Ban san xa ki yi sllh ba ae da na tashe ki" bata ce komae ba, jin shima yyi shiru yasa ta daga kai tana kallonsa idonta ya sarke cikin nasa tayi saurin sunkuyar da kai murya can kasa tace "Ina kwana sir" durkusawa yyi gabanta ya dago kanta yana murmushin da ya bayyana fararen hakoransa yace "Lfya lau amaryar sir" ta dauke kai da sauri ta boye fuskarta, yyi dariya ya dago ta yace "Sakko mu je muyi breakfast my bby" a hnkli tace "Shiryawa xanyi" yace "OK ina jiran ki a kasa" yana fadin hka ya juya ya fita, mikewa tayi ta fiddo kayan da xata sa, sae da ta fara amfani da miskin da Anty Amina ta bata snn ta shirya cikin atamfa java ta fesa turare ta sa hijab ta sakko kasa.
Da rana suna xaune falo yana kallo ita kuma tana kwance gefensa tana game da wayarsa tace "Sir mun koma makaranta fa" ya juya yana kallonta yace "Yea nxt wk xa kiyi resume" tace "Sir me sa baka son kayi lecturing kuma" ya girgixa mata kai yace "Na gama period dina ne, clinic xan koma ynxu, am also resuming work" bata kuma cewa komae ba har aka kira la'asar yyi alwala ya tafi mosque ita kuma ta haura sama don yin sllh. Da daddare ta karba wayarsa wae xata kira ya Aliyu shi dae kallonta kawae yake ta dinga kiran yayanmu amma still a kashe, wnn karan kuka ta saka masa wae ya ki shiga, shi dae bae tanka ta ba, ya dae lallabata ta ci tuwo da miyan vegetable da teemah ta kawo, da kyar ta dinga cin abincin don gaba daya baya ranta daga karshe ta bar masa sauran ta koma sama ya bi ta da kallo. Ko da ya shigo dakinta wajajen goma da rabi tayi wanka ta canxa kaya xuwa na bacci tana xaune gaban madubi tana
Kkrin daure gashinta amma ta kasa tsabar cikansa, dama a gida ya Aliyu ko Mami ke taya ta daure gashin don ko yayyinta ba wani iyawa suke da gashin ba, kasa ci gaba tayi ganinsa, ya karaso gaban madubin yana kallonta kmr me rada yace "shud I help" bae jira cewarta ba ya kai hannunsa kan gashin, ta fixge kanta da sauri kmr xata yi kuka tace "Bna so" shiru yyi yana kallonta ta dauki net ta shiga tura gashin ciki kawae, ita takaicin ta ynda ma xata tashi tsaye da kayan jikinta, da tasan xae shigo ynxu da tuni ta kwanta, rungume hannayensa yyi yana kallonta, ta gama tura gashin duk da bae gama shiga net din ba ta mike da sauri ta nufi gado don dauka hijab dinta ya fixgota ya hade ta da kirjinsa don dama singlet da 3qtr ne kadae jikinsa, k'ara ta saki tsabar tsoratan da tayi ta fara kiciniyar kwace kanta amma ya ki saketa yana kallonta, hawaye ya cika idonta muryarta na rawa tace "Plss stop this sir" Cikin kaushin murya yace "Stop what?" Tuni jikinta ya dau rawa ta fashe da kuka ssae tana girgixa masa kai tace "Plss sir kayi hkuri don Allah ka sake ni" a hnkli ya saketa ya koma gefen gado ya xauna ta sulale nn kasa xuciyarta na bugawa da karfi, murya can kasa yace "je kiyi alwala" da sauri tace "Nayi sllh sir" yace "Na sani, do as I say" jiki a mace ta tashi hawaye na sakko mata ta nufi bayi ta dauro alwala amma ta ki fitowa, ta kusa minti goma tsaye a bayin taji yace "Zainab" muryarta na rawa tace "Na'am" a hnkli ta tura kofar ta fito ta samesa xaune gefen gado, yana kallonta yace "Dauki hijab" ta dauki hijab dinta ya shimfida darduma ya ja su sllhn nafila raka'a biyu, ya dde yana addua'a, kafin ya juyo yana kallonta ya dafa kanta ta rufe ido da sauri gabanta na faduwa, addu'o'in ya kuma yi masu yana kallon ynda heart beat dinta ke karuwa, sae da ya shafa Addu'an har lkcn idonta a rufe snn ya daura hannu a kirjinta dae dae xuciyarta ta bude ido a tsorace xata yi baya ya fixgota cikin sanyin murya yace "Ki nutsu Zainab, ur heart is throbbing."
Chapter 63 · 0% Book details