← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 89

Sashe 51

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

66......
Shiru dad yyi yana kallon likitan, gnin jiran amsarsa likitan ke yi yasa ya sauke ajiyar xuciya yace " 'yar uwarsa ce Zainab" likitan ya jinjina kai yace "Shawara ce xan baku, in ma hanasa ita aka yi to a bashi in har kuna son lfya da kwanciyar hnklinsa" Dad ya share wani xufa da ke keto masa da kyar yace "Ce maka yyi yana sonta?" Likitan yace "Ae ba sai ya gaya min ba Alhaji, na fahimci komae" Dad ya dau fiye da second ashirin yana kallon likitan daga bisanni ya jinjina kai yace "Toh shknn ngd likita, xan iya shiga in gansa koh?" Likitan yace "Xa ka iya shiga amma idan ka tarar yana bacci kadda ka tashe sa" Dad yace "Toh ngd" snn ya mike ya fita daga office din rae a dagule, ya dde tsaye jikin bango yana mmkin lamarin daga karshe ya nufi ward din da Aliyu yake. Kwance dad ya samesa idonsa lumshe ya karasa gefen gadon yana kallonsa cike da tausayinsa, to amma me yasa tun farko bae fito yace yana son Zainab ba sae da ya bari aka karbi sadaki da kaya, Dad ya jinginar da kansa jikin kujerar da yake xaune ya shiga tunanin ynda xa'a bullo ma lamarin. Da asuba dad na dawowa daga masallaci ya sami Aliyu xaune ya cire drip din hannunsa ya dafe kansa, dad ya karaso da sauri yana kallonsa yace "Ya aka yi Ali? Ka tashi?" Da kyar ya dago kansa yana kallonsa da idanuwansa da suka sauya kala cikin sanyin murya yace "Sllh xan yi" Dad yace "Xaka iya kuwa?" Kai kawae ya gyada masa ya sauko daga kan gadon ya nufi bayin dake ward din yana gnin jiri. A ward din dad ya shimfida masa darduman da ya karbo, duk sae da Aliyu ya rama sallolin da ake binsa duk da jirin da yake gani, snn ya juya yana kallon dad dake ta kallonsa, ya sunkuyar da kai ya gaishesa cikin sanyin murya, Dad ya amsa yana murmushi yace "Ya jikin Ali" yace "Da sauki Abba" Dad yace "To Ma'sha Allah, Allah kara afuwa" Aliyu xae yi magana aka bude kofar dakin Mami ta shigo rike da flask din ruwan xafi da leda dauke da kayan beverages da Bread, murmushi ne ya bayyana fuskarta gnin Aliyu xaune kan darduma ta karaso ta ajiye abin hannunta tana kallonsa tace "Sannu Ali, ya jikin" duk da yyi mmkin ganinta bae nuna ba, ba tare da ya kalleta ba yace "Da sauki" mikewa yyi ya koma kan gado ya xauna ta bi sa da kallo snn ta karasa kan gadon.

Karfe sha biyu saura aka yi discharging dinsu don jikin nasa Alhmdllh, sae dae har lkcn jin xuciyarsa yake kmr ba tasa ba, duk da dad yaso ko da xuwa yamma ne a kuma gnin jikinsa amma Aliyu ya nuna shi ya ji sauki a sallamesa kawae, ssae likitan ya kuma jad'da'da ma Dad muhimmancin bayanin da yyi masa daxu a office, dad da duk tunanin ynda xae bullo ma lamarin ya damesa yace "In'sha Allah xa a kiyaye Dr" Saleem ne yyi driving dinsu ya maida su gida, kwanciya Aliyu yyi kan kujera a falo ya lumshe ido. Afeefah da sakkowarta falon knn ita da Anty Jamila da su Ilham xa su je asibiti don tun da asuba ta ishesu da kukan ita a kai ta gun yayanta, Aliyu ta gani kwance falo, ba tare da tayi wani tunani ba bata kuma damu da wa enda ke falon ba ta karasa wajensa da gudu ta fada kansa ta fashe da kuka ssae tana kallonsa, shima kallon nata yake ya kasa cewa komae, da kyar ta iya bude baki muryarta na rawa ta daura kanta bisa kirjinsa tace "yayanmu" lumshe ido yyi ya hade hannunsa da nata, cikin sanyin murya shima ya kira sunanta, mikewa dad yyi cike da damuwa don komae ya dagule masa ya fice daga falon, toh shi kam ya xae yi da Dr Aliyu da mahaifansa kar su daukesa karamin mutum, a balcony ya hadu da Dr Sharif da Ma'aruf suna kkrin shigowa, har kasa Dr Sharif ya durkusa ya gaishesa, dad ya amsa masa yana kirkiran murmushi, Ma'aruf ya gaida dad din nasa shi ma, snn suka tambayesa jikin Aliyu, dad yace "jiki Alhmdllh yana ciki" Mami kam tun shigowar Afeefah falon dama ta kasa daga kai daga karshe ma dad na fita ita ma mike ta haura sama ba tare da ta kallesu ba. Da sallama Dr Sharif ya shigo falon da Ma'aruf, Momy ta kalli Afeefah dake jikin Aliyu har lkcn bayan ta amsa masu sallaman tace "To Zainab ae sae ki daga sa hka nn, Kinga jikin sa ba kwari" dai dai nn Dr Sharif ya sauke ido kan Zainab dake jikin Aliyu har lkcn idonta rufe, sunkuyar da kai yyi sae dae kasa karasawa cikin falon yyi sae murxa makullin motar dake hannunsa yake, Ma'aruf yace "Bismillah mana Dr" sae a snn Afeefah ta dago da sauri suka yi ido hudu da Dr Sharif, a hnkli ta xamo daga jikin Aliyu ta dawo kasa tana kallonsa, sunkuyar da kai yyi ya karaso cikin falon, ya xauna nn kasan rug din falon cikin sanyin murya ya gaida mum, ta amsa tana murmushi hade da ce masa ya gajiyan jiya, Murmushi kawae yyi a sanyaye yana kallon Aliyu da ya kafa masa ido yace "Ya jikin" Aliyu ya gyada masa kai cikin sanyin murya yace "Alhmdllh," Dr Sharif yace "Allah kara afuwa" Ma'aruf yace "Sannu barrister, Allah kara lfya" murmushi kawae Aliyu ya iya masa, Afeefah kam tun shigowar Dr Sharif falon ta kasa dago kanta, har sae da Ma'aruf yace "Ina kwana Anty Zainab" snn ta dago a hnkli tana kallonsa ta kirkiri murmushi tace "Ina kwana yaya" Ma'aruf yyi dariya yace "A'a ki dae ce min lfya kawae, na bar maki yayan" Momy tayi dariya tace "Ae ka bar ta ynda ka ganta yau bbu wnda ta gaisar gidan nn, tunda ta dare kan yayanta ko waigo mu bata yi ba" Murmushi tayi snn ta kalli Dr Sharif dake kallonta har lkcn, cikin sanyin murya tace "Ina kwana sir" Sauke idonsa yyi daga kallon nata a hnkli yace "Lfya lau" mikewa yyi yana kallon Momy yace "sae xuwa anjima momy, xan tafi" Momy tace "breakfast fa Aliyu?" Yace "Mun yi momy" Aliyu dake kallonsa har lkcn ya kalla yace "Allah ya kara afuwa barrister" Aliyu yace "Ameen ngdd" Ma'aruf ya juya yana kallo yace "Captain sae xuwa ltr" bae jira cewarsa ba ya fice daga falon da sauri Afeefah ta bi sa da kallo a sanyaye, Mikewa Ma'aruf yyi ya bi bayansa, tsaye ya samesa ya hade kansa da motarsa, Ma'aruf ya dafa sa yace "Ya aka yi Dr" dagowa Dr Sharif yyi da kyar yana rike da kirjinsa da hannu daya yace "Bana jin ddi ne" Ma'aruf yace "Subhanallah, to ina xa ka ynxu" a takaice ya basa amsa yace "Hotel, xanje in sha drugs" bae jira cewarsa ba ya bude mota xae shiga don wani jiri yake gani, Ma'aruf ya riko sa da sauri ya karbi makullin motarsa yace "Let me drive yhu"
Chapter 51 · 0% Book details