← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 89

Sashe 47

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Afeefah na kwance ita kadae dakin Mami misalin sha daya saura na dare tayi jigum kmr mara lfya, Mami kuma ta shiga yin wanka a bayi, bude kofar dakin da aka yi yasa ta saurin dago kanta don ganin Wanda xae shigo, Anty Safiya ce ta shigo dakin, ta karaso kan gadon ta xauna tana kallonta, Afeefah ta mike xaune ita ma tana kallonta lkci daya hawaye ya taru idonta, Anty Safiya ta jawo ta jikin ta cikin lallashi tace "Kar ki kuma xubda hawayen ki Zainab, ba a taba cire ki cikin mutan gidan nn ba kuma baxa a taba ba, ki kwantar da hnklin ki Kinji little sis, duk daya muke a gidan nn wllh, amma ina son in maki tambaya daya Zainab" dago kai Afeefah tayi tana kallonta, Anty Safiya tace "Ae kina son yayanmu ko Zainab?" A tsorace Afeefah ta dago kai tana kallonta, lkci daya ta fashe da matsanancin kuka ta boye fuskarta jikin Anty Safiya cikin rawar murya tace "Wllh Anty ni bana sonsa, ni yayana ne shi, wllh yayana ne, yayanmu ne fa Anty" Shiru Anty Safiya tayi jikinta yyi sanyi kalau, amma bata ce komae ba, bude kofar bayin Mami tayi ta fito, cikin fada ta fara magana "kin ga ku kiyaye ni Safiya, ku kuma kame kanku tun kan ran ku ya baci a gidan nn, maxa fita ki bar min dakina" Mikewa Anty Safiya tayi jiki a mace ta fita daga dakin. Washegari ko breakfast din kirki Afeefah bata yi ba Mami ta dauki jakarta bayan ta ja ta sun je sun ma Abba sallama, shi dae ko iya bude baki bae yi ba har suka fita daga dakin, duk yan matan gidan dake xaune jigum a falo suka bi uwar tasu da kallo har ta fita daga falon tana rike da Zainab, Adnaan dake xaune balcony bae ko kallesu ba har suka sauka balconyn, Mami kam ko a jikinta don ko gaisheta yau ma bae yi ba, Sae da Mami ta ga tashin motarsu Afeefah snn ta juyo gida. Karfe goma da rabi Zainab ta isa gidan kawunta a Kaduna, a gajiye ta shigo falon, dake Momy ta san da xuwanta don Mami ta kira ta shaida mata ta mike da sauri da fara'a ta karasa ta amshi jakarta tana mata sannu da xuwa, jin hka su Ilham suka sakko kasa su ma suna welcoming dinta cike da murnar xuwanta, murmushi kawae Afeefah ke kirkira har suka haura sama snn ta fada kan gado ta yi kwanciyarta. Kyaleta su ilham suka yi sanin ta gaji, suna fita daga dakin nn da nn bacci ya dauketa. Da matsanancin ciwon kai Afeefah ta farka da azahar, ta mike da kyar ta nufi bayi don yin alwala, ko da ta idar kasa mikewa tayi daga gun, lkci daya hawaye ya cika idonta tunawa da tayi wae fa ashe ita agola ce a gidansu na kano, kuka ssae ta fashe da tuno maganganun Mami na jiya da ta dinga yi, dama ya Aliyu ba Muharraminta bane, to don me ake ta boye mata matsayinta, Dr Sharif ne ya fado mata, hkn yasa tayi karfin halin mikewa da sauri ta nufi wayarta dake kashe cikin jaka ta fiddo ta kunna, ta jima tana kallon wayar daga bisanni tayi dailin nmbr Dr Sharif, bugu biyu ya daga, a sanyaye tayi masa sallama, shima cikin sanyin murya ya amsa yace "yhu left me vry worried about yhu Dear, me sa kike kashe wayar ki now a dayz pls" Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tace "Kayi hkuri bbu charge ne" shiru yyi snn a hnkli yace "Are yhu still in Abj?" Girgixa kai tayi murya can kasa tace "No! Am in Kaduna ynxu" yace "Are yhu serious plss?" Dan murmushi tayi tace "Allah" yace "Waow m also in Kaduna ynxu, I just landed, jiya uncle din ki ya bukaci in xo if m less buzy, sauka na knn wllh, but let me ask yhu plss neman me yake min?" Xaro ido tayi tace "Nima daxu fa na xo sir, I don't knw" yace "Shknn, sae na shigo anjima da yamma, Allah sa kiran alkhairi ne Zainab" a sanyaye tace "Ameen" yace "Me kike son in taho maki da?" Murmushi tayi murya can kasa tace "Abu me ddi sir" murmushin shima yyi yace "Ok" sallama ya mata ya katse wayar, dai dai nn Anty Jamila ta shigo tana murmushi tace "Sarkin shagwaba sakko mu yi lunch, ina fatan kinyi sllh?" Afeefah tayi murmushi tace "Nayi Anty" snn ta mike ta bi bayanta. Ko da Afeefah ta koma sama bayan ta dan cakalkala abincin wanka tayi ta wanke bakinta ta fito snn ta dauki yar doguwar rigar ta shara shara mara nauyi ta sa, ta dauki net dinta ta saka a kanta, snn ta dauki wani nvl din Ilham dake dakin ta shiga karantawa absentmindedly, nvl din na hannunta har aka kira la'asar jin xa a tada sllh yasa ta Mike ta shiga bayi, ko da ta idar da sllh komawa tayi kan gado ta kwanta ta dalilin Sara mata da kanta yake ba kadan ba, har wani rufewa idonta yake tsabar ciwon da kanta ke mata, gashi taki nuna ma 'yan gidan bata jin ddi su kuma suka yi tunanin ko duk gajiya ne tunda mota ta biyo, hkn yasa Momy ta bata paracetamol ta kuma ki sha ta boye, wayarta dake ring ta jawo da kyar ta daga tare da karawa a kunnenta, muryan Wanda ta ji yasa xuciyarta ya kusa shigewa cikin ta don tsoro, cikin sanyin muryarsa me ddin sauraro ya kira sunanta a sanyaye, jikinta ne ya dau rawa lkci daya ta katse wayar snn ta kashe gaba daya ta jefar ta cusa kanta cikin pillow ta fashe da matsanancin kuka jikinta na rawa, ta jima tana kuka daga karshe bacci ya dauketa. Ko da Aneesah ta shigo dakin don yin alwala samunta tayi cikin bargo, ta yaye bargon tace "Lallai ma Zainab wae har ynxu gajiyan ne hka, baccin yamma ma da bae da kyau," shiru tayi jin jikinta ya dau xafi ba kadan ba, da mmki Aneesah tace "Baki da lfya ne Zainab," Afeefah ta bude idonta da ya sauya kala ta kasa ba Aneesah amsa sae hawaye da ta shiga yi, Aneesah ta juya da sauri ta fita, ba a dau lkci ba suka dawo da Momy da Anty jamila, Momy ta dago ta tace "Subhanallah baki da lfya ne dama Zainab?" Afeefah bata ce komae ba sae kuka da ta fara yi, hkn yasa hnklin Momy ya tashi ta juya tana kallon Jamila tace "Ke kira min saleem ya xo ya kai mu asibiti" Juyawa Jamila tayi da sauri ta fita, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Mami baya dagawa ina jin yana masallaci" Da damuwa Mami tace "gashi ni bna driving da daddare ko xaki iya Jamila?" Jamila tace "Da sauki Momy, ki bari nasan ana idar da sllh ma xae shigo," Tare Dr Sharif ya shigo gidan da Saleem, Jamila dake falo tana jiran shigowar yayan nata tayi masu sannu da xuwa bayan ta gaida Dr Sharif da fara'arta snn tace "ya Saleem kae fa muke jira tun daxu, asibiti xa ka kai mu Zainab bata da lfya" kallonta Dr Sharif ya tsaya yi, Saleem yace "Kai Haba me ya sameta?" Da damuwa Jamila tace "ta ki fadi, sae kuka take" Saleem ya kalli Dr Sharif yace "Dr mu je" ba musu Dr Sharif ya bi bayansa, suna shiga dakin ya tsaya kallon Afeefah da ke rungume jikin momy idonta rufe, Momy na ganin Dr Sharif tace "A'a Aliyu ashe ka iso, sannu da xuwa" dan murmushi yyi ya gaida ta ya karaso bakin gadon yana kallon Afeefah da ta bude ido tana kallonsa lkci daya tayi saurin kulle idon, a dan sanyaye yace "Momy me ya sameta" Momy tace "Wllh bamu sani ba, tun da ta xo dama naga yanayinta, wae da asibiti xa mu ynxh" Durkusawa yyi bakin gadon yana kallon Afeefah cikin sanyin Murya yace "Zainab!" Bude ido tayi a hnkli tana kallonsa, jin ta ki cewa komae yasa Momy ta saketa tace "Bari in baku waje" tana fita Jamila ta bi bayanta snn Saleem, Dr Sharif ya mike da damuwa ya xauna gefenta yace "Tok to me plss Zainab ina ke maki ciwo," bargon jikinta ya cire ta koma baya ta dukunkune waje daya da sauri Sbda kayan dake jikinta, dauke kai yyi har ta rufe jikinta da bargo snn ya juya ganin ynda idonta yyi ja ssae yasa ya kai hannunsa goshinta jin xafi yasa yace " Subhanallah, Mu je asibiti?" Da sauri tace "A'a!" Yace "To gaya min inda ke maki ciwo" a hnki tace "Kai na ke ciwo"

Eeshatullah Goni

[5/22, 07:57] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 47 · 0% Book details