Sashe 18
Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
27__28 Afeefah ne xaune daki ita da Sadiya, ita tana karanta handouts dinta sadiya kuma na kwance tana danna wayarta, Mami ta shigo dakin tace "wae me ku ke yi ne? Ina Jiddah? Ku fito ku daura girkin rana don bbu yar da xan ma girki yau ta ci ku fito ku shiga kitchen" tana kai wa nn ta juya ta fita daga dakin, Afeefah ta ajiye handout din hannunta da sauri ta kwanta tare da lumshe ido kmr me bacci, Sadiya tace "ehh kya ma bude idon ne yarinya, sannun ki da wayo" tana kai wa nn ta fice, Afeefah ta kuma gyara kwanciya kmr me bacci, Jiddah ce ta shigo dakin bayan kusan minti biyar tace "ke Afeefah baxa ki fito mu shiga kitchen bne" Shiru Afeefah tayi kmr me baccin gske, Jiddah ta juya ta fice, Mami ce ta shigo dakin a tsawace tace "Zainab!" Mikewa xaune tayi da sauri tana murxa ido kmr xata yi kuka tace "Mami ni bacci..." Bayi ta shige da gudu ta kulle tun kan Mami ta karaso ganin ta yo kanta, Muryar Adnaan taji a dakin alamar Mami taje ta kirasa yana cewa "baxa ki fito ba sae na bude kofar nn, wa kika ajiye xae maki girki a gidan nn, ke baki da aiki sae dae a baki ki ci ki addabi mutane da kukan bnxa koh" murguda baki tayi kmr yana ganinta taki bude kofar, gate taji an bude downstairs ta washe hakora sanin ya Aliyu ne ya shigo, lkci daya ta saki kukan karya, Adnaan ya bude baki yana kallon kofar hka ma su Jiddah dake bakin kofar dakin a tsaye suna jiran fitowarta, muryar Aliyu su ka ji a corridor din rooms din yace "me ya faru?" Jiddah ta tabe baki tace "kaga yayanmu Mami ce fa tace mu je muyi girki shine ta shige bayi ta kulle" daga cikin bayin Afeefah tace "yayanmu ka ga fa karatu nake xa muyi test Monday" kmr xata yi kuka ta kare maganar, Aliyu ya watsa masu harara yace "mutane nawa xa suyi girkin? Ina su Sumayya?" Sadiya ta bata fuska tace "ba suna sch ba su" ya kuma watsa masu harara yace "ku biyu baxa ku iya girkin ba sae kace masu girkin gidan bikin, common get lost my frnd" Muryar Mami suka ji tana cewa "ka ga Aliyu ka fita idona bana son kana min hka a gidan nn ita wacece da baxata shiga kitchen ayi girki da ita ba, ta fi wani ne a gidan nn, ko idan ta tafi gidan mijinta ni xan bi ta ina mata girki?" Murmushi Aliyu yyi yace "sae mijin ya yafe mata girkin Mami," wani harara ta balla masa tace "Ka fita harkana fa, kuma ta fito idan ba hka ba in sa Adnaan ya daure min ita yyi mata shegen bugu" Juyawa Aliyu yyi yana hararan Adnaan, Adnaan ya fice daga dakin kmr xae tashi sama, Aliyu ya juya yana kallonsu Jiddah yace "ku bar dakin nn kar in taka ku" ficewa suka yi da sauri, Mami tayi kwafa ita ma ta fice tana cewa ta fito ta samesu kitchen idan ba hka ba sae dae ta ci bbu yau a gidan nn. Suna fita Afeefah ta bude kofar bayin, ta fito tana turo baki, ya Aliyu yyi murmushi ya kama hannunta ya nufi dakinsa da ita, har aka gama girkin rana Afeefah bata fita ba, Mami ta kwashe rabonta ta kara ma mai gadi Jiddah ta kai mashi, sadiya na kai ma ya Aliyu nasa a daki yace "Na Afeefah fa?" Tace "ina jin yana kitchen" yace "to dauko Mata," kai ta gyada masa ta fice duk da tasan bata da rabo, sae da ta isa falo ta fara dariya, ganin sadiya bata dawo ba yasa yace taje ta dauko abincin ta a kitchen da kyar ta yarda ta fita wae Mami xata doketa, tana shiga kitchen taga bbu komae an ma wanke tukunyar, ta koma sama kmr munafuka tace "sun cinye yayanmu" murmushi yyi yace "je dauko spoon ki xo mu ci nawa," kitchen ta koma ta dauko spoon suka ci a tare. Da yamma tana kwance dakin ya Aliyu tana kallo shi kuma yana dakin Mami wayarta ya soma ring mikewa tayi xaune ta dauki wayar gabanta na faduwa, wnn nmbr jiyan nn ne dae, sau uku yana kiranta yau bata dauka ba, mikewa tsaye tayi ta nufi dakinsu da gudu ta mika ma Jiddah wayar tace "Aunty Jiddah ki daga ki tambayi waye don Allah" karban wayar tayi tana kallon nmbr snn ta daga tayi shiru, jin anyi sallama yasa tace "wa ke magana wae," "ba da ke nake son magana ba, mika ma Zainab wayar" kmr munafuka ta mika ma Afeefah wayar. Afeefah tace "wae waye yace maki" Jiddah tace "oho" kara wayar a kunnenta tayi ta hade rae yace "Hello" tace "ina jin ka?" Murmushi yyi jin ynda ta amsa mashi yace "Me yasa kika ba yayarki wayar, kina tsorona ne?" Girgixa kai tayi tace "sbda me xan ji tsoron ka, ae Allah shine abun tsoro?" Yace "yea gskya ne," ta hade rae tace "kar ka kuma kiran layina ni ban san ka ba" yace "amma ni na sanki" a fusace tace "a ina ka san ni?" Cikin sanyin murya yace "nasan ki a bayero da kuma jan bulo" xaro ido tayi da mmki amma ta kasa cewa komae, yace "are yhu there?" Tsaki tayi tace "toh ni ban san ka ba kada ka kuma kiran layi na" katse wayar tayi ta jefar kan gado, Jiddah tace "wllh ki daina irin hka, baki san ko wani irin mutum bne kawae yaje ya cuce ki a bnxa, gwara ki bi sa a hnkli ku rabu lfya" Afeefah kmr xata yi kuka tace "to ni ya xan yi, bace kada ya kuma kirana ya ki ji" Jiddah tace "a hnkli xaki bi sa har ya rabu da ke, amma kar ki masa wlknci ko ki gaya masa bakar magana baki san wani irin mutum bne shi, baki kuma san meye a xuciyarsa ba, Afeefah ta bata fuska tace "wayyo na shiga uku to ina ya samu nmbrna Anty Jiddah?" Jiddah tace "oho ta ya xan sani nima" Afeefah tace "to in gaya ma yayanmu?" Da sauri Jiddah tace "ke! Gaya masa to tunda baki sa hnkli, so kike ya kirasa kawae ya xaxxagesa ki ja ma kanki" Afeefah tace "to to baxan gaya masa ba ba ruwana" fice wa Jiddah tayi daga dakin da sauri jin Mami na kiranta Afeefah ta xauna kan gado a sanyaye gabanta na faduwa, to waye wnn mutumin kuma, da daddare tana dan dube dubenta a wtspp Msge ya shigo da wani sabon nmbr, kura ma nmbr ido tayi lkci daya ta gane na me kiranta ne, gabanta na faduwa ta bude Msge din tana kallon sallamar da yyi mata, dakewa tayi ta amsa ko Allah xae taimaketa ya gaya mata inda ya Santa, bude Dp dinsa tayi da sauri tayi don ganin meye a kai, taga wata kyakkyawar yarinya rike da cake me kyau alamar birthday tayi, kallon yarinyar kawae take don gani take kmr ta taba ganinta amma ta rasa a ina, can ta fita taga bae mata reply ba still, kin sauka tayi tana jiran reply din, har bayan kusan minti takwas snn reply ya shigo, "ba ki yi bacci ba? Yhu re suppose to b readin ur book fa, who are yhu chattin with this late?" turo baki tayi ta mayar masa da cewa "Don Allah where did yhu get my contact frm, don Allah na ce" sae bayan kusan minti biyar reply ya shigo, "Go offline now!" Tsaki ta dan yi tana mmkin irin command din kmr ta san shi, reply ta mayar masa tace "ba ka ma Allah knn?" Lkci daya ya mata reply da cewa "to wa ke xan ma idan ban ma Allah ba, common go offline my frnd, idan baxa kiyi karatu ba ki kwanta kiyi bacci nd stop wasting ur tym here" ji tayi kmr ta saka kuka don takaici, gashi tana tsoron masa musu da ta tuno maganganun Jiddah, "OK" kadae ta mayar masa snn ta sauka ta kashe data ta jefar da wayar gefenta tayi kwanciyarta. Washegari kmr jiya vibration din wayar ta ne ya tasheta, ta jawo wayar da kyar tana kallon screen, din ta wara ido da sauri ganin lambar, samun kanta tayi da dagawa daga daya bangaren taji yace "almost tym for sallat baccin ya isa hka Madam" takaici ne ya isheta cikin bacin rae tace "to Ca nayi maka bbu masu tashi na ne a gidan mu" a nutse yace "ban ji ba, me kika ce" tsoro ne ya kamata tace "Ca nayi nagode, ynxu xan tashi" yace "OK" snn ya katse wayar. Da safe suna xaune dinnin suna breakfast, da ke ranan Saturday ne har da Adnaan da ya Aliyu Mami ce kadae bata dinnin din, Sumayya tace "ya Aliyu wnn hutun ka dde sosae" Afeefah ta galla mata harara tace "just two wk shine xa ki ce ya dde...." Wayarta da ke vibrate ne yasa tayi shiru tana kallon screen din wayar, ta dago kai tana kallon Jiddah da ta tabe baki ta ci gaba da shan tean ta, mikewa tayi ta nufi stairs da sauri, ya Aliyu ya bi ta da kallo, dakinsu ta shiga ta daga kiran kan ya katse ta kara a kunne, "Ae nayi xaton baxa ki daga ba" murguda baki tayi kmr yana ganinta ta ki cewa komae, "Zainab!" Ta amsa da "Na'am," yace "Gud mrnin" da kyar ta iya mayar masa da gaisuwar, yace "kinyi breakfast," girgixa masa kai tayi tace "shi nake yi" yace "okk srry, sae anjima" ji tayi an bude kofar dakin ta katse wayar da sauri ta juya tana kallon ya Aliyu, yace "wa ya kira ki?" Kame kame ta soma yi tace "yayanmu, kaga dama yayanmu Maryam kawata ce ta kirani," a nutse yace "karya kike, tell me the truth wa ya kira ki" muryarta na rawa tace "Ita ce yayanmu" ya fi minti biyar yana tsaye yana kallonta snn ya fice daga dakin, ta sulale kan gado ta xauna tare da sauke ajiyar xuciya, hka ta karashi mid break a gida