← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 89

Sashe 15

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hnkli Afeefah ta tura kofa ta shigo bayan tayi sallama ta karasa kusa da table dinsa kanta a kasa tace "am here sir" jin bae ce komae ba yasa ta dago kai tana kallonsa, hararanta taga yana yi, yace "Sit" ba musu ta xauna tana kallonsa, yace "Me aka maki a gida?" A hnkli tace "yayanmu ne ya gaya ni da Abbanmu" kallonta yake yace "Me kika masa?" Girgixa masa kai tayi kmr xata yi kuka murya can kasa tace "wae don nace ka bani coffee" shiru yyi yana kallonta gnin hka yasa ta soma wasa da fingers dinta, "me yasa kika gaya masa na baki coffee?" Dago kai tayi ganin hawaye idonta yace "kar ki min kuka" gyada masa kai tayi ta mayar da hawayen snn tace "Dama yace in hado masa coffee ne da daddare shine da na kai masa daki nace masa ashe coffee yana da ddi ban sani ba sae yace eh mana, sae nace masa har da madara ka sa min....." Murmushin da taga yana yi yasa tayi shiru tana kallonsa, ya ce "ina jin ki" shiru tayi har lkcn, yace "go on!" Sunkuyar da kanta tayi tace "shine sae ya mareni, kuma ya gaya ni da Abbanmu ana ta min fada" muryarta na rawa ta kare maganan tana kallonsa, a hnkli ya daura fingers biyu kan lips dinsa yace "kar ki min kuka" ta gyada masa kai tare da hadiye kukan, murmushi ya kuma yi yace "meyasa kika gaya masa na baki coffee?" Girgixa masa kai tayi tace "ni ma ban sani ba" yace "beside gani nayi kina kallona ranan shi yasa na baki Zainab" xaro ido tayi tace "sir ni ban kalle ka ba wllh" murmushi kawae yake ya jawo foil papern dake desk a gabansa ya warware ya dauki table knife yyi slicin cake din ciki ya soma ci a hnkli yace "ya sunan yayan naki?" Sauke idonta tayi daga kallonsa tace "Ya Aliyu!" Ya dan wara ido yace "uhhn Namesake dina ne knn" Bata ce komae ba, bayan kusan minti uku ta dago kai tana kallonsa jin bae ce komae ba, suka hada ido don kallonta yake tayi saurin sunkuyar da kanta, cake din gabansa ya dauka ya mika mata yace "Take" ta girgixa kai da sauri tace "Thnk yhu sir" hararanta yyi yace "Shine kuma kike kallona?" Kmr xata yi kuka tace "ni ban kalle ka ba wllh" a dan tsawace yace "C'mom take this" har wani rawa hannunta yake ta karbi cake din da yake mika mata, yace "Eat" tace "Sir...." Kallon da ta ga yana mata yasa ta kai cake din bakin ta shiga ci a hnkli yana kallonta, rabi ta ci tace "Sir na koshi wllh" ba tare da ya kalleta ba yace "In xubar kike nufi, yhu had beta finish it right away," kmr xata yi kuka ta karasa cin cake din ya mika mata table watern da ya fara sha, ta karba a hnkli ta bude ta sha snn ta ajiye sauran, wayar ta dake jaka ne ya soma vibrate ta bude jakar yana kallonta ta fiddo wayar, xaro ido tayi sae kuma ta mayar da wayar da sauri yace "feel free, pick yhur cal" girgixa masa kai tayi da ganinta kasa a tsorace take, a nutse yace "wa ke kira?" Da kyar ta iya cewa "Yayanmu" yace "To dauka mana" bude jakar ta ta dauko wayar da ya katse a lkcn, kuma kira aka yi, ta daga kai tana kallon Dr Aliyu kmr xata yi kuka, yyi murmushi yace "pick" daga kiran tayi ta kara a kunne tayi shiru, ya Aliyu yace "Baki gama fushin ba Afeefah" turo baki tayi tace "Eh" yar dariya yyi yace "Srry Angel, nayi laifi baxan sake ba...." Make kafada tayi ta fashe da kukan karya tace "bana so, kuma ni bbu ruwana da kai kar ka sake min magana bbu ruwana da kai" Kallonta kawae Dr Shariff yake, ya Aliyu yace "ohh Haba yar Kanwata, I said am srry, yhu caused everything" ta kuma saka kukan karya tace "ni ka kyaleni joor" lallashinta kawae ya Aliyu ke yi yana mata promises kala kala, lkci daya ta fashe da dariya tace "yhu Promised fa yayanmu" yace "Allah Kanwata I mean it" dariya take sosae tace "ohk byee na hkura" katse wayar tayi ta mayar cikin jakarta ta dago kai tana kallon Dr Aliyu da ya kafa mata ido, wani kunya ya rufeta ta rufe fuskarta da tafin hannunta da sauri tana yar dariya tace "Sirrr" murmushi yyi yana kallonta har lkcn, hkn yasa ta cusa kanta cikin Hijab dinta tana dariyar jin kunya.

Eeshatullah Goni😘😘
🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

Dedicated to all my fans.... Luv u all❤❤

22......

Gajiya tayi da boye fuskarta ganin bae ce mata komae ba ta bude fuskar a hnkli ta mike ba tare da ta kallesa ba tace "Sir am goin home" Yace "ashe bayan kuka ma har da dariya kika iya hka?" Boye fuskarta ta kuma yi da sauri ta fara wani sabon dariyar kmr an aikota, murmushi yyi yana kallonta, can ya mike ya dauki makullansa ya fice daga office din ta bi bayansa. Ba tare da ta kallesa ba yana kulle office dinsa tace "Sae gobe sir" yace "OK Allah ya kai mu" Main gate ta nufa ta samu adai daita da xae kai ta har gida. A falo ta samu ya Aliyu da Mami ta gaida Mami shi kuma ta 6alla masa harara xata haura sama Mami tace "ina su Jiddah" Tace "Mami sae shidda fa xa su gama lecture ni kuma tun uku na gama" Mami bata ce komae ba Afeefah ta haura sama, Aliyu ya dan saci kallon Mami snn ya Mike ya bi ta. Bedroom dinsu ya sameta ta bata fuska tace "ni ka tafi" Dariya yyi yace "ba kin ce kin hkura ba Kanwata" juya masa baya tayi yace "To ki shiriya mu fita yawo da daddare," tsalle ta doka ta rungumesa tace "Yeehhh thanks yayanmu, wllh na hkura" dariya yyi yace "toh ina jiran ki downstairs ki xo mu yi kallo," juyawa yyi ya fice daga dakin, ta shiga cire kayan jikinta snn ta fada bathroom don yin wanka. Da daddare Ya Aliyu ya fita da ita kmr ynda yyi mata alkawari, yawo suka yi ssae snn ya biya da ita shoprite don siya mata ice-cream da kuma shopping da ta ce xata yi, Shopping ta fara yi duk abinda tasan tana bukata ta dinga diba yana tura mata trolleyn, bangaren Ice-cream suka nufa daga karshe bayan ta gama siyayyanta tace "yayanmu mu dan siya ma su Anty Jiddah da Sumayya kar su ji haushi na koh? Ka ga suna ta fushi da xa mu fita" Yace "to xa mu siya masu" ice-cream robobi Shiddah suka siya snn ta kuma sa shi ya siya mata Wanda xata sha a hanya aka sa mata scoop biyu na vanilla da chocolate, juyawa tayi da sauri ba tare da thinking twice ko akwae mutum a bayanta ba taji ta fada jikin mutum kusan rabin ice-cream din hannunta ya xube jikinsa, da sauri ta koma baya, ta xaro ido ganin duk ta juye masa ice-cream din ta daga kai tana kallonsa feelin guilty, sae kuma hkurin da take shirin fara basa ya makale ta kafa masa ido, murya can kasa tace "Sir!" Kallonta shi ma yake, ta cire dankwalin kanta da sauri ta shiga goge masa ice-cream din chest dinsa bayan ta dafa shoulder dinsa duk da ynda ya fi ta tsayi tana cewa "Am srry sir bn san.... Kayi hkuri plss sir" kallonta kawae Dr Shariff yake, kanwarsa ce ta bullo da trolley tana ganin abinda ke faruwa ta karaso da sauri tace "ya aka yi yaya, bata gani ne," Afeefah dake goge masa jikinsa har lkcn da dankwalinta tace "Mistake ne bn sani ba" kmr xata yi kuka ta kare maganar tana kallon yarinyar, Dai dai nn ya Aliyu ya karaso gun da trolley ya tsaya kallon Afeefah da mamaki yace "meye hka wat happened?" Kmr xata yi kuka tace "ban sani ba na buge sa yayanmu shine sae ice-cream ya xube jikinsa" Karasowa Aliyu yyi ya fixge dankwalin hannunta yana mata mugun kallo, snn ya karasa goge ma Dr Sharif jikinsa ya danka masa dankwalin ba tare da ya lura da na Afeefah bne fuskarsa a daure yace "srry" snn ya ja ta suka bar wajen, waigawa take tayi tana kallon Dr Sharif da ya bi su da kallo kafin su sha kwana ta daga masa hannu alamar _bye bye_ tare da yi masa murmushi, shi ma ya mayar mata, biyan kudin kayansu yyi yana janta har lkcn fuskarsa a daure suka fita ya tura ta cikin mota cikin tsawa yace "don kin xuba masa ice-cream shine xa ki kama gardi kina goge masa jiki? Kina da hnkli kuwa?" Girgixa masa kai kawae tayi, yyi tsaki ya xaga driver seat ya ja motar a fusace ya bar wajen. Sae da suka isa gida yyi parkin snn ya kamo hannunta a hnkli yace "am srry sweet sis, me yasa kike taba namiji" sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, hkuri ya shiga bata don yyi mamakin rashin kukan da bata yi ba, daga karshe ta dan yi murmushi alamar ta hkura, shima murmushin ya sakar mata ya ja kumatunta yace "ko kefa yar Kanwata," a hnkli tace "dankwali na yayanmu" yace "yana ina?" Ta dan yi shiru snn tace "ka bar masa" wara manyan idonsa yyi yace "meyasa baki ce min naki bane? Ohh yi hkuri xan siya maki wani atamfar me kyau kin ji" murmushi tayi da ya bayyana beauty point dinta da ke gefen kumatunta na dama tace "thnk yayanmu" ya bude motar ya fita ya fiffito mata da kayanta ya kira su Jiddah su xo su kwashe.

Eeshatullah Goni😘😘🌸👩🏻 'Ya mace Kyautar Allah 👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 15 · 0% Book details