← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 89

Sashe 2

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

2.... Washegari da safe Afeefah da sauran yayyinta suka gama shirin tafiya makaranta don duk Bayero suke, suka sauko kasa gaba daya don yi breakfast, su Sumayya dama bakwae da rabi suke barin gidan, tea kawae Afeefah ta hada, ita a dole fushi take tun kan abinda ya faru jiya, bbu Wanda ya kalli inda take, Adnaan sae watsa mata harara yake ganin bata gaishesa ba ta kuma ki gaishesan, ya gama shan tean sa ya mike don shima yyi shirin xuwa aiki ne da yake Banker ne shi, Kudi ya ciro a aljihunsa dubu biyu ya mika ma jiddah yace "ga wnn ke da sadiya ku kara a kudin break yau" Afeefah ta shiga mitstsika ido murya can kasa tace "ina kwana yaya" harara ya galla mata yace "wnn kuma da wa take" mikewa tayi da sauri tana kkrin boye dariyarta ta kamo hannunsa tace "wllh ni ma sae ka bani yaya" ya fixge hannunsa yace "da'alla" su Sadiya suka dinga dariya ta fashe da kukan karya ta rungumesa tace "ni wllh yaya kana ganinsu ko" murmushi yyi ya ciro duba daya ya mika mata ta washe hakora tace "ngdd yayana" yace "ayi karatu da kyau snn ya fice rike da briefcase dinsa don ya sallami Mami, Abba bae yrda sun sa gyale su fita ba don hka dukkansu da Hijab suke xuwa sch, Afeefah ta nufi dakin Aliyu ganin bata gansa ba tun da ta sauko ta gansa kwance yana bacci har lkcn, ta isa kusa da gadon ta dan yi kara ya bude ido da sauri tace "yayanmu xa mu tafi" harara ya galla mata yace "nace ki daina tashi na idan ina bacci" ta turo baki ta juya ta fice daga dakin, Driver na ajiyesu makaranta duk suka kama hanyar Faculty dinsu, Afeefah da ko sati biyu bata yi da fara Bayero ba taji duk makarantar ya isheta, lecture Hall dinsu ta nufa tayi mmkin ganin har an soma lecture, ta karasa gun kofar shiga lecture hall din ta tsaya kmr munafuka don bata manta me Aunty Safiya tace mata ba wae idan ka xo ka tarar lecturer ya shiga class to kadda ma ka sa ran shiga lecturen ranan don koro ka xae yi, lecturan da baxae wuce shekaru talatin da biyu ba ya daga kai yana kallon ta, ta dauke kai da sauri ya ci gaba da lecturing dinsa, har aka kai karshen lecture din Afeefah na tsaye inda take, ya bada assignment snn ya kwashi takardunsa ya fito ta basa hanya da sauri, yana kallonta yace "me yasa ba ki shiga lecture ba?" Kmr xata yi kuka tace "idan na shiga xa ka Kore ni" Murmushi yyi kawae ya wuce, ta nufi wani karkashin bishiya a sanyaye tana tunanin shknn bata samu lecturen safe ba, wata yarinya ce ta xauna gefenta tace "Baki shigo lecture ba kika tsaya bakin kofa, ae wnn lecturan baya kora da kin shigo" Afeefah tace "haba" yarinyar tace "wllh kuwa, ga handout din da ya bada sae kiyi photo copy, ya sunan ki" Afeefah tace "sunana Afeefah" yarinyar tace "ni sunana Maryam Sadis" Afeefah tayi murmushi tace "nyc name" Maryam ta mike tace mu je kiyi photocopyn," Afeefah ta mike ta bi bayanta suka nufi shagunan da ake photocopy. Karfe uku da minti sha biyar suka fito daga lecturen su na karshe ranan, Maryam tace "mu je mu dan sha drinks kafin lkcn sllh yyi" wani cafeteria suka nufa suka karbi drinks biyu suka xauna suna sha suna hira kmr da can sun saba, Afeefah tace "to dan koya min lecture din da ku ka yi da safe mana idan kin gane" Maryam ta bude handout din tace "nima fa ba wae na gama ganewa ne ssae ba don ni course din wahala yake min, amma bari in maki bayani iya in da na gane" bayani Maryam ta shiga yi mata da farkon handout din kmr ynda lecturen yyi masu, murya suka ji daga gefensu duk suka juya suka juya gaba daya, lecturan course din suka gani xaune shima da drink a gabansa, yana kallon Maryam yace "idan lecturer yyi maku lecture ba ku gane ba, tun a ajin ya kamata kuyi tambaya ya ganar da ku" Maryam tayi murmushi cike da jin kunya bata ce komae ba, Afeefah ma ta sunkuyar da kai, mikewa yyi ya dawo spare kujerar dake kusa da su ya xauna, ya karbi handout din ya shiga masu bayani gaba daya har sae da ya tabbatar sun gane, godiya ssae suka yi masa barin Maryam, ya sakar masu murmushi yace "yhu re all welcm" yana kallon Maryam yace "ya sunanki?" Tace "sunana Maryam," ya gyada kai yace "nyc name, ke fa me tsoron shiga lecture" ya fadi hka yana kallon Afeefah, ta sunkuyar da kai da sauri cike da jin kunya tace "Afeefah" ya wara nanyany idonsa yace "Afeefah kuma, sunan gskyan ki xa ki fada min" murmushi tayi har lkcn bata dago ba tace "Zainab" yyi murmushi shi ma yace "Nyc name, next tym ki dinga xuwa sch da wuri don kadda ki dinga missin lecture daga farawan ki" ta gyada masa kai tace "nagode" mikewa yyi, yyi excusing kansa ya fita daga cafterian.

Eeshatullah Goni😘😘

🌸👩🏻'Ya *Mace* Kyautar Allah🌸👩🏻

A true life *love* story

By *Ashmaad*

3.....

Kallon juna sukai snnan maryam tace "saiki ki kkri nxt class dinshi kixo dawuri sabida course din mutuminnan naada wahala, tana fadin hka ta miqe tashi muje masallaci muyi sallah mutafi gda, masallaci suka shiga sukai sallah suna idar wa ta dauki wayanta sabida tunda take sallah taji yna vibrating, missed call din Sadiya tagani saita dubi maryam tana cewa " kinga drivern mu yaxo saimun hadu gobe, har ta wece sae ta kuma dawowa" what tym Muke da lectures Cox bbu tym table a gurina" 8:30am ki kkri kixo dae da wuri don matar itama da xarar tashiga to bbu wanda xai shiga, godiya tae Mata sukai sallama, tana fita sukaci Karo da jiddah "dallah mallama kixo mutafi tuntuni muke jiranki sallah kamar kina hadawa tun daga subhi, harararta afeefah tayi tai wucewarta ta shige motar,

Basu fita daga motar ba har sae da drivern ya ijye motar a parking space snnan suka fita, afeefah ce karshen fita koda ta fito saita nemi su jiddah tarasa wanda suna fitowa da sauri sukai cikin gida, ta6e baki tae tana tafiyarta a hankali kamar wadda kwae ya fashe mawa, tana stepping qafarta cikin gidan taji an fuxgota da sauri ta juya tana fadin yaya adnaan me kuma nae? "kewae yaushe xaki wayo? Sisters dinki kowacce saida ta gaidaani kafin suka shiga gida, amma kina ganina kika dauke Kai wlh saina saisai ta maki tunani a cikin gidannan, tuni hawayen dake idonta suka soma bin kuncinta daidai lokacin Aliyu yashigo da sauri ya rungumeta "Adnaan! Adnaan!! Adnaan!!! Kaji na kiraka sau uku, wlh idan baka fita harkar afeefah ba ranka xae baaci, Akan wani dalili xaka tasata gaba tuntuni na lura kap cikin yarn gdannan kafi sa mata ido matsawar ka cigaba da takurata wlh ranka baxai kyauba" am telling u this, shikam mamakin duniya duk suka isheshi ya rasa dalilin dayasa Aliyu ke haka bbu dama yaji anamata fada, Amma idan shi yatashi mata bbu mai cewa don me

Tana shiga daki ta nufi bathroom tae wanka, kaya mara nauyi tasaka jikinta ganin yamma tayi dakin ma'mi tashiga ta gaidata "ya makarantar afeefah? Cewar ma'mi,... Hmm!! Ai ma'mi yaukam ban samu lecture din safe ba, ina xuwa na tarar da lecturer a cikin lecture hall din duk a tunanina shima mutumin bai bari a shiga idan ya shiga ashe shi baya Koro, ma'mi tace to baki samu wasu sun nuna miki ba? Nasamu handout din nai photocopy cikin ikon Allah sai muka hadu da lecturen ya koya mana har muka gane "masha Allah" gobe ma kya kara Komawa baccin asbah, don ya koya maku yau bashi xaisa nxt tym ma ya koya makuba, gara kudinga hakura da baccin asbah a'ah tou
Chapter 2 · 0% Book details