← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 89

Sashe 50

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

65.....
A hnkli Afeefah ta bude idonta ta sauke kan Ma'aruf dake xaune kan kujera kusa da gadon da take kwance, mikewa yyi lkci daya ya sakar mata murmushi ya kama hannunta yace "Kin tashi Zainab" kkrin mikewa xaune ta shiga yi hkn yasa ya taimaka mata ta xauna, ta shiga bin ward din da kallo kmr me son tuno abu, xumbur ta shiga kkrin sauka daga kan gadon ya riketa da sauri yace "Ina xa ki?" Kuka ta saki a rikice tace "Ya Ma'aruf ina yayanmu?" Ya kwantar da murya cikin lallashi yace "yana lfya wllh, Kinga bacci yake ki bari...." Kuka ta kuma fashewa da tace "A'a ni wllh ka kai ni wajensa in gansa don Allah don annabi" ya hade rae yace "baki ji me nace maki bne, shima ae yana nn asibitin, kuma nace maki bacci yake" xata yi magana aka bude kofar dakin Saleem ne ya shigo da sallama Dr Sharif na biye da shi a baya, hadiye sauran maganar tayi ta sunkuyar da kanta sae dae har lkcn hawaye na bin kuncinta, Saleem ya karaso yana murmushi yace "Kin tashi Zainab?" Kai kawae ta gyada masa ba tare da ta kallesa ba, ya karaso bakin gadon ya daura hannunsa a goshinta yace "hope bbu inda ke maki ciwo koh?" Gyada masa kai tayi nn ma, a hnkli ta dago kai tana kallon Dr Sharif dake tsaye daga gefen Ma'aruf, murmushi ta sakar mata cikin sanyi murya yace "Sannu, ya jikin" sunkuyar da kanta kawae tayi, a hnkli tace "Da sauki" ya karaso bakin gadon ya dan rage gudun drip din snn ya juya ya fita. Duk irin ynda Zainab ke ta damun Ma'aruf da Momy a cire mata drip din hannunta a kai ta taga yayanmu kin bari a cire mata suka yi wae sae ya kare, hkn yasa ta dinga hawaye, sae bayan maghrib drip din hannunta ya kare, ana cire mata kuwa ta sakko daga kan gadon wani jiri ya debe ta, Ma'aruf yyi saurin rikota, Momy tace "To ina xaki ji karfin jikin ki kin ki cin abinci, jamila hado mata wani tean" Afeefah ta girgixa kai da sauri tace "Allah momy na sha dayawa daxu don Allah a kai ni in gansa mana" hawaye na bin kuncinta ta karasa maganan, Ma'aruf yace "To sae kin yi alkawarin baxa ki je ki daga ma mutane hnkli da kukan ki ba" da sauri tace "Allah" Ma'aruf ya kama hannunta yace "To muje" binsa kawae take har suka fita daga ward din, da ganinta kasan bbu karfi jikinta, A hnkli Ma'aruf ya turo kofar dakin ya shiga tana biye da shi a baya, yana kwance idonsa a lumshe ga drip a hannunsa, a hnkli yake numfashi, Mami ta gani xaune gefensa da saleem, kallo daya Mami tayi mata ta dauke kanta, Afeefah ta karasa bakin gadon a sanyaye hawaye na bin kuncinta tana kallonsa, wani kuka ne ya xo mata Ma'aruf ya janye ta daga jikin gadon yace "Hka muka yi da ke" girgixa masa kai ta shiga yi da sauri, yace "To mu tafi ae Kinga bacci ya ke" cikin kuka tace "A'a kayi hkuri Allah ban gama ganinsa ba" Ma'aruf xae yi magana Dad ya shigo dakin, murmushi yyi ganinta ya karasa kusa da ita ya dafa kanta yace "kin tashi mamata, bbu inda ke maki ciwo koh" kai kawae ta gyada masa hawaye na bin kuncinta, ya kama hannunta suka fita daga dakin xuwa can harabar asibitin, ya samu wasu kujerun roba biyu suka xauna, nn ya shiga lallashinta yana assuring dinta jikin Aliyu da sauki ssae, bacci kawae yake, muryarta na rawa tace "Amma aman jini fa yake yi dady" dad yace "Nace ki kwantar da hnkli mamata ae baxae sake ba, xuwa anjima xa ki ga ya tashi" suna nn xaune har mota ta shigo haraban asibitin, yana gama parkin ya fito, ganin dad yasa ya nufi inda suke xaune dad yace "Har ka dawo Ali" Dr Sharif yace "Eh na dawo Abba," Dad yace "Nawa maganin yake" Dr Sharif yyi murmushi yace "Dubu sha biyar ba dari biyar" Dad ya sa hannu a aljihu yace "Ina da kudi a nn, bari in baka" wani murmushin ya kuma yi yace "Ka bar shi Abba" Dad ya hade rae yace "Kai bana son hka ba ni na aike ka ba wae, gashi" juyawa yyi ya bar wajen yace "Allah ka bar shi Abba" duk ynda dad ya so ya dawo kin dawowa yyi har ya shiga cikin asibitin.
Har Karfe tara da kusan rabi Aliyu bae farka ba, Dr Sharif yyi assuring dinsu sae xuwa can eleven xae tashi, bae kai Karfe goma a asibitin ba yyi ma Dad sallama ya tafi tare da Ma'aruf, gnin har goma da rabi ya kusa yasa dad yace saleem ya mayar da su Momy da Mami gida shi xae kwana asibitin, Momy da Mami na fita dakin dad ya kalli Afeefah dake xaune har lkcn kusa da Aliyu yace "Mamata tashi ki bi su ku tafi gida ki huta gobe sae ku dawo" marairaicewa tayi tace "Wayyo dady ka bar ni nima in kwana nn plss" Dady yace "A'a ku tafi kawae gobe ae xaku dawo da safe" Saleem ne ya kama hannunta gnin har idonta ya cicciko yyi ma dady sallama suka fita don shi xae mai da su Momy gida. Karfe sha daya da minti arba'in dad ya ga Aliyu na jujjuya kai, mikewa yyi daga xaunen da yake da sauri ya karasa kan gadon yana kallonsa, gnin yanda yake rike da kirjinsa yana jujjuya kai yasa dad ya nufi kofa da sauri don xuwa kiran nurse, ji yyi yana ambaton sunan Allah can kasa, dad ya juya da sauri yana kallonsa, lkci daya ya ga ya bude ido ya mike xumbur kmr Wanda aka tsikara lkci guda ya shiga kiran Zainab yana kkrin sakkowa kasa, da hanxari Dad ya koma ya rikesa yana kiran sunansa, girgixa Kai kawae yake yana rike da kirjinsa da yake ji kmr xae tsage ya daura kansa kan kafadar Dad, dad na pat din bayansa a hnkli, sae da ya nutsu snn dad ya dago kansa yana kallonsa yace "Sannu Ali" kasa cewa komae Aliyu yyi sae bin dakin da ya shiga yi da kallo kmr me son tuna abu, lkci daya ya kuma xabura dad ya mayar da shi xae kwantar don ya fita kiran likita, ya rike dad da sauri hawaye ya shiga gangarowa idonsa yana girgixa Kai kmr me son yin mgna amma ya kasa, dad da hnklinsa ya tashi ssae yace "Bari in kira likita ynxu Ali, am coming" kin sake sa still Aliyu yyi muryarsa na rawa yace "Abba, Zainab" da mmki dad yake kallonsa don a iya saninsa he was unconscious ko da Zainab ta suma daxu, dad yace "Zainab kuma, Me ya sameta? Daxun nn suka wuce gida har da Mamin ka Ali" girgixa kai kawae Aliyu ke yi hawaye na sakko masa yace "Abba kar a raba ni da ita don Allah, Abba a tausaya min a bani Zainab, Abba....." Kasa ci gaba yyi ya dafe kirjinsa da ke masa azaba da hannu biyu ya runtse ido, kallon mamaki da confusion Dad ke masa baki bude, wani kara Aliyu ya saki da karfi yana girgixa kai yana rike da kirjinsa da yaji na neman tsagewa, a rikice dad ya mayar da shi ya kwantar da sauri ya nufi kofa xae fita ya ci karo da likita da nurses guda biyu, hanya ya basu suka shigo dakin, kasa tsayawa dakin dad yyi ya fita a sanyaye maganganun Aliyu na masa yawo a ka, me knn? Dad ya fi minti sha biyar a corridor din wards din jingine jikin bango duk jikinsa yyi sanyi likita ya fito yana kallonsa yace "Alhaji mu je office" binsa Dad yyi har suka shiga office din, likitan ya ajiye stethoscope din hannunsa yace "Alhaji wacece Zainab?"

Eeshatullah Goni

Ku dinga hkuri dani pls uxururruka ne suka yi yawa but after gobe in'sha Allah xa ku dinga samun typn ssae.
[5/22, 07:59] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad
Chapter 50 · 0% Book details