← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 89

Sashe 37

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ana gobe Afeefah xa su gama exams tana kwance daki da handout a hannunta tana karatu Sadiya ta shigo tace "wae kije in ji Abba" Afeefah ta mike ta ajiye handout din hannunta snn ta sa hijab ta fita ta nufi falon Abba, su Sumayya ta ji suna yi ma mutum sannu da xuwa a falo, ta karasa stairs ta leka downstairs ta ga yayanmu ne, da gudu ta sauka kasa ta karasa cikin falon ta rungumesa cike da murnar ganinsa don kusan 3 mnth knn bae xo ba, yyi murmushi yace "ya exams Zainab" ta wara ido tace "ae gobe xa mu gama, yayanmu ni wajen ka xan je hutu ba Kaduna ba" yana cire safar kafarsa yace "To Allah sa Mami ta yarda" mikewa yyi yace "naga motar Abba, yana sama?" Zainab tace "ehh" tare suka haura sama da ya Aliyu suka shiga falon Abba, Adnaan ne ya fito daga falon yyi ma ya Aliyu sannu da xuwa snn ya galla ma Afeefah harara yace "baki san ke ake jira ba" turo baki Afeefah tayi ta shiga falon tare da ya Aliyu tana wondering me tayi kuma ake kiranta, Abba na xaune da alamar ita yake jira, Mami ma na xaune a falon ta bi ta da kallo har ta karaso cikin falon ta xauna tana kallon Abba kmr mara gskya tace "Abba gani" xaunawa Aliyu yyi gefen Mami da tayi murmushin ganinsa tace "Ya hanya Ali?" Ya shafa kansa yace "Alhmdllh Mami, ya gidan" tace "Lfya lau, na ma yi xatan se da yamma xaka shigo da kace min kana Nasarawa" Aliyu yace "Nayi tunanin baxan samu Abba bne shi yasa na xo ynxu" se a snn Aliyu ya gaida Abbansa dake ta kallonsa gnin yanda ya rame, Abba yace "Lfya lau, kayi rashin lfya ne?" Girgixa kai Aliyu yyi yace "A'a lfya ta lau Abba" Abba yace "to yyi kyau" juyawa Abba yyi yana kallon Afeefah yace "Dama Zainab da kika je hutu wancan karan Kaduna ce masu kika yi aure kike so?" Juyawa Aliyu yyi yana kallonta, ita kuwa ba karamin faduwa gaban ta yyi ba, tayi shiru tana kallon Abba a tsorace, Mami tace "ba magana ake maki ba" hawaye ne ya cika idonta muryarta na rawa tace "ni bnce ma kowa hka ba" Abba yace "karya xa ki mana knn," fashewa da kuka tayi tace "Abba Allah ni ban ce ma kowa xan yi aure ba" Abba yace "to kin san kuwa Abbanku na Kaduna yana shirin bikin ki da nasu Jamila, jiya da daddare ya bugo min yana min bayani wae kin tsaida miji a Kaduna xuwan ki na kwanaki, ynxu ina son sanin waye mijin, kuma a ina kuka hadu, sannan ina son da bakin ki ynxu ki gaya min irin dokata na gidan nn kafin in sa a xane min ke"

Eeshatullah Goni

[5/22, 07:57] Umar Dalha: ?????? 'Ya mace kyautar Allah??????

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 37 · 0% Book details