← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 89

Sashe 62

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Eeshatullah
Masu shirin bin yayanmu UK suyi magana a masu Visa. Ehe.
[6/29, 06:25] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

77......
Karfe tara Afeefah ta tashi daga bacci, ta dde xaune bakin gado ta rasa takamaiman abinda ya tsaya mata a rae, kawae dae tasan bata da sukuni, ganin tara har da minti goma yasa ta mike ta rage kayan jikinta ta linke su snn ta nufi bayin da ke dakin, wanke baki tayi snn tayi wanka ta dauki brand new farin towel dake bayin ta daura, amma ta kasa fitowa tunawa da tayi bata shigo da hijab ba, tura kofar bayin tayi daga karshe ta fito, da sauri ta nufi kofar dakin don ta kulle amma ko karasawa bata yi ba aka tura kofar dakin, 'yar kara ta saki ta durkushe wajen kmr xata yi kuka, yyi tsaye nn bakin kofar yana kallonta ya girgixa kai yana murmushi, can dae da ta ga ba fita xae yi ba, ta dago kai tayi rau rau da ido sae dae bata bari sun hada ido ba tace "Plss sir ka tafi xan sa kaya" yace "Ok" snn ya juya ya fita ya kullo mata kofar, sae a snn ta mike da sauri ta sa key kofar, cike da jin kunya ta nufi gaban madubi ta xauna tayi shafe shafenta snn ta mike ta fiddo kayan da xa ta sa, cikin mintunan da basu wuce goma ba ta shirya cikin riga da skirt na holland me ruwan ganye da yellow, ba karamin kyau kayan yyi mata ba kuma ko make up bata yi ba amma tayi kyau ssae, ta fiddo hijab dinta fari ta sa, xaune tayi karshen gadonta tayi jigum, ta kusa wani minti goma a hkn ya kwankwasa kofar dakin, ta mike ta nufi kofar ta bude ta juya ta koma, murmushi yyi gnin dogon hijab din jikinta yace "Taso muyi breakfast downstairs," yana fadin hka ya juya, ta mike a hnkli ta bi bayansa kmr me counting steps dinta, a tsakar falo ta same shi yana hada tea, ta xauna dan nesa da shi ya dago kai yana kallonta sae kuma ya ci gaba da abinda yake, ita ya ajiye ma tea'n snn ya hada coffee dinsa, ya bude mata kulolin dake dauke da sinasir, farfesu kala har biyu sae fried potatoes da kwae da plantain, yana kallonta yace "Serve ur sef" yana fadin hka ya mike ya koma kan kujera da cup din coffeensa, har ya gama shan coffeen bae ga ta dibi komae ba sae tea take ta kurba a hnkli, ya ajiye cup din hannunsa yace "ko ni xan dibar maki?" Bae jira amsarta ba ya sakko ya dauki plate ya dibar mata sinasir, ya dauki wani plate ya dibar mata farfesun naman rago snn ya kuma dibar mata potatoe ya ajiye mata gabanta yana kallonta yace "Sun ishe ki?" Sunkuyar da kai tayi bata ce komae ba ya mike ya koma kan kujera. Gnin taki taba komae still yasa ya mike ya bar mata falon gaba daya ya haura sama. Ta dauki sinasir din ta mayar cikin kula har da naman, ta rage potatoes ta bar wnda xata ci. Tana gamawa ta kwashi plates da kulolin ta nufi hanyar da take tunanin kitchen ne, ta kuma tsaftace kitchen din tayi dan wanke wanken dake sink snn ta fito falon nn ma ta dan yi goge goge ta koma sama ta shiga dakinta. Kwanciya tayi tai lamo kan gadonta I xuwa ynxu kam tasan tunanin yayanmu kawae take shi ya hanata sukuni, wasu hawaye suka xubo mata ta kifa kanta kan filo ta shiga rera kuka a hnkli, jin an bude kofar dakin ta yasa ta dago da sauri tana share fuskarta, Karasowa yyi yana kallonta tayi saurin sunkuyar da kai, ya xauna gefen gadon yace "sannu da aiki" turo baki tayi ta kauda kanta, ya langwabar da kai yace "Ki gaya min kukan da kike Zainab baki son auren koh?" Girgixa masa kai kawae tayi, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta yace "To tell me y u re crying" a hnkli tace "Yayanmu" yyi shiru yana kallonta kafin yace "wat abou him?" Ta dago jajayen idonta tana kallonsa tace "He said xae xo ran bikina kuma bn gan shi ba" Dr bae ce komae ba ya shiga share mata hawayen ta, cikin kuka tace "Am missing him" rungumeta yyi, lkci daya ta saida kukanta ta fara kiciniyar kwace kanta, ya ki saketa murya can kasa yace "Ni ba kya missing dina" gnin irin rungumar da yyi mata ya tsoratata ssae, cikin muryar da ba tata ba tace "Plss sir stop this" Hijab din jikinta ya cire da hannu daya ta fashe da kuka tace "Don Allah ka Bari sir ni bna so" murya can kasa yace "Kar ki kuma sa min hijab a gidana" ba kadan ta tsorata ba don gani take kmr ba Dr Sharif din da tasani bane wnn, wanda bae son ko hada hannu da ita a da, turasa tayi da karfi ta mike ta shige bayi ta sa key. Tana jin fitarsa ta fito da sauri ta sa key dakin gaba daya tana share hawayen idonta tayi kwanciyar ta kan gado.
Chapter 62 · 0% Book details