← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 89

Sashe 25

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

34.....
Karasowa cikin dakin Aliyu yyi yana kallonta, Afeefah tuni wayar hannunta ya sulale kan gado ta jawo pillow da sauri ta rufe ganin bae lura ba, tsaye yyi bakin gadon yana kallonta taki dago kanta, yace "Zainab!" Da kyar ta iya bude baki a hnkli ba tare da ta kallesa ba tace "Na'am" xaunawa yyi gefen gadon yace "Ki gaya min meyasa ke kadae ce baki jin mgna ta a gidan nn" Shiru tayi bata komae ba, a tsawace yace "Zainab!" Dago kanta tayi tana kallonsa da idonta da yyi ja, lkci daya hawaye ya cika idonta a hnkli tace "kayi hkuri yayanmu baxan kara ba" rungumeta yyi yace "Sau nawa kike making min wnn promise din kina break din sa Zainab?" Cikin muryar kuka tace "Na daina yayanmu" dago kanta yyi murya can kasa yace "promise?" Kai ta gyada masa tana hawaye, mikewa yyi ya kama hannunta suka fita daga dakin ya nufi nasa da ita. Kwata kwata Afeefah bata saki jiki da shi kmr ynda ta Saba ba ranan, duk sae ta ji ta a takure abinda bae taba faruwa da ita ba suna tare da Ya Aliyu, tsarabar da ya yo mata ma bata wani nuna farin ciki kmr ynda take yi da ba, kawae dae tana xaune dakin ne ta kafa ma plasman dake ta aiki ido, shi kuma yana danna laptop dinsa, gaba daya hnklinta na kan wayarta da ta baro a daki duk ta kagu ta fita, ta rasa dalilin da yasa ta damu da kiran Dr Sharif hka, Sumayya ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon ya Aliyu tace "yayanmu wae Mami tace in kira Afeefah" ba karamin farin ciki Afeefah tayi ba don sae da ta sauke ajiyar xuciya, Mikewa tayi tana kallon ya Aliyu tace "yayanmu na tafi Mami na kirana" kai kawae ya gyada mata ta dauki ledan tsarabar da ya bata ta fita ta nufi dakin Mami, kasan dakin ta xauna tana kallon Mamin tace "gani Mami" Mami tace "kin gama hada kayan naki?" Afeefah ta gyada Mata kai tace "na gama" Mami tace "je kiyi ma Abbanku sallama ynxu, gobe da sassafe Adnaan xae tafi kd sae ki bisa kawae" mikewa Afeefah tayi ta fita ta nufi dakin Abba, yana xaune falonsa yana kallon news, ta xauna kasa, yace "ya aka yi Zainab, yau ba ki yi bacci da wuri ba knn" tayi murmushi tace "eh bnyi ba Abba, dama Mami ce tace in xo in gaya maka gobe xan tafi kd" shiru Abba yyi yana kallonta can yace "toh shknn Allah kai mu, tafi ki kira min ita" mikewa Afeefah tayi ta fita daga falon ta koma dakin Mami tace "Mami Abba yace in kira ki" Mami tace "to jera min kayan nn kafin in dawo" Mami na Kai wa nn ta fita ta nufi dakin mai gidan nata, Kallonta kawae Abba yake har ta xauna snn yace "ynxu dae nuna min kike kin fini iko da Zainab a gidan nn koh Zuwaira?" Mami ta kallesa da mmki tace "kmr ya knn?" Abba yace "wato ke a ganin ki ke ya kamata ki dinga yanke wasu hukucin a kanta knn don Kinga ina maki shiru koh?" Mami tace "don nace xata kaduna shine nayi laifi Alhaji?" Abba yace "sae ana gobe xata tafi ya kamata a gaya min? kuma ma wae sae ki aiko min ita tsabar ki gwada min kin fi ni iko da ita ko me" Mami tace "Allah baka hkuri, kuma don naga Adnaan xae tafi kadunan ne gobe yasa nace kawae ya tafi da ita da su Jiddah, kuma kasan da sassafe yake tafiyarsa ba kmr Aliyu ba." Abba yace "to baxa su yi tafiyar sassafen da shi ba, ae Ali na nn da yamma sae ya Kai su" Mami bata ce komae ba, ya Mike ya shiga dakinsa ya dauko dubu 50 ya mika ma Mami yace "gashi kiyi Masu siyayyar da ya kamata" Mami ta sa hannu ta karba tace "Allah kara budi" snn ta mike ta fita daga dakin. Afeefah na gama gyara ma Mami kayan da ta sa ta ta tafi dakinsu, Jiddah kadae ce tayi bacci, Sadiya kuma na danna wayarta, kan gadonta ta nufa da sauri ta daga pillow ta dauki wayarta ta ga Dr sharif bae kuma kiranta ba, juyawa Afeefah tayi taga Sadiya ba kallonta take ba, kmr munafuka ta shige bayi da wayar, dailing number tayi, yana fara ringing ga katse ya kirata, "Baki yi bacci ba?" Kunya ne ya kamata don ko duba Karfe nawa bata yi ba, da sauri tace "ehh naga mis cal ne" Dr Sharif yace "na kira kin dauka kuma kika yi shiru" tace "uhm yayanmu ne ya kirani" Dr Sharif yace "OK, ya su mama?" A hnkli tace "suna lfya" yace "me kike yi har ynxu ba ki kwanta ba" tace "na hada kayana ne, gobe ya Adnaan xae tafi da ni Kaduna" yace "Really?" Kai ta gyada masa kmr yana ganinta, yace "Ashe xan yi missin crying student dina" murmushi Afeefah tayi murya can kasa tace "ae xan dawo kafin a kare hutu" a hnkli yace "Shknn, journey mercy Dear" shiru tayi jin abinda ya kirata da, "Are yhu there?" Ya tambayeta jin shirun, Da sauri tace "um na ngdd" yace "welcm, sleep sweet!" murmushi tayi ya katse wayar, ta fito daga bayin a sanyaye.
Chapter 25 · 0% Book details