← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 84

Sashe 9

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata nemi kowa ba kai tsaye dakinta ta nufa ta shiga wanka ta hado da alwala ta gabatar fa shafa'i da wutirinta tunda tun a gidan ya ahmad tayi isha,ta dauki kimanin minti goma ta azakar dinta sannan ta ninke sallayar ta sauko qasa ta nufi dakin ummi,ummin ta amsa sallamar bayan ta mata sannu da zuwa ta sanar da ita anty hafiza na gaisheta ummi tace "kinje kenan?"ta gyada kai tace"bayan fitarku ne ummi gidan shiru ba dadi shine nace bari kawai na leqa biyu"har ta bude baki zata mata fadan fita ba tare da ta tambayeta ba sai kuma ta tuna fadilan ba gwanar yawo bace banza bata kai zomo kasuwa,ta tabbatar ba'a banza ta fita ba,dama farida ce to tasan hali,sai kawai tace"ina amsawa"fadila tace "ummi bari na wuce na kwanta na gaji"ta dubeta tace"au yau ba zaki jirayi dawowar abban naki ba?"ta gyada kai"um ummi abincinsa na dining area na parlour dinsa ni dai sai da safe"ta miqe ummi tace"Allah ya tashe mu lpy nima wanka zan shiga ki jamin qofar"tana qoqarin fita taji ummi ta kirayeta ta dawo da baya tana amsawa"bayan fitata wa ya kawo kaya a baqar leda suna nan a parlour?",sai a sannan ta tuna da kayan da aliyu ya aiko a kawo mata,ta sunkuyar da kanta tace"ummi yaya aliyu ne ya kawo to sai na mantasu a parlour"ummi ta gyada kai tace"yayi miki kyau,fadila ki maida hankalinki fa,gidan kishiyafa zaki,ba ke kadai zaki zauna ba ballantana kice zaki dinga abinda ranki keso......ta danyi jim,jin fadila bata ce komai ba ta Dora"sai kije ki debe tun kafin abbanki ya zo ya gani ranki ya baci"ta qarasa maganar tana shigewa bandaki ,jikinta a salube ta fita,ta isa inda ledar take ta dauke ta tayi sama da ita Hannu biyu ta tallafe habarta da su ranta a jagule,yaushe su ummi zasu fahimci tsananin da take ciki?,har ga Allah tana son ali yana burgeta a rayuwarta komai nasa yana bata sha'awa,yau da za'a ce aliyu yana sonta a sai ta fi kowa farinciki,to su su ummi suna tsammanin ita ke son kawo cikas,ta share hawayenta ta daga ledar tana zazzage kayan ciki Bandir ne na 'yan dubu dubu sababbi fil a miqe guda hudu sai chocolate packet hudu manya ,sai turare guda hudu designers,sai awarwaraye banguls da zobensu na gold guda biyu ,sai agogon hannu na azurfa guda biyu shima,komai tsada ne da tsari,cikin zuciyarta take fadin"yadda Aliyu na ke da kyau da tsari haka everything na shi yake,yadda aliyu yake special haka komai daya dangaceshi yake,komai nashi special one ne hakanan abun ban sha'awa ne,ina ma aliyu zai soni?,ina ma Aliyu zai rufeni da da so da qaunarsa da na zamo daya daga cikin mata masu tsananin sa'a a rayuwarsu"hawayen tausayin kanta suka ziraro mata,ta dauki daya daga cikin rapper din kudin tana shinshinawa,ta lumshe idonta don qamshin turarensa kawai ke tashi a jikinsu(haka aliyu yake saboda yadda turare ya zaunar masa a jikinsa duk abi da yayi gogayya da shi sai yayi qamshin turarensa) Farida ta shigo dakin da sallamarta,fadila ta amsa tana janye mata kayan dan faridan ta samu gun zama,cikin tsokana faridanke tambayarta kayan,tace"duba ki gani ya Aliyu ne ya kawo dazun ki zabi abinda kike so(haka ummi ta koyar da su tun suna qanan idan daya ya samu abu to zai raba tare da dan'uwansa )ta yaba kayan sosai ta dauki turare biyu tace sun isheta,fadila tayi tayi da ita ta qara taqi,ta turo mata kudaden gabanta hadi da yage 'yar paper da taga anyi rubutu a jiki kamar haka"kiyi hidimar biki idan basu isa ba zansa a adado miki"tadan tabe baki cikin ranta tace"nafi buqatarka da su da zaka gane hakan""farida ga kudin hidimar bikinan inji aliyu idan basu kai ba a mishi magana"farida ta dauki kudin tana juyawa tace"har dubu dari hudu "fadila tave"hmmm ni da ua ban su nasan mai zanyi ma da su"farida tace"ni da anty hafiza munsan me zamuyi miki da su,ko iya wadannan ma sun isa ya sallameki"ta miqe tana cewa"bari in nunawa ummi,sai da safe sister"ta fita taja mata qofar tana ayyana abubuwan da zasu yiwa fadilan masu amfani Duk cikin satittikan da suka biyo baya cikin hidamar shirye shiryen biki suke,ita kam fadila bata da wani zabi na kanta,da zasu yarda ma da sun qyaleta haka don bata da sha'awar yin komai kama daga gyaran jiki zuwa kan duk wasu events da ake yi yayin bikin aure,don duk abinda zatayi wanda za'ayi don shin abun bai dada shi da qasa ba baya gabansa hakan yasa itama ta tsani komai,sai da anty hafiza ta zaunar da ita ta nuna mata duk abinda tayi idanun duniya na kanta,zata tona asirin kanta da kanta ne sannan ta amince da tsare tsaren da suke zuwar mata da su,hatta magunguna tanajin farida na sha da qyar tana mita ita kam nata ido karba kawai take ta daddake tunda tana ganin babu wani amfani da zasu yi mata To fa masu karatu ga fadila Abbas na shirin shiga gidan Aliyu salim maitama,gidan da aka gargade ta da shigarsa tun kafin ta kai ga shigarsa,shin mene shawararku gareta???? 10:34 pm 07066139278 [10/16, 12:25 PM] Salma Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Ranar laraba 12 ga watan biyu aka soma da kamu ,ba dan qaramin kyau amare sukayi ba,kai kaso kazo kaga yadda kamun ya qawatu matuqa da gaske,an zubar da dukiya sosai kasancewar wannan ne bikin ummi na farko kuma na qarshe,tamakar tagwaye haka suka zama komai iri daya suka sanya hatta da awarwaro da zobe Kasancewar abban su babar bare umminsu bafulatana sai aka raba abun biyu shigar farko sukayi shiga irin ta bare bari cikin wata lafiyayyar lafaya wadda kudinta ya tasamma kimanin dubu ashirin kamu aka musu irin na bare bari sosai sannan daga bisani kuma suka canza shiga irin ta fulani cikin kayan saqi nan ma aka musu kamun fulani,shida na yamma aka tashi bayan sallar magariba kuma masu kidan qwarya suka zauna zuwa goma na dare Irin cikar da gidan yayi yasa su fadila haqura da zaman gidan su da qawayansu suka koma gidan maman zainab maqociyarsu ce kuma babbar macace don idan batayi sa'ar umminsu ba to zata girmemeta,zainab din yarinyarta ce kusan sa'ar farida ce Fadila nabin kowa da ido don a yanzu kam jikinta ya qarasa mutuwa murus,bata da kuzari ko qanqani komai cikin dakiya da qarfafa mata gwiwa da anty hafiza ke mata take yinsa,ga wani ciwon kai da ya addabeta,ta riga ta saba ita ko da can bata saba da shiga hayaniya ba ko bikin dangi ne bata kwana sai dai farida ta kwana ita kam komai dare zata dawo gida ne,ko hayaniya tayi mai yawa to yanzu kanta zai fara ciwo ko qirjinta ya dau zafi Kwance take kan gadon zainab din ta juya ma tarin 'yammatan dake dakin sunata hayaniyarsu baya ta fuskanci fuskar gadon,yawancinsu duk qawayen farida ne sai 'ya'yan 'yan uwa,farida tayi sallama ta shigo dakin ita da aminiyarta ruqayya hannunsu dauke niqi niqi da ledoji na take away wanda aikin mubarak(angon faridan) ne shi yace a tazo suje tayi musu take away,ta zube musu nan hayaniya ta qaru kowacce tana daukar tata,ta iso kan gadon hannunta da ledoji biyu,ta dan taba qafafun fadilan tace"sister tashi"fadila ta miqe daga kwanciyar ta zauna tsakiyar gadon ta tanqwashe qafafunta tana kallon farida,qasa-qasa muryarta tace "yayaa ga abinci ki daure ki ci sai ki sha maganin ciwon kan ko dan idon mutane ida yaso sai ki kwanta ki huta,"tana maganar tana bude ledar da ta shigo da ita din ta tura mata gabanta,ta sake bude dayar ledar tana cewa"ga dinkimmu na dinner din gobe ta can muka biya da mubarak muka maso"ta soma fito da su Wani dan ubansun material ne mai azabar kyau wanda ko makaho ya shafa yasan cewa ba qananan kudade aka sa aka siyeshi ba,milk ne da ja(milk and red),ita kanta faridan da tunda ma anty hafiza ta bawa ya ahmad da zashi india ya siyo musu bata ganshi ba sai yau da aka karbo dinki faridan ce ke zuzutashi sai yau taganshi yayi bala'in tafiya da ita ,ta jinjina kak tace"an gode miki sister farida"farida tayi dariya tace"ai wannan aikin anty hadiza ne ragowan su earings ma da zamu sa suna gunta"fadila tace"Alla ya saka mata da alkhairi"ta jawo ledar da faridan ta bude mata,gasashshiyar kaza ce da hanta wadda aka mata gashi mai ruwa ruwa da albasa,shawarma sai kuma ice cream roba biyu ,tayi murmushi ta kalleta kafin tave komai faridan ta rigata magana"ke dai yaya ki ci kawai,kina tsammanin bansan abinda kime boyewa bane a dan qaramin fridge dun gefan gadonki ba wanda ke hanaki maida hankali kici abinci? "sai dariya ta kama fadila,lokaci guda kuma tausayin rabuwa da junansu da qaunar 'yar uwarta ya kamata,lallai ne dan uwa rabin jiki,naka nakane qwalla ta ziraro mata ita ma faridan sai ga qwallar,dai dai nan rumasa'u(yar qanwar umminsu ce(ta shigo dakin,ganin haka ta saki dariya" a'ah kaga twince sisters wato ku daga fara biki har kun soma gunsheqen kukan rabuwa tun kafin aje ko ina?"yawan hayaniyar da yammatan keyi ya hanasu jin abinda take cewa,farida na dan murmushi ta goge hawayanta,ita kuwa fadila da yake sa'annin juna ne saita harareta"to ina ruwanki 'yar sa ido?"cikin dariya tace" a'ah Allah ya huci xuciyarki bani na kar zomon ba ratayar ma ba'a bani ba ni ummi ce ta turoni tave inzo inga kinci abinci don tasan hali"ta fada tana leqen ledar gaban fadila,fadila ta muwa lanqwashe ledar,tana cewa"kuma duk kwadayin mutum bazaici ba ba?"cikin son zolaya rumasa'u tace"haba aminis ni dake fa bata baci"fadila ta zaro kazar ta nannde mata tace "ungo a banni na hadiyi yawu"tafice tana dariya,farida da tun dazun take ta musu dariya tace"hoo yaya ruma akwai zolaya da abun dariya yanzu fa idan kika bibiya itama bacin zatayi ba baiwa wani zatayi"fadila tayi murmushi tace"ta ji dai Shi dai gundura kawai" Da taimakom farida fadila ta saki jikinta sosai don har ta samu ta shige cikin 'yammatan aka shiga hirar harda ita,hakan ya taimaka mata ta samu sauqin takurar da zuciyarta tayi sosai kafin dare yayi kowa ya kwanta Washegari gidan kwalliya anty hafiza ta debesu suka tafi,cikin wasu awoyi aka qalqale wa kowacce fuskarta da kwalliya
Chapter 9 · 0% Book details