← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 84

Sashe 58

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shirme yake(hhhhhh),da suka sauka ko a ethopia aka basu dakunan kwana kan sai gobe zasu qarasa nijeria jinsa yayi kamar a saka shi a kurkuku,masifa kawai yake yana fadin dole ya sayi private jet nashi,dole yana ji yana gani ya haqura har sai washegarin Qarfe goma na safe a garin kano tayi masa,tuni nasiru yazo da mota don daukarshi,gidansu yace ya wuce da shi kundila maiduguri road,yana shirin fitowadaga cikin motar saiga sumayya ta fito cikin shirin tafiya school,da sauri ta sauya akalar tafiyar tata ta nufo gurin motar fuskarta qunshe da fara'a"sannu da zuwa ya aliyyu" ta fadi tana leqa cikin motar cikin neman fadila,"yauwa" yace yana sanyo qafarsa waje,ya dubeta cikin dakiyar nan tasa "ke,me kika bani ajiya kikemin leqe leqe cikin mota" sai ta dawo ta tsaya dai dai cikin fara'a "anty fadila nake leqe ko zan gani yaya,surprising din mu kuka so yi shi yasa ko a waya bata gaya mana ba,kwananta biyu ma bata kira mu ba ashe kuna hanya"da sauri ta juya tana shirin komawa ciki tace "bari na fara yi mawa momi albishir"sosai jikinsa ya mutu basu da labarin ma ta dawo to me yake faruwa ne?"maida qafar tasa yayi cikin motar ya rufe ya bawa nasiru umarnin ya kunnata su wuce sani mai nagge(unguwar su fadila) Har cikin gidan malam ya bude musu suka shiga,ya fito ya ningina jikin motar bakinshi fal addu'a,yana tunanin yadda zai shiga gidan ne,sai ga muhammad ya fito daga inda suke ajiyar motocinsu hannunsa dauke da qaton almakashi irin na yankan shuka,nasiru ne ya qwala masa kira,da sauri ya juya ganinsu yasa shi nufo gurin yana fara'ar ganin aliyyun,"sannu da zuwa yaya"muhammad ya gaida shi ya amsa masa "kai da anty ne yaushe kuka dawo amma bata gayama ummi zaku dawo ba"ya fadi yana washe baki da son jin amsar inda yayarsa take,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"aliyu ke fada cikin wani irin hali,muhammad ya juya yana fadin "bari nakira abba bai fita ba"aliyu na shirin hana shi saiga abban ya fito ummi na riqe da jakarsa Sosai abban ya nuna jin dadin ganin aliyun,yasa muhammad ya bude sitting room suka shiga,maganar da abban ya qara fadi ita ta sake tabbatarwa da aliyyu fadilan bata zo gidan ba"ina mai kukan tafiya yanzu dai ai kuka ya qare ko tunda gashinan anje lafiya an dawo lpy"aliyun ya sunkuyar da kai wata fargaba na shigarsa "tana lafiya abba" abinda ya iya fada kenan,to shima abban bai takura masa da wata doguwar hira ba ya sallameshi shima ya fice kasuwa Gidansa kawai yasa nasirun ya kai shi don bai san kuma me ya rage masa ba,tunaninsa ya tsaya cak,a harabar gidan ma'aikata ne kowa na masa barka da dawowa,baijin ma me suke fada hannu kawai yake daga musu,ya sallami nasiru ya fito daga cikin motar yana shirin shigewa ciki aka sake dage gate din gidan,tsayawa yayi hadi da juyowa don hajin wanda aka bude mawar,motar samirah ce wadda ta sake cin ubanta,su hudu ne cikin motar,wata dabance ke driving din samirah na gefanta sai wasu su biyun a baya,dariya suke ta sheqawa sam basu ma kula da wani aliyyu ba har suka yo parking,har ta fito tana sheqa dariyarta kamar wadda aka yiwa albishir din ba zata mutu ba,cak ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima ya zuba mata ido,suma qawayen dariyarce ta tsaya cak,sun san halinsa sarai baya da kyau,sum sum daya bayan daya suka fice daga gidan,kai kawai ya gayada ba tare da yace mata komai ko ya sake kallonta ba ya shiga bangaransa Yafi mintin talatin a zaune kafin ya miqe yaje yayi wanka,kafin ya kammala shiryawa anyi kiran sallar azahar,duk wani motsi da zaiyi tana manne cikin ransa,duk wani tunaninsa na ina zai sameta?ina zai ganta?ina kuma yanzu zaije nemanta?,cikin yadin tissue fari tas ya shirya,yayi kyau sosai duk da kana kallonsa zaka karanci bai cikin walwala duk da kusan hakan yanayin fuskarsa yake amma wannan karon ya ninka yadda yake da,ficewa yayi kansa tsaye ba tare da ya nemi kowa ba da kansa ya ja motar ya bar gidan Sai da ya fara tsayawa a masallacin bakin layinsu ya bada faralin sallar azahar dinsa sannan ya wuce,kai tsaye yahaya gusau ya wuce gidan farida,ya dan jima a tsaye a qofar gidan baiga gilmawar kowa ba har yana shirin komawa sai ga dahiru almajirin faridan,da sauri dahirun ya qara so inda aliyyun ke tsaye don ya ganeshi,cikin girmamawa ya gaida aliyyun,ya amsa masa yana tambayarsa matar gidan na ciki?,ya amsa masa da "eh alhaji ko a kira maka ita za'ayi?" "A'ah tambayarka dai nake so nayi"aliyu ya fda yana gyara tsaiwarsa "to..Allah yasa na sani" "tayi wata baquwa tsakanin jiya da shekaran jiya da yau?" "Kai gaskiya a'ah,don suma jiya suka dawo daga lagos ita da mai gidan"ya fada masa cikin bashi tabbaci Idanunsa ya rufe yana jin wani abu sannan ya bude,ya saki qaramar ajiyr zuciya sannan ya ciro kudi ya bama dahirun ,cikin murna ya amshe yana zuba godiya,bai bi ta kan godiyarsa ba ya shige motar ya tasheta ya bar layin Har la'asar aliyyu salim na bulayi bisa titunan kano,shiga wancan fita wancan,ko manshi da yake qonawa bai damu ba,ya rasa inda zai zauna bare yayi tunanin mafita,gaba daya feeling kansa yake a matsayin guilty,cikin rudanin inda ta tafi yake,ina ta boy e kanta haka?,duk da yana ji daga can cikin wani sashe na zuciyarsa na gaya masa she is safe and she is in safety place Sai da ya soma ganin gurare daban daban na ta alwalar sallar la'asar sannan ya samu ya kashe motar a bakin wani masallaci ,ya daura alwalar ya bi jam'i,sai bayan da ua idar ne yaji cikinsa na qugi sannan ya tuna rabonsa da abinci har ya mance,ya miqe ya koma cikin motar tasa ba tare da yabi ta kan yunwar dake sakadarshi ba,sai da akayi sallar magariba yana bilayin yawon titina sannan ya gano cewa wannan fa ba mafita bace,tunanin matsalar itace zata samar masa mafita da gano masa inda fadilan ta boye,ya juya akalar motarsa ya nufi gidansu dake kundila. ....... *mrs muhammad ce* [10/16, 2:09 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* Yana shiga ya tadda rabi'ah kan dining area ita da iftihal momy na kitchen,da alamu su din ma zaman na cin abinci ne,da gudu iftihal ta gangaro tana ihu "yeyyyyyy daddyyyy"kamar yadda ta saba ta duqa ta gaidashi,ya amsa mata maimakon ya dauketa ya shilla sama yadda suka saba wannan karon sai taga kawai ya shafa saman kanta yayi hanyar kitchen din,ta tabe baki kamar zata saki kuka Tana kiciniyar rufe warmer taji an rufe freezer,ta dago kai da sauri aliyyun na tsaye yana daddakar ruwan mai azabar sanyi,sai da ya shanye robar guda momin na kallonsa ta zuba mai ido,ganinsa take a wani birkice duk da jikinsa fes yake kuma ya yi kyau da 'yar cika(sakamakon kulawar da ya dinga samu a china)amma abunka da mahaifiya kallo daya tayi masa t gano akwai damuwa a ransa Yana qare shanyewar suka hada ido da momin,sai ya kautar da kai ya sanya robar cikin dust bin yana cewa "momi barka da dare ina wuni"bata dai daina kallon nasa ba tace "lafiya lau Ali kun dawo lafiya?" "Lafiya qalau ha fada yana jan kujerar plastic dake kitchen din zai zauna "mun sameku lafiya?" Ya sake tambayar momin yana dauke kai don baya son irin kallon nan na momi,nan da nan take naqaltar mutum,itama sai ta dauke kan tana ci gaba da rufe warmer din tace"lafiya lau,tun safe sumayya tace min gaka,shiru shiru baka shigo ba ko da aka leqo kuma ba kai a gun"ta qarashe maganar idanunta a kansa kamar tana son jin amsa kenan Ya basar da zancan ta hanyar cewa"rabu da wannan shirmammiyar yarinyar momi,makaramta fa zata tafi amma don gulma ta koma,gida muka qarasa kawai"ta dire warmer din tana cewa"ina 'yata fadila" gabansa sai da ya buga "lafiya"kawai ya iya furtawa tare da miqewa don kada ta sunkuto masa wata tambayar da zai gagara kubutar da kansa,ta waiwayo tana cewa "a'ah ina zuwa kuma?" "Zan wuce gida ne momi" "baku gaisa da abban naka ba,yana gida fa,kuma ma na zaci tare zamuyi dinner ko?" Abinda momi bata sank ba bazai iya jiran abban nasa ba don gani yake kallo daya zai masa ya karanto abinda ke faruwa,karo na farko da aliyyun yayi ma momin qarya a rayuwarsa "Zani gida ne momi za muyi magana da mukhtar,na baroshi ne da mutane a can wadanda ban sallamesu ba na taho" to da yake ma qaryar bata karbeshi ba sai ya jada harda subul da baka ba tare da ya ankara ba "ya zaka dawo bayan baka sallami baqi ba ali?,wai meke damunka ne haka?,a kunnena fa abbanka ya tursasaka zuwa bikin bude kamfani,yanzu kuma ka taho ka bar jama'a acan,baqonka annabinka fa ali"yayi saurin dosar qofar fita yana cewa"momi ai ba matsala mukhtar zaiyi komai kamar ina nan,sai da safe momi idan abban ya sauko ki gaida shi ina hanya goben"baki sake ta bishi da kallo tana ayyanawa tabbas akwai abinda ke damun yaron nan,gashi da shegen zurfin ciki kamar mace,idan kaji cikinsa to ya ciyoshi ne,ta dan daga murya tana cewa"ka gaida mutan gidan" "zasu ji momi" ya fadi yana barin falon cikin sauri don kada suci karo da iftihal ta tsaida shi Har ya koma ya bude sashensa ya shiga yayi wanka ba wadda ya gani,shi yama fi son haka din ma,yasa koda sunzo babu abinda.zai samu sai qarin tension,shi kuma yanzu abinda ke damunsa yasha kansa fiye da komai,sai da dibi kusan awa daya da wani abu sai ga salima,fuskarsa ta zubawa ido tana murmushi saboda sosai aliyyu ya canza,ya qara ja sumarsa ta sake baqi sidik,gargasar jikinsa kamar an dada mata baqi laushi da yawa,ya sake kyau,badon fadila da ta hargitsa masa lissafinsa ba da abun yafi haka,hakanan shima ya sakar muta fuska don ya zama dole haqqinsu ne don bazaya yiwu haqqin wani ya danne na wani ba,kuma matsalarsa yasan ba tasu bace indai ta wannan bangaren ne Da sauri ta qaraso ta zube ajikinsa tana fadin "oyoyo welcome my dear"yadan karata ajikinsa yace "thank you ya muka sameku?" "We are fine but I miss you" yadan saki fara'a "ok,to ai yanzu gani
Chapter 58 · 0% Book details