← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 84

Sashe 61

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kanta qaunar aliyyu tayi mata illar wadda take huduwa tun daga zuciyarta har zuwa idanunta da bakinta,bata da abunyi anty hauwa ta sani wani daci ne da fadilan ta dade tana guntsa taje fesarwa idan ta hanata kuma bata yi mata adalci ba,tasan cewa kokwanto ne yasa fadila fadin wadannan maganganun amma ba har cikin zuciyarta bane,ta kuma gama gasgatawa wani irin salon rikicin soyayya ne ya kunno kai kawai tsakaninta da aliyyun,sanoda haka sai kawai tave mata "shikenan fadila kici gaba da addu'o'inki ki yi ta istihara,Allah ya zaba abinda yafi alkhairi" Har anty hauwan ta kai bakin qofa fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"am sorry anty idan maganganuna sun bata miki rai" murmushi ta saki "don't mind,banji komai ba araina fadila" murmuahi itama tayi mata tace "na gode" haka Allah yayi fadila bata aon bacin rai ko yashin hakai ko kadan kamar yadda bata son taa ta batawa wani rai ko ta shiga haqqinsa Kwana biyu yama cikin wannan hali,duk wasu harkokinsa na gida dana waje yaqi maida hankali kan kowanne,daga qarshe dai kasa jurewa yayi gani yake kamar su suka boye masa fadila,yana ganin da wani yashin hankalin gwara wani,da ya rasata gwara a yanke masa duk wani hukunci da za'a yanke masa idan yaso su bashi ita,ya gaza jure kewarta komai nasa ya yi missing dinta, Tsakiyat uncle abba da momi ya zauna ya warware masu abinda ke faruwa kamar yadda halayyarsa take fadin gaskiya,momin ce ta saki salati mai nauyi yayin da uncle abba yayi shiru gami da yin tsai da ransa,sai a lokacin ne kuma hankalinsa ya soma tashi momi tayi shiru ne tana jiran jin umarni ko me mijin natazaya fada?,yayin da uncle abba ya rasa me ma zaya ce din?,sama da minti biyar kafin ya dago yace "tashi kaje aliyyu" cikin firgici ya dago kai yana kallon uncle abban,ya sake maimaita masa"ka tashi kaje nace mu zamu nemota" alhaji yaje fa kace?" Momi ta fada cikin fushi,a nutse uncle abba ya kalleta "to maimunatu mai zai zauna yayi min?,yaje kawai tunda ya gama nasa aikin ko,mu kuma ba sai muyi namu ba?" Tasan sarai halin mijin nata saboda haka ta gamsu da abinda yace "gaskiyane"shi kam aliyyu yadda bai tanka ba sabida rudani haka ya kasa tashi kansa na sunkuye jinsa yake kamar wani mutum mutumi,har sai da uncle abban ya gaji da ce masa ya tashi shi da momin suka taahi suka bar masa falon Da azahar momi ta dauki wayarta ta kira anty hauwa kamar yadda uncle abba ya ce ta ce mata yana son ganinta ko zuwa najima ne,sai kuwa aka taki sa'a suna cikin gaisawa kausar ta soma qwala kiran "anty fadilah!anty fadila!!na kasa daukowa"nama ne tace ta ciro mata cikin fridge sunce suna son dambun nama to naman ya riga yayi qanqara,tuni momin ta tsaya da amsa gaisuwar "maijidda wace fadilance a gidanki?" Cikin son boye boye tace "am ....fadila ce ta zo mu gaisa,dazun aliyun ya sauketa" "mu kuma dazu aliyyun ya bar nan yana cigiyar ta ba"momi ta katseta "aljanu ke miki wasa da hankali ko gida biyu su aliyun suka rabu?" "A'ah momi ai" "kinga dakata shi aliyun ya riga da ya sanar da babaku komai da kansa,dama maganar da na kira ki kenan akai,saboda haka idan anyi magariba ki dauko ta kuzo" Hawaye bibbiyu fadilan keyi"anty me yasa kika sanar musu anty,munyi alqwari dake anty,me yasa suka sani?" "Fadila aliyyu da kansa yakai kansa gun abba,momi kuma ta san kina gidan nan dazun da kausar ke qwala miki kira" "me yasa aliyyu zai min haka?,don me yasa zaije ga uncle abba?,me yasa baiyi sakin cikin rufin asiri ba?,so yake kowa sai ya ga laifinshi kenan?"sai lokacin tayi dana sani,tayi data sanin da ta fito tun ranar da yazo gida anty hauwan ya bata takardarta ba tare da kowa yaji ko ya gani ba,suna sake doso unguwar bugun zuciyarta na daduwa,tabbas da kafin su yi nisa naty hauwan ta gaya mata inda zasu babu shakka ba zata ba sauka zatayi,gaba daya jikinta rawa yaje ta kasa nutsuwa sai da anty hauwan ta riqeta sannan ta iya shiga falon......... *mrs muhammad ce* [10/16, 2:11 PM] Salma *WA YASAN GOBE?....* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* Umminta ta gani da mominta zaune kujera daya,uncle abba da abban nata kuma na kujera daya,sai iftihal dake zaune dare dare kan cinyar abban nata,duk kansu suka amsa sallamar,sosai taji dadi cikin ranta don rabon da tasa iyayen nata a ido har ta manta,sai dai hararar da ummin nata ta watsa mata ita ta sagar mata da gwiwa,anty hauwa ce ta fara gaida su sannan itama ta gaidasun,sama sama ummin ta amsa mata don har gwara abbanta,cikin salubewar jiki ta koma gefan kujera ta rakabe Aliyyu ne ya shigo cikin sallama yana sanye da shadda dinkin tazarce kansa babu hula,da gudu iftihal tayo gurinsa,hannunta kawai ya iya riqewa bayan da ta gaidashi,gaida su yake saidai abba da umminta ne kawai suka amsa masa,yana shirin samun guri ya zauna uncle abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa "kai....dakata ba zama na kiraka kayi ba...ungo nan" ya miqa masa farar takarda da abun rubutu "rubutawa yarinya sakinta tunda Allah yasa mun ganta" da sauri ya daga kai ya soma rarraba ido cikin filin falon yana neman inda fadilan take,can ya hangota a takure a gefan kujera kanta a qas Gaba daya idanunsa suka rufe,tuni ya manta da cewa akwai wasu wai iyayensa a falon ya durfafeta,idanunsa qir bisa kansa,wani shauqi mai cakude da matsananciyar qaunarta yake fisgarshi,sai da yaje daf da ita uncle abba ya daka masa tsawa wadda ta sashi dawowa cikin hayyacinsa "qaniyarka nace dawo nan" inji uncle abba yana masa nuni da gabansa inda zai zauna din bayan daquwar da ya watsa masa,a salube ya nufi gun yana tafiya yana waiwayen fadilan da kanta ke qasa idonta na digar hawaye,takardar ya sake miqa masa "ungo nan rubuta" sai a lokacin abban fadila yayi magana "haba alhaji bai kamata ba,ya za'ayi yaro da matarsa kuma yana son abarsa a tilasta masa saki,abinda ya faru ai ya riga ya faru,kuskurene kuma babu wanda baya yi,kuma ni idan banda shirmen quruciya irin na fadilan ma banga abun da yayi zafi haka ba,tunda kuma alhamdulillah ya gane sai muyi addu'ar Allah yaci gaba da hada kansu" "Wa?wannan?"uncle abban ya fada yana nuna aliyu da yatsa, "ai bai isa ba tunda tafiso ya saketa sai ya saketa,ai zaluncin ma alhaji yayi yawa,mun zaba mata miji ba tare da jin ta bakinta ba ko musa mana bata yi ba ta karba harda godiya tayiana biyayya,taje ta zauna da shi zuciya daya amma ya dinga azabtar da ita,babu kuma wanda ya taba sani ko sau daya sama da shekara guda har da kusan rabi,kuma yanzu don bamu da adalci tace bata da buqatar zama sai mu tilasta?don me?,mu zamu yi mata zaman auren?," sai lokacin itama ummi ta tanka "to alhaji tunda ya gane kuskurensa don Allah sai abar maganar,ke fadila wallahi tallahi na kuma jin kin furta mijinki ya sake ki ko mai ya hada ku kuwa sai....." "a'ah hajiya,ya kuke neman daure ma yaro qarqashi ne?" Inji momi" "barsu indai baso suke su nanamin su suka haifi fadila ba"inji uncle abba Cikin sauri hajiya amina(ummi) tace cikin girgiza kai "Allah ya kiyaye alhaji Allah ya sawwaqe,haba haba da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne"ya dauke kansa ya maida kan aliyyu "saketa nace ko?"ya nuna shi da yatsa "kuma don ubanka" (aliyyu bai yaba jin yayi zagi ba ko da wasa sai ranar "a gidan nan zata ci gaba da zama ni ne dai ubanta "qasa yayi da kansa yaqi furta uffan,babban abunda yasa jikinsu yayi sayi ganin hawaye nabin fuskar aly,mutumin da komai tsanani ba zaka ga koda qwalla bane bisa fuskarsa yau shi ke kuka saboda mace?,anty hauwa kamar ta tayi haka take ji don dai kawai zancan manya ne kuma basj bata damar shiga ba,sauqinta daya ma iftihal tayi bacci kan cinyar ummi "Abba wallahi ko wuqa zaku sa ku dinga yankan naman jiki na bazan iya sakin ta ba,kuyi min afuwa abba" abban fadila ya dubi uncle abban "don Allah salim a naci albarkacin amintaka ina mai baka haquri kan ka sassauta fushinka kan yarona"falon ya dauki shiru na wasu lokuta kamin abban ya saki ajiyar zuciya "naji...naji,abu na farko da zan fara fada shine alhj abbas kai da hajiya amina ku yimin alqawarin babu wanda acikinku zai tursasawa fadila koda ta bayan fage ne kan sai ta koma gidanta ba tare da ita ta yanke hakan ba?" Ba yadda alh salim ya iya don yana tausayama aliyun yace "nayi" ummi ce tayi shiru har sai da hajiya maimuna tace "baki ce komai ba" "nima nayi"itama ta fadi ci ke da tausayin aliyu "Abu na biyu,anan gidan fadila zata zauna har sai taji ta amince don radin kanta zata koma,idan yaso naga mara kunyar da zai koreta don ba gidansa bane haka nan ba da qwandalarsa na hada na gina gidana ba"ya fadi yana muzurai,sarai aliyun ya sani da shi abban yake amma sai ya sunkuyar da kansa,saboda shi kam a yanzu kome zasu fadi yaji ya gani kuma ya yarda suyita fadin,ko bulala dukkansu zasu dauka suyita zabgarsa yaji ya amince zai kuma shanye tunda dak an janye batun saki cikin lamarin,uncle abba ya nuna shi da yatsa "saura kuma naga qafarka inda take bare kace zakayi yunqurin takurawa ko tursasa mata sai na saba maka fiye da tsammaninka,tashi ka bawa mutane guri mutumin banza kawai",bashi da zabi illa barin falom kamar yadda abban ya umarcesu ya miqe ya fita bayan ya duqa yace "na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma,Allah kumabya huci zuciyoyinku"yana tafiya yana satar kallonta har yanzu kanta na duqe taqi ma ta dago ya kalli koda fuskarta ne Sosai uncle abba bayanin dalilin yin wannan hukuncin bayan ya sallami fadilan da anty hauwan,yana sone koda aliyun yayi nadama ya sake sanin darajarta da amfaninta a gunsa kafin ta koma masa,cikin dariya abban ke cewa"haba alhaji ai ba sai kace komai ba,amma dai don Allah a sassautawa yarona haka"dariya duk sukayi,daki aka bawa fadilan kusa da nasu sumayya,amma tace tafiso ta zauna cikin su sumayya,a daren aka
Chapter 61 · 0% Book details