Sashe 44
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani tsoro da ya kamata,ta qanqame belt din dake hannunta wadda ta kasa daurawa jin jirgin na niyyar dawowa qasa ya tarwatse da su lol har naga idon masu karatu aliyyu salim mai tama da fadila zasu mutu Ta qanqame belt din dake hannunta jin tana niyyar subucewa daga kan sit din ta,cikin zafin nama aliyyu ya kareta da hannunsa sannan ya amshe belt din ya zagayeta da hannayensa ya daura mata hadi da cewa "silly girl" ya gama ya koma kan danne dannen da yake kan laptop abinsa ba tare da ya sake dubanta ba,a dan sace ta harareshi gami da jan dan siririn tsaki ,ya juyo da sauri don tsakin kunnuwansa sukaji kamar tayin da azama ta dauke kanta ta maida window Allah ya taimaketa basu hada ido ba sai ta waske Tafiya ce ta awa hudu ta saukesu a *ethopia* don musayar jirgi cikin babban birnin na *ethopia* wato *addis ababa*,ba kwana zasuyi ba amma saida aliyyu ya kama one room apartment cikin hotel din dake kusa da airport din,tamakar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta nemi gefan kujera qwaya daya dake cikin dakin ta zauna a takure,sallar magariba da isha'in da bata yi bane ke damunta amma duk a takure take bare tayi azamar tashi Tana kallo ya dora jakarsa kan gado ya tube takalminsa da socks dinsa ya shige toilet,motsin ruwan da ta ji yasa ta raya alwala yakeyi Kusan minti arba'in ya fito sanye da rigar towel mai budadden qirji ,kallo daya ta masa ta dauke kai tsigar jikinta na tashi ,gashine kwance luf a qirjinsa baqi sidik tamakar wanda ake sawa relaxer kamar yadda na hannayensa da qafafunsa suka kwanta saboda ruwan da suka sha,ta sake runtse ido gabanta na dan faduwa da alamu ma shi ko ajikinsa don goge sumar kansa yake da dan qaramin towel dake riqe a hannunsa Ganin ya soma kunce dan zaren da ya taimaka wa rigar ta rufe jikinsa ya sata yin azamar afkawa toilet,ta dade numfashinta na kaiwa da kawowa wani abu na mata yawo a jiki sannan ta iya daura alwalar ta fito,ta cimmasa tuni ya har ya tayar da tasa ta koma gefe ta kalli inda taga ya kalla ta tayar da alama nan ne alqibla har ta kammala tata ta zauna tana lazumi lokaci lokaci tana satar kallonsa har ya sallame Shirye yake a yanzun cikin jacket masu kalar green da black sabanin dazu da yake sanye da suit baqaqe kullum aliyyu cikin sa kaya yake sabanin wadanda ta sanshi da su,kusan ma zata ce bata taba ganinsa yayi maimaice ba,yana zaune saman qafafunsa ya kammala addu'arsa ya shafa ya miqe tayi saurin yin qasa da kanta don kada su hada ido tana yiwa Allah tasbihi saboda kyawun da taga yayi mata har ya juya ya fice Fitarsa ba dadewa daya daga cikin ma'aikatan hotel din yayi knocking ya shigo mata da abinci fried spaghetti ce da roosted chicken sai drink da ruwan gora mai sanyi duk da cewa akwai su cikin fridge dake dakin,babu abijda ta iya ci sai lemon da ta sha Saman kujera ta nade ta janyo wayarta ta kunnata wadda tun shigarsu jirgi ta kashe,babu service da ya hau saboda ya fita daga inda yake da amfani ,ta danna power off ta kashe don bata da wani amfani ta maida kanta ta kwantar a hannun kujerar A hanzarce ya shigo ya dauki jakarsa ya juya yana cewa "let's go"ta miqe ita ma ta dauki tata ta bi bayansa *_CHINA (SIN)_* *_guangzhou airport_* Qarfe hudu na yamma da minti ashirin a agogon qasar china qarfe sha daya da minti ashirin agogon Nigeria suka sauka a qasar,iyakar gajiya fadila ta yita,tafiya ce ba kadan ba tamkar ta yada shege zama ne na awanni kimanin goma sha biyar a jirgin wadda bata taba tafiya makamanciyar ta ba Da qyar take daga qafarta da tayi mata taruwar jini saboda tsabar zama,suka sake bin layin screening immigration suka karbi passport suka kuma duba visa dinsu don tabbatar da cewa sun samu izinin shigowa qasar tasu,bayan sun tabbatar da ingancinta suka buga musu stamp suka wuce Sauran kadan aliyyun ya bace mata saboda ta lura cike yake da kuzarinsa tafiyarsa yake kamar baiyi wata doguwar tafiya ba bisa dukkan alamu ya saba da irin wannan tafiyar,motar ce mai azqbar kyau da daukan hankali tayi parking gabansu mutum uku ne suka fito dukkaninsu sanye da coart baqaqe baqin space da baqin sau ciki ,cikin girmamawa suka iso inda aliyyu yake biyu daga ciki suka miqa masa hannu sukayi musabaha,cikin harshen nasara suka fara gaisawa dayan dake gefe ya dauki akwatinansu ya sanya a bayan motar Bayan ya ruge boot suka dunguna gun motar fadila ta bisu a baya,ita da shi na sit din tsakiya biyun kuma na sit din can bayan driver din kuma ya shiga mazauninsa ya tada motar,hira suke abinsu da aliyyu yayin da hankalin fadila ya kasu biyu,daya ta dora shi ne bisa ga aliyyu yadda yake turanci kai sai ka ranyse [10/16, 1:52 PM] Salma *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* Yayin da hankalin fadila ya rabu gida,daya ta dorashi ne kan yadda aliyyu ke turanci kai ka rantse da Allah cikakken buture ne gaba da baya,babu tuntuben harshe ko kuskure ko qanqani,daya kuma ya tafine kan kyawu tsari gami da tsaftar garin ,garine mai azabar kyau da tsari,yanayin gine ginensu sun burgeta matuqa da gaske,saidai abu na farko da ya daga mata hankali dan banzan sanyin da suka tarar ana danawa a garin ,taji daya daga cikin yan chinan na sanar da aliyyu yanzu ma aka shiga cikinsa wanda irin wannan sanyin a Nigeria shine wucewar jaurarmu A hankali motar taci gaba da kutsawa cikin cikin kyakkyawan shimfidedan titin har suka shigo cikin wata kyakkyawar unguwa mai tsafta da tsari wanda tafiyar fadila tsakanin airport da inda suke yanzun ta fuskanci haka unguwanninsu suke,basu yi wani nisa a layukan da suke wucewa ba suka sa signal suka gangara wani layi,sun kusa kaiwa qarshen layin driver ya faka qofar wani dan kyakkyawan gida dake yanyame da shukoki daga gaban gidan kuma grass carfet ne to kusan ko wanne gida dake layin haka yake left to right Driver din ne ya fito ya bude musu qofa sannan ya bude boot din ya fitar da kayansu,Aliyyu ya ciro keys daga aljihun cikin rigar suit dinsa ya miqa masa ya sa hannu ya karba ya nufi gidan ya bude,ya shigar da kayan sannan daga bisani shima ya shiga Tun fadila na tsaye har ta gaza jure tsaiwar ta maida bayanta ta jingina jikin wata 'yar bishiya dake dashe a gun,shi kam tsaye suke qyam jikin motar shida lukas da andi suna ci gaba da hirar kasuwancinsu cikin harshen nasara,jifa jifa tana tsintar wani abu wani abun kuma ya kuce mata idan tunani ya rinjayeta,tsayuwar awa guda cif sannan ya fito ya qarasa shigar da ragowar kayan da bai dauka ba ya kaisu ciki,ya dawo cikin girmamawa ya ya miqawa aliyyu maqullan ya karba yana tambayarsa "have you finished?" Ya gyada kai gami da cewa "yes sir everything is ready"ya girgiza kai yana cewa "well done"ya juya gunsu andi da lukas ya basu hannu sukayi musabaha gami da sallama ya juya ya nufi cikin gidan su kuma suka shige motar driver ya jasu suka bar gun a kasalance ta rufa masa baya zuwa cikin gidan Falone wanda ba za'a kirashi qato can ba hakanan ba zaka kirashi da qarami ba,saidai yadda ya tsaru dole ya qayatar da kai ta yadda zaka iya fin sha'awarsa ma fiye da wani qaton,kujeru ne set guda yan madaidaita masu azabar kyau sai labulaye na alfarma da suka kewaye falon ta yadda baka iya bambance ina qofa take center carfet center table da wasu yan qanana dake maqale tsakanin kujera da kujera tafkekiyar plasma TV da home theater dining area mai dauke da dining table mai kujeru hudu komai na falon fari ne tas sai wasu abubuwan masu sirkin baqi kadan,qofofine hudu cikim falon daya kitchen ne sai store sai public toilet sai bedroom,komai tsaf yake kuma qal qal ta tsammaci hakan dama idan tayi la'akari da dan karen son tsafta irin na aliyyu Fadila ta zabi daya faga cikin kujerun tayi saurin zama saboda yadda take jin gajiya na nuqurqusarta har cikin qashi ji take tamkar ba zata iya daga koda yatsanta ba,tana nan takure kan kujerar tana satar kallonsa,gaba daya sanyin garin ya soma takura ta tun yanzun,ga bashin sallah dake damunta tunaninta daya ta ina zata soma iya taba ruwa da wannan azababben sanyin? Key yasa ya bude dukkanin qofofin ya tura daya wadda a samanta aka rubuta da wani dan siririn katako mai kyau *bedroom* ya shige,ta miqe itama a gajiye ta shiga public toilet cikin sa'a ta tadda a kwai heater kunna ta tayi ruwan ya dan yi zafi sannan ta kunna famfo na zafin da na sanyin ta saisaita su yadda zai mata dadin alwala,falon ta dawo saidai bata san ina ne gabas ba don haka ta kintaci inda taji hankalinta ya fi karkata ta tada salla Minti goma ta kammala magrib da isha'i har ma da shafa'i da wutirinta,batabar kan carfet din ba tana duqunqune cikin hijabinta wanda dama yana cikin jakar hannunta haka al'adarta yake ko ba zata sanya hijabi ba to bata rabo da shi cikin jakar ta,a hankali tana duqunqunen idanunta suka soma mata nauyi da radadin bacci tamkar an watsa mata tsakuyoyi a cikinsu gajiya da bacci suka yi mata tarom dangi suka murqusheta bata san sanda ta bingire da bacci ba agun Cikin sabon shiri yq fito yana sanye da jibgegiyat rigar sanyi mai gashin dabba daga ciki trouser ne da long sleeve shirt duka baqaqe kansa hular sanyi ce ta gashi mai azabar kyau qafafunsa boot ne mai dan tsawo ya sanyawa hannayensa safofin hannu ya saye idanunsa cikin gilashin nan nasa na ko yaushe cikin hanzari ya fito da niyyar fita don sama musu abinda zasu ci idanunsa ya sauka kanta tsakiyar centre carfet din dake tsakiyar falon ta cure guri guda Ya san sanyin garin ne ya soma addabarta shi kansa da ya saba zuwa abroad cikin irin wannan yanayin wannan karon sanyin ya dameshi balle ita da bai