← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 84

Sashe 29

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

indai ta bangaren qalqale jiki ne salima ta iya wannnan kam,yanzun ma ashirye take cikin dinkin lace baqine mai adon ja,ya sauke biron dake hannunsa Mrs muhammad ce [10/16, 12:42 PM] Salma *wa yasan gobe?*....... *written by safiyya Abdullahi musa huguma* Ya sauke biron dake hannunsa yana dan binta da kallo,tayi masa kyau sosai,fuskar sa ta dan sassauta daga dauretan da yayi ganin yadda take masa murmushi ,gefansa ta zauna cikin salon kissa take cewa"barkanka da warhaka ranka ya dade"yadan janyota jikinsa yana cewa "barka kadai......sai yanzu aka ga damar zuwa yimin sannu da zuwan?"ta san tabe baki tace"girki na ne da zan taho daga dawowarka?" "Ko ba girkin ki bane ni ba mijinki bane?" "To ayi haquri ko" yace "ya wuce"ya maida kansa kan aikinsa tana tayashi da hira jifa jifa yana amsa mata Samira ce ta shigo wannan karan harda sallama,abun arziqin nata yau yana da yawa don ba'ayi wari da.wari ba riga da zani ta saka na atamfa,kanta tsaye ta zauna daf da shi tana mata sannu da zuwa ba tare da ta nuna ma ta san da zaman salima ba agun,ya dan saki fuska bayan ya ja yatsun hannunta da nashi zara zaran yatsun yace"bana amsawa tunda kema sai yanzu" "bana shishshigi ne sweet kuma bana son maiyi shi yasa"ya dade da haddace wannnan kalma daga bakin samiran,don haka ya mele baki gefe sannan yace"lallaikam,da kun bani babies ai da sai nace kusha zamanku ni kuma insha hira da yara na ko?" "Nikam ai na riga nabada tawa baby din"cewar salima"no she is belongs to momy,u already know...sabuwa nake so"cikin shagwaba ta dan bata rai sannan tace"haihuwa is not easy dear"samira sai ta tabe baki hadi da cewa"mukam ai ba yanzu ba,tunda sauran quruciyata "aliyyu ya jawo ragowar takardunsa yaci gab da rubuce rubucensa ,kowacce yasan inda tasa gaba dama salima d tasu ai tun shekarun baya,shikam idan da abunda ya rage masa yanzu shine tara family babba Cikin kwanaki n fadika ta watsar da duk wata harka data danganci aliyun ta koma rayuwarta irin ta da,idan gari ya waye tayi ayyukanta na gida ta fice office sai ta dawo tan dawowa ta shige to sai washegari idan ta gaji sai fa kira farida ummi ko anty hafiza su sha hirarsu,ko muhammad yazo mata su wuni tare abinsu Gaba dayan bangaren ya fita daga ran aliyyun saboda tsabar kacamewar da yayi,ko ina ba kyawun gani a hargitse,ranar da salima ta fita daga girki yaga tana shirin kulle sashen ta wuce nata sashen,cikin takaici ya kalleta ganin bata da niyyar kawar da ko cup din da ta hada masa tea bare akai ga batun gyara "jimana!" Yace da ita a zafafe ta dawo tace gani"bai ko kalleta ba ya daga intercom ya kira sashen samira ,sai da ta qara wasu mintina kana ta iso hakan ya sake hassala shi,ya dubesu cikin bacin rai yace "Anya kuwa ky mata ne cikakku?ba ko wani jinsin bane ku?"a mamakance suka dago suna kallonsa,"kamar ya?"inji samira,da hannunsa ya soma yi musu nuni da falon suna binsa su kuma da kallo,"ku duba....dubi......haka ya kamata ace ya kasance?haka sauran mata suke barin turakar mazajensu?....abun naku ba ya yi yawa na lira ba hankali a ciki,ba tsafta ba iya kula da miji?kuma ni kuna son kyautatawa daga gareni?....it cant abun yayi yawa na gaji da tolerating bad attitude dinku.... as from today ya zama dole a kanku kowacce kafin ta bar nan ta tabbatar ta gyara duk inda ya kamata ba ruwana da qazantarku ruwanku ne ku gyara naku ko ku barshi haka is not my own business..... Ya suri briefcase dinsa ya fice,da kanshi yau zaiyi driving kasancewar nasiru baya nan ya tafi ganin gida ,ya juya kan motar ya danne horn yana jira a bude masa,ta kalli gilashin mudubin dake gefansa da niyyar gyara zamansa don ganin wanda kebin bayansa sai yaga wata motan na jira ya fita itama ta fita,ya duba sosai sai ya hangota zaune hannun ta saman sitiyarin fuskarta tayi fresh cikin safiyar,agogon dake daure a tsintsiyar hannunta take kallo da alama ta kusa maka rane don sai yatsina fuskarta take,material ne ajikintan yellow mai adon coffee,ba makeup ko kadan a fuskarta banda powder data shafawa soft chocolate skin dinta,sai lips balm data shafawa lips dinta sirara masu taushi,tayi lullubinta na mutunci har saman ka,ya dan tabe baki ya dauke kai itakam bata san ma yana yi ba,duk da ta ganshin Ayimin afuwa kasancewar yau ina da uziri irin wanda ke kama ko wanne irin dan adam na turo muku shi late kuma ba yawa amma zamu hadu insha Allah,ina godiya a gareku Mrs muhammad ce [10/16, 12:42 PM] Salma *wa yasan gobe?......* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* Fisgar motar yayi ya ficee daga gidan sannu sannu take binsa a baya har suka bar cikin layin suka hau babban titi,yana hangota ta qarawa motar gudu tayi over taking nasa ta wuce shi ba tara da ta dubi koda sashen sa ba,ya daga idanunsa yabi motar da kallo yana dan gyada kai cike da mamaki da jin izza shi zata nuna wa iyawa da qwarewar sarrafa mota?,yaushe ma ta fara kama sitiyarin Wani girman kai ne ya kamashi,ya qarawa motar shi speed cike da qwarewa da gwaninta shima ya mata over taking,ta lura sarai da shi amma sai ka rantse da Allah batasan da wanzuwarsa akan titin ba,ta dan cije lebenta sannan ta dan daki saman sitiyarinta cikin zuciyarta tana dariyar mugunta,sai da ta barshi ya sakankance sosai ta take motar ta qara maya gudu sai ji yayi fit ta wuceshi ,cikin zafin nama da mazantaka ya qara wa tashi shima wutar don ya nuna mata bata isa ba saidai kafin ya qaraso har ta qaraso kwanar freedom ta sanya signal ta shige,ta morrow din gaba suka hada ido yana wucewa amma sai ya wuni mugun dauke kai kamar ma bata sanshi ba Ya girgiza kai ya miqe kasancewar b.u.k zai shiga hanyar ta rabu cikin zuciyarsa yana fadin"zan koya miki hankaline kin maida ni abokin wasanki kenan Qarfe biyu ya baro b.u.k din bayan ya kammala abinda ya kaishi,kai tsaye ya tashi motarsa ya bar makarantar,biyu da rabi ya iso freedom hakanan bai taba zuwanta ba koda hira suke son yi da shi yana basu appointment ne,ahankali ya gangara layin ya qaraso bakin gidan radio din ya yiwa mai tsaron bakin qofa horn ua taso don yaji me ke tafe da shi,da ganinsa ya fara fara'a cikin mutunci suka gaisa ba tare da jiran komai ba ya bude masa qofa yana jira ya shiga,da hannu aliyu yayi kiransa ya qaraso saitin window ya ranqwafo yana saurarensa,"wata sabuwar ma'aikaciyar ku nake nema ina fata bata fita ba"cikin tunani yake kalleshi,aliyu ya gyada masa kai da son tabbatar masa,sai kuma yadan saki murmushi yace "oh ko haj fadila?"aliyu ya gayada kai yace"yes itace" tana nan ciki kuwa bata fita ba mutuniyar arziqi kuwa ranka ya dade.....ko kira maka ita za'ayi"aliyu ya dakatar da shi" a'ah barshi zan dan jirata ba matsala"ya tada motar ya shiga security suka nuna masa gun parking"ya daidaita motar qasan bishiyun dake gun ya kasheta,ya miqar da sit din nasa ya kwantar da shi yadda zai masa dadin kwanciya,yayi sama gaba daya da glass din motar kasan cewarsu akwai (tinting)jikinsu,yasa hannu ya qaro qarfin a.c dake jikin motar ta gauraye masa ko ina ya kashe dukkanin wayoyinsa ya watsa su sit din gefansa,ya maida bayansa ya kwantar jikin kujerar yana fuskantar ginn gidan idanunsa akan reception,lokaci lokaci kuma yana bude mujalla yana dubawa Zaman minti ashirin yayi ya ganta ta fito gefanta wata yar matashiyar ce sabe da baby girl a kafadarta ,ita tayi hanyar waje ita kuma ta nufi inda tayi parking tasa maqullinta ta bude motar tashiga,ya miqe ya gyara zaman kujerarsa ya jawo belt ya daura,ya kunna motar ya biyo bayanta sanda take ficewa daga ginin gidan radiyon Ko kusa fadila bata lura da shi ba don bata kawowa ranta ba,cikin kwanciyar hankali take tuqinta,wani mahaukacin horn taji ana mata kafin ta ankara motar ta zo daf da ita tana shirin gogarta a gigice tayi gefe da motar tana ci gaba da kallon motar da ta kasa tantance waye a ciki?,kafin ta gama wannan tunanin har ya dawo daya side din data koma ya sake matsowa daf da ita yana shirin gogarta,sai ta tsorata kasancewar titin da ta biyo ba mai yalwar jama'a bane bugu da qari kuma rana ce babu gilmawar mutane sosai a gun Cikin lokaci qanqani ya gama rudata gaba daya ta tsorata dama da hugunta ya dinga komawa,tuni lissafinta ya qwacr tama manta sitiyarin na hannunta ne,sai ta taji motar ta soma yawo da ita saman titi idanun aliyu na kan motar,ya zubawa motar ido ganin ta soma yawo bisa kwalta a hankali yana nazari,ya saki ajiuat zuciya sanda yaga ta daidaita ta daina tangal tangal din da takeyi,ya qaraso saitin window dinta sai ya sauke glass ta juyo idanunta cike da taf da tsoro suka hada idanu,ya dauke kansa ya qarawa motar speed yayi wucewarsa,wani abu ya daki zuciyarta sai ta kasa tuqin,ta sauka a hankali ta gangara gefan kwalta ta kashe motar ta jingina da makarin motar idanunta a runtse zuciyarta na ci gaba da bugawa ,sai hawaye ya biyo rufaffun idanunta ta saki kuka silently,sai da taji don kanta ta samu nutsuwa sannan ta kunna moyar taci gaba da tafiya slowly a gefan titi don gaskiya ya dauki haqqinta Tana isa parking space taga motar tayi tsammani ya shge cikin gidan saidai tana gama kulle motar ta ganshi tsaye jikin motar yana amsa waya,idanunsa suka shiga cikin nata wadanda suka dan kafa alamar tayi kuka takaici yasa ta sakar masa harara hadi da murguda masa baki ta shige jin alamun taku tayi ana bin bayanta,tana juyawa taga kuwa shi din ne,tasan mai yasa ya biyota cikin azama ta qarasa shigewa bangaren nata daidai lokacin da yakai hannunsa zai fincikota,tayi saurin sanya maqulli ta qulle qofar hadi da jingina a jiki,tana kallonsa ya juya ya koma" kawai"ta fada a hankali Zaune take tana kallon wani Indian film hum dil de chuke sanam tana ganin son maso wani tamkar nata da aliyu,ta bada hankalinta kacokam bisa t.v din sai tsintat qamshinsa tayi yana yawo bisa hancinta,ta dago da
Chapter 29 · 0% Book details