Sashe 12
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na raguwa hakan ya tabbatar mata ana debe su ne tafiya suke,ga tarin mamakinta sai ta jiyo muryar samira na cewa"ku gaida gida na gode Allah ya huta gajiya,ina jiranku gobe da safe,kuma wlh kada ku yarda sai sun vika muku kudin siyan bakin"fadila ta jinjina kai tana cewa cikin zuciyarta lallai ba shakka kowane tsuntsu kukan gidansu yake Cikin qanqanin lokaci gidan ya sake zama tsit,ba komai cikinsa sai hasken fitilu daya gauraye da kukan tsintsaye da kuma gyare jefi jefi,haka ya sake assasa tsoron dake zuciyar fadila ta runtse idanunta gam tana ambaton sunayan Allah hadi da addu'o'in tsari,sannu a hankali taji idanunta da jikinta sun fara nauyi ,gajiyar kwana da kwanaki suka fara sauko mata,taji bata da buqatar komai illa kashingida,ta zame ta dogara gwiwar hannunta a hannun kujerar,tsananin gajiya yasa bacci har y a dauketa bata sani ba ASUBA TA GARI AMARYAR ALY Mrs muhammad bello ce [10/16, 12:29 PM] Salma Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Firgigit ta farka kamar an tasheta,ya zame mata jiki tun a gida assalatun farko take tashi tayi yan nafilfilu kafin assalatu na biyu daga nan idan ta idar tayi baccin mintuna idan tana da lacture ta shiga kitchen ta shirya breakfast,yauma gajiyar bata hanata tashin ba saidai ta sabawa lkcn da ta saba tashi sai kiran a kiran sallah na biyu ta tashi,cikin kasala ta miqe don har yanzu tanajin nauyin jikinta tayi miqa hadi da salati idanunta suka kai kan wata farar leda babba mai dan duhu guda biyu tsoro ya darsu a zuciyarta ta katse miqar a iya saninta sanda zata kwanta babu ledar a gun to ya akai ta samu?cikin sanda ta isa inda ledar take kamar wadda akace za'a kama,saidai tunkan ta bude ledar qamshin turarensa ya ziyarci hancinta,hakanne ya bata amsar tambayarta lallai aliyu shi ya shigo da ledar tayi mamakin yadda har ya shigo ya fita bata sani ba, Ta bude ledar gasashshiyar kaza ce wadda akai wrapping dinta guda uku sai ice cream da ya gama narkewa saboda an ciroshi daga ma'ajiyarsa sai fresh milk manyan roba har uku,sai yoghurt shima roba uku tayi ajiuar zuciya ta mayar da kayan,kasala ta sake kamata taja da baya ta koma bisa kujerar ta zauna tana aheqar daddadan turarensa tamkar yanzu yake a gun,ta shiga hasashen fuskan aliyun a cikin wadannan awoyin da yake angon mutum biyu,kishi ya taba zuciyarta,tafan bata waau lukuta a zaune ta kasa tabuka komai sannan ta miqe ta lalubi corridor din nan ta zabi bedroom daya ta shiga,tana alwala tana qarewa tsaruwar toilet din kallo,tabbas dole hajja gana tace kamar ba za'a mutu ba,bayan ta idar sa sallar ma tana lazumi dakin taci gaba da bi da kallo tana yaba irin namijin qoqari da iyayenta da yayansu Ahmad suka yi,bata kammala ba wani daddan bacci ya rinjayi idanunta nan bisa dardumar sallarta Hasken rana da ya soma shigowa ta window yana taba fuskarta shi ya farkar da ita,da addu'ar tashi daga bacci ta miqe a bakinta ta dubi agogon dake ajjiye kan bedside ya nuna mata goma da minti sha biyar na safe batayi mamakin awanni data shafe ba tana baccin ba,toilet ta shiga ta kunna water heater dake manne a kusurwar bandakin cikin mintina qalilan ruwan ya tafasa ta kunna shower ta daidaita zafinsu ta shige kwamin wankan ,tsaf ta shirya cikin atamfa mai zanan manyan ganye mai kalolin pink da ja sai light blue,dinkin da ita atamfar kanta tayi.masifar karabarta duk da ba wani make up tayi ba hoda ce kawai sai man lebe da kwalli,dinkin ya lafe mata sai kayi tsammanin fitted gown ce daurinta yayi das wanda ya awa gashinta damar kwanciya bisa dokin wuyanta Ta fito falo ta kwashe siyayyar jiya ta kaisu kitchen,tsayawa tayi kallon kitchen din tana jinjina kai da dan guntun murmushi akan fuskarta ba shakka ummi tasan tsarinta game da kitchen kuma ta san maitar kitchen irin tata don haka ta cika mata ahi da dukkan wani nau'i na kayan amfanin kitchen babu ce kawai babu,abun nema ya samu nan ta bata lokaci gun tsara da shirya kitchen dinta yadda take muradi,tana tsaka da aikin ta jiyo ringing din wayarta wadda ita sam ma ta mance da ita ta fito galin tana laluben inda take,tsakiyar filalluka ta hangota tasa hannu ta dahota tana duba mai kiran garida ta gani tayi yar dariya sannan ya daga hadi da sallama,muryar farida a qasa ta amsa fadila tace lafiyanki qalau kuwa?"ta masa mata da "hmmmm,ai dole ki ce min lpy qalau tunda ke naji miryarki garau da ke "fadila da bata fuskanceta ba tace"kamar yaya? Wani abu ya faru ne a gida?"farida ta sake ajiyar zuciya tace"mubarak bashi da tausayi Allah sister fadila jiya kada kiso kiga rashin imanin da ya gwadan,anty hafiza tasan haka amma ta dinga dirka mana magani"fadila data dau haske a zancan nata tace"to Allah ya kyauta""wlh kin ga na kasa tashi sister"ta fada cikim karyewar murya,wani yarrr fadila taji tausayinta da tsoro suka kamata tace"ai ke likita ce saiki kula da kanki Allah ya bada lpy"tace"amin na gode ina ya Aliyu" "Baya nan" Cikin sauri farida tace "kada dai ace samira kika miqawa uwargidan bayan ke aka fara daurawa aure kuma ke aka fara kaiwa?" Fadila cikin son abar zancan tace"ban sani ba 'yar jarida kije ki fara jinyar kanki tukun idan kin warke sai kiji amsa"ta katse wayar,jikinta yayi sanyi sosai a salube ta zauna agefan kujerar,ashe har faahin matsayinta ma sai da aka mata?ita idan banda yanzun ma bata san itace gaba da samiran ba tasa hannayanta biyu ta dafe kanta cikin wani irin yanayi da ta kasa tantance ame take?,ganin ba mafita yasa ta koma kitchen taci gana da gyare gyarenta zuciyarta cike fak da tunani, Da azahar baqi suka soma zuwa mata sallama din komawa gidajensu yan maiduguri ne da yan gwambe,zuwa qarfe uku suka tafi sai su rumasa'u sa'adah minah rahama da hafsah duk cousins dinta ne rumaisa tace'?"wai ke ya ne?"fadila ta kalleta da alamun tambaya ,sa'adah ta karbi zancan "gidan farida muka fara zuwa tana can kwance mubarak nata hidima amma ke gaki dungur gur a zaune"fadila ta juya idanunta tace"lallai yarannan"da yake ta basu tazarar yan kwanaki ta Dora"kuce kawai uawon sa'ido yau kuka fito ko"dukkansu suka sheqe da dariya ,suka ce"to ai gwara kafin mu wuce muga lamira sun daidaita " tace"to Allah ya qara muku himmar sa'ido"ta fada tana shirin shigewa toilet rahama tace"to ai sai ki kira mana angon mana mu gani ko shi aka dorawa jinyar"ta jiyo ta harareta tace"baki isa ba kuma kwa qaraci zaman gulmarku ku tattara yammatan qafafunku ku koma inda kuka fito"suka sake aheqe mata da dariya ,ita kuwa ta shige toilet din tana fadi a ranta"koni bancin arziqin samun ganinshi ba rabonku da ganinsa tun a dinner to nima hakan take" La'asar gidan ba kowa duk sun yoye sun mata yan gyare gyaren da suka ga ya dace na game da jere da yan goge goge sukayi sallama cike da kewa tabi kowaccensu da dan dasheshan turare,turaren wuta ta zuba a bin turare mai amfani da wutar lantarki ta daidaita sanyin a.c falon yayi wani dadi qamshi da sanyi auka hafe guri guda,turare na musamman da hajja gana ta musu da kanta kuma ya tsumu sosai don ya jima a ajjiye ta musu tanadinsa,don haka qamshin har farfajiyar gidan,wajajen biyar ta sake gyara fuskarta ta feshe jikinta da turarurruka don dama babdaga baya ba fadila gun qamshi ta gabatar da la'asar da ta kufce mata,tana linke sallayarta tana ci gaba da jiyo hayaniyar dangin samira don tun farkawarta da safe wajan goma da rabi ta fara jin zuwansu,ta gama ta koma falo ta kama mbc bollywood dan ta samu ta debe mata kewa,kafin takai ga zama kan kujerar taji ana knocking din qofarta,ta nufi qofar tana cewa "waye?"saidai shiru ba'a amsa ba,don haka tasa hannu ta bude idanunta a waje don ganin waye,a subhanallah,ta fadi a zuciyarta saida bugun zuciyarta ya dadu sosai fiye da qima,Aliyu ne tsaye a bakin qofar yana sanye cikin wani lallausan farin yadi qal(tissue),yadin nada shara shara don hakka hatta farar vest dinsa kana iya hangota,dinkin yarbawa aka masa(boda)iya gwiwa da dogon wando yana sanye da baqin takalmi idanunsa saye da farin gilashinsa na qa'ida kansa ba hula sai kwantacciyar sumarsa kamar mai sa mata relaxer saidai natural ce haka sumarsa take,qamshin turarensa ke dukan fuskarta,tsintar muryarsa tayi yana cewa"su bar maka a nan ka dinga daukowa kana ahigowa da su"hakan yasa ta tabbatar bashi kadai bane,tayi niyyar yin sauri ta koma ciki don ba hijabi a jikinta saidai ta kasa moysa qafafunta,sai jan jiki da tayi ta rakube a bayan qofa,nasiru n yake shigowa da kayan abinci duk wani dangin abunci da nasha na har ya kammala shigewa da su tsaf aliyi na tsaye tsakiyar falon hannayansa zube cikin aljihunsa yana facing qofar store yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,ta haka fadila ta morewa kallonsa ba tare da ya sani ba,ingarman namiji ne wanda siffar qarfi ta bayyana atare da shi bayansa kawai ka kalla zaka fassara hakan,nasiru ya fito yana kade hannayansa ya dan russauna yace"yallabai na gama"yana qoqarin zaro kudi a aljihunsa yace"yauwa ya miqa masa kudin yace"raguna zaka samo guda biyu ka biyaau su gyara komai su wanke acan ka duba motar zuwa kasuwa ka tafi a ita""to yallabai"ya fada yana shirin wucewa"nasir"aliyu ya kirashi a aladabce ya juyo yana amsawa"ka biya ta gidan gona su gyara kaji ka taho da su""an gama sir"cewar nasiru ya fice da sauri Ya juyo yayo tattaki har zuwa bakin qofa,fadila ta saci kallonsa sai taga hankalinsa na waje,cikin sanyin jiki da sanyin mutya tace masa"ina wuni"yqdan kalli sashin da take ya kauda kai,cikin wata dakakkiyar murya yace"kada ki qara zama haka bayan kin san cewa ba ni kadai bane,in kunne yaji......"tace"to"har yasa qafarsa awaje yadan dawo da baya ba tare da ya dubeta ba yave"qarfe takwas ki sameni a gefena"to ta sake cewa,"shikenan babu abinda kike da buqata?"ya fada yana duba agogon hannunsa,"babu"tace "Ok ki duba saman kujerarki"kawai yace yasa kai ya qarasa barin sashin aransa yana cewa"ta wani labe sai kace wadda ake kora" Hannayansa harde bisa qirjinsa yake bin harabar gidan da kallo ,ko ta ina dangin samirah ne kamar