Sashe 56
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace tayi abu uku ta iya wanka canza kaya sai sallah,tana zaune akan darduma tana share hawayen dai nata,ta yanke hukuncin da taga shine daidai saidai ta rasa me yasa zuciyarta ke son bijere ma umarninta?,anty hauwa ta turo qofar ta shigo ,a sanyaye fadilan ta dago kanta tana masa mata sallamar sai kuma wani dan kukan mai dan qaramin sauti ya kubce mata ta sunkui da kai,dirshan anty hauwan ta zauna gabanta ta riqo hannayenta "cool down fadila mana,ki nutsu ko gayamin me yake faruwa?,ni kuma na miki alqawari tunda kika zabeni kika kawomin matsalarki zanyi qoqarin warware miki ita"cikin sigar lallashi har anty hauwa ta ciyo kanta ta tsagaita kukan duk da hawayen dai basu bar zuba ba Ta danja majina irin ta mai kuka tace "anty so nake na rabu da aliyyu"zaro ido antyn tayi har da sakin hannun fadilan,daga bisani ta tattro kalaman tambayarta "saboda me fadila?,me ya shiga tsakaninku haka bayan kowa na ma ali murnar morewa aure yanzu?kowa sha'awar zamanku yake?,"murmushin takaici ne ya kama fadila ta girgiza kai "anty zaman mu abun sha'awa ne ga wanda baisan halin da nake ciki ba,ni da nasan me nake ciki banga abun sha'awar ba,banga sha'awa ga tilastawa wanda bai sonka ya zauna tare da kai ba,kin taba ganin inda anty wuta da ruwa suka hadu suka cakuda suka zauna kuma suka rayu suka wanzu gu daya?,banga abin shaawa ga zamantakewar auren da babu soyayya cikinta ba sai zallar qiyayya,anty aliyyu na cutar da ni ta hanyar rashin samun soyayya da kulawarsa,hakana ina matuqar cutar da shi ta hanyar tilasta masa zama da ni baya baya so,baya sona,ina cutatsa ta hanyar sashi kallona a matsayin matarsa,bayan ya gayamin baya sona bakuma zai taba sona ba,don me zan zauna anty allah ya kamani da haqqin cutar da shi?" Ido ta kuma zarowa tace"kamar yaya fadila,kimin gwari gwari ki daina min zancen kurma da bebe" Ta dago tsaf tana kallkn antin don mafita yanzu take nema,so take ta canza rayuwarta yanzu,so take ta bude sabon babin rayuwa ta manta komai,rayuwartatake so ta maida ta ta mafarki ta fara ta gaske,tana so ne ta manta da aliyyu ta manta ta taba sonsa,baya sonta(a zatonta) itama ya kamata ta qishi(nikam nace hmmm zaiyiwu kuwa????)hmmmmm muje dai zuwa ga *part 3* *alhamdulillahi rabbil alamin,wassalatu wassalamu ala man talaqqal qur'nu mi ladun hakimul khabir* *godiya ga mahaifana* *sannan godiya ga dukka members din group dina huguma novels readers da dukkan wani masoyi na wa yasan gobe,Allahbya bar qauna ameen summa ameen* *kuci gaba da bina da jin yadda wannan rikita rikita zata kasance,meye ra'ayinku game da jaruman wannan littafi?ina saurarenku ta number wayata* *na gode* *mrs muhammad ce* [10/16, 2:08 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* WA YASAN GOBE?....**WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HIGUMA* *PART 3* A hankali ta bude bakinta tace "anty *ta inda aka hau ta nan ake sauka* ,kece silar qulluwar igiyar aure na da aliyyu,ranar wanka kuma ba'a boye cibi"............A nutse cikin hikima ta soma labarta mata tun ranarhaduwarsu da aliyyu,ta fara sonshi tun kafin tasan waye ne shi,hakanan tun kafin shima ya san tana yi,ta rufe da cewa "sai ajiya na sake tabbatarwa aliyu ba sona anty yake ba bisa wani qwaqqwaran dalili nawa"(ta rufe ba tare da ta gaya mata ba),tayi shiru hawaye na diga a fuskartaShuru anty hauwa tayi don ta kasa cewa komai,ta jima cikin jimami,ta jima tana gyada kai kafin daga bisani ta saki nanauyan ajiyan zuciya "fadila sannunki da qoqari,ba shakka ke din jarumar mace ce mai son farincikin iyayenta,kin cika 'ya ta gari kuma 'yar halak,dama wannan zaman kike amma bamu taba gani ko a fuska kin nuna alamu ba?,tabbas aliyyu zaici qaniyarsa duk hukuncin da kika daukar masa ya dace da shi,wanne taimako kike da buqata a guna fadila fadeshi,kowanneiri ne zan iya miki shi,nayi da na sanin zamowa silar hada aurenku,na zamo silar xamanki cikin qunci bayan ni ima zaune cikin walwala"anty hauwan ta fadi cikin takaiciGirgiza mata kai fadilan tayi "kada ki soma dana sani anty,domin kuwa qaddarar Allah ce,ya hukunta hakan dole sai ya faru koda babu ke anty......alfarma daya nake so anty....bana son kowa ya san ina gidan nan koda kuwa 'yan gidan mu ne,bana son in sake tozali da aliyyu har sai ya ban sakina,rabuwa nake son nayi da shi saboda na barshi ya sake yayi rayuwarsa ba takura,in barshi ya rayu da masoyansa don rayuwa tare da miqiyi cikin inuwa guda ciwo ne da ita"ta fadi maganar tana jin wani daci har kan harshentaSosai anty hauwa taji wani tausayi nata har cikin ranta ta girgiza kai gami da kama kafadarta"indaiwannan alfarmar kawai kike nema fadila baki da matsala,kin samu dari bisa dari,amma in one condition.....sai kin min alqawarim cire wannan damuwar daga zuciyarki,kin bar wannan dan banzan kukan da kike,ba lokacin ki bane na kuka yanzu lokacin aliyyu ne har taya shi ya kamata ayi saboda asarar mace irinki da yake shirin yi,asarar da bazai taba maye gurbinta ba,dubi fuskarki yadda ta canza saboda tsananin kukaMurmushin yaqe tayi"insha Allahu na bar kukan anty daga yau,bazan sake zub da hawayena ba akan aliyyu,yadda bay sona ni din ma na bar sonsa kenan har abada" "good" anty hauwa tace tana dariya hadi da girgiza hannayen fadilan,sai kuma kunya ta dan kamata yadda ta taqarqare tana gaya mata bata son dan uwanta ita kuma ta kuma tana bata goyon baya ba tare da son kai ko zuciya ba ta sunkui da kai,Murmushi anty hauwan tayi "kada ki ji kunyata fadila gaskiyarki kike fadi,kowanne hukuncikuma da kikayi yayi daidai,don wallahi kinji na rantse miki mace dai dai ce zata iya irin zaman da kikayi ba" Ya sallami mai taxi din da kudin da shi kansa baisanyawansu ba sannan ya shige gidan,bisa kujerar falo ya zube yana maida numfashi,wani azabar ganinta yake son yi ,a hankali ya kai idonsa inda ta saba ajjiye masa ruwa da drinks wayam gun yau ba komai,ba qamshin girkinta babu na freshner dinta,sai yaji gidan tamakar kango garin ya koma masa tamkar maqabarta,burinsa kawai gobe tayi yafice ya bar qasar,wayarsa ta soma karadi ya cirota don takaici bai san sanda ya bugata da qasa ba ta bude komai ya tarwatse a saman centerA sanyaye ya zauna gefan gadon hadi da zubawa farin bedsheet din nasu ido yadda ya baci da jini haryanzu yana bisa gadon,bai son tayar da ita ne a jiya shi yasa ya tureshi gefe ya kwantar da ita,idanunsa suka sake kaiwa kan tray na breakfast da ya hada mata tun safen kafin ya fita,yana nan yadda ya shigo da shi dai dai da cup ba'a juya shi yadda ya saka shi ba da alamun babu abinda taci kenan?Ya daga zanin gadon yana qarewa jinin jiki kallo,shi kansa bedsheet din wata qimarsa yake gani,daga qarshe ya duqunquneshi a qirjinsa da dukka hannayensa biyu idanunsa na a lumshe,wata mahaukaciyar soyayyarta ke ratsa shi,baisan lokacin da ya kwanta saman gadon ba,fuksarta ce kawai ke masa yawo cikin idanunsa,zanen fuskar yake gani sanda suka kasace a lokaci mafi tsada dadaraja a rayuwarsa,lokacin da bazaya taba barin tunaninsa saidai mutuwa ta cire masa shi,lokacin da bazai taba daina ganin darajarsa ba saidi mutuwa ta hana shi,qamshinta ya dinga ji sosai kan pillow din da ta kwata tamkar tana gurin,da sauri ya bude idonsa,vest din ta ce ta jiyan daya yaga saitin hancinsa,da sauri yasa hannunsa ya dauko ta yana sake mannata cikin hancin nasa,tamkar zai shide tamkar zai zuqo fadilan daga jikin vest dinJuyi yake sosai cikin wai irin shauqin qauna da soyayya da bai taba zaton akwai makamanciyarta ba a duniyarmu "why u leave me?why?,I cannot sustain missing you,I can't,me yasa sai da kika mun kyautar abu mai tsada da daraja baki tsaya kin karbikema abu mafi tsada da daraja aguna ba kika barni?,me yasa ba zaki tsaya na saka miki dimbin kyautatawarki gareni ba?,why baki sanar da ni sirrin zuciyarki ba sai lokacin da kika barni why?....." shi kadai qwal cikin gidan harma a dakin yake ta wadannan sumbatuSam ya kasa hassalawa kansa komai,koda suit dinsaya gaza cirewa bare akai ga yin wanka ballantana kuma batun abinci,koda yana da buqatarsa bazai iya ci din ba don harshensa bai gamsuwa da girkin kowa idan ba natan baSai yanzu ya soma tantance son da yame mata ashe yafi wanda yake ma girkin ta?,sai yanzu ya fara ankara da dalilin da yasa yake hasala da yawa idan bata gyara masa part ko bata masa girki ba fiye da yadda yake jin zafi yake hasala fiye da su samira?,sai yanzu ya gane dalilin da yasa yake jin haushi idan ta kammala girki ta bar masa bangarensa kafin ya dawo?,sai yanzu ya fuskanci dalilun da yasa yake qin cin abinci har sai ya tilasta ta ta zauna by his side har sai ya kammala?,ashe sone hakan?,wani irin salon sone wanda bai farga da wane lokaci da kuma yaushe ya shiga zuciyarsa ba sai yanzu?,ba abun mamaki bane don bai taba kamuwa a akaran kansa da *SO* din ba sai a kanta,tamkar ya taso ne ya saba da cusa masa shi ake ta qarfin tuwoKamar ya jawo goben haka yake ji,daren gaba daya ji yayi yayi wani mugun tsawo a gunsa kamar jansa aka dada yi,gani yake kamar gari bazai waye ba,kayanta dake cikin cupboard gana daya ya watsosu ya barbazasu kan gadon ya kwanta akai yana shaqarsu ko zai samu sa'idar zugi da zillo da zuciyarsa ke masa game da ita,saidai inaa....kama da wane bata wane,tamkar wani zautacce haka ya koma idanunsa jazur bashin baccin jiya da yau gabadaya kuma bacci bai ziyarceshi ba sai gab da suba Kiran wayarsa su mr lun ke tayi amma gaa daya layukan switched off,suna baqatarsa sosai don awanni uku kacal ya rage a soma gudanar da bikin,baqi masu zuwa nata tambayarsa,hakan yasa andi da kansa ya taho gidan takanas ba shiriCikin bacci yaji anataba qararrawa da alamun neman izinin shigowa ake,tsaki yaja ya maida kansasaman filon hadi da maida fuskarsa hannun hagu maimakon dama a yadda take dazu bashi da ko niyyar tashi,saidai mai danna qararrawar yaci gaba da matsata kamar babu gobe har sai da mijin nadiya ya fito abdul basid,hakanne ya sashi miqewaa fusace ya zare rigar saman ya cire tie din ya wurgar ya bar