Sashe 48
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wata doguwar ajiyar zuciya cikin baccin nata harda juyawa,ya kalli hannunta handkerchief din da ya bata ne duqunqune tsakiyar dogayen yatsunta,karo na farko wani abu mai kama da tausayinta ya ratsa zuciyarsa,ya tuna yadda ta tsorata dazun ya tabbata rashin dawowarsa ne da baiyi da wuri ba da kuma dauke wuta da akayi wanda qarewar kudin wutar su ne daga can company din ya jawo haka,yasa hannunsa ya danyi mata baya da gashinta da keson shigar mata ido Da sauri ya janye hannunsa kamar wanda wuta ta ja,ya daga kai ya kalli lokaci sha biyu na dare saura minti shida,yasa hannu a ahankali kamar jiya ya zare filon nata,a tsorace kuwa ta tashi don har sai da yasa hannayensa ya tareta don kada ta fado,sai bayan ta nutsune suka hada ido ya janye hannunsa tayi qasa da kanta,tana jin takunsa sanda ya shige bedroom,sai da ta tsaya ta tattare kwanukan ta mada kitchen dare ya riga yayi ga dan Karen tsoro wanda ya hanata gyare gun kamar yadda ta saba Tamkar jiya yauma kwance yake saman center saidai yau lullube yake da wani qaton lallausan farin bargo ba irin na kan gadon ba,saidai ya debe gaba daya filallukan kamar jiyan blanket din kawai ya bar mata Again yauma dai sallar ta tarar da shi yana yi saidai ita bayan sallar asuba bata koma bacci ba breakfast ta hada masa don taji da yana waya kamar yana cewa zai fito da wuri zasu Beijing Washegari maqociyar ta ta hannun hagu mr lin ta shigo mata 'yar asalin qasar china dince tana da yara uku,sosai fadila taji dadin kulawar da ta nuna mata sun dan jima suna taba hira har daya mqociyar tata ta shigo,sunanta nadiyya 'yar asalin alqahira ce sai fadila tafi farinciki da nadiyya fiye da mr lin saboda addini da suka hada duk da cewar itama mai kirki ce,saidai ita nadiya yaronta daya mashkur sai mai gidanta abdul-basid karatu ne ya rabosu da qasarsu,sunyi hirarsu da ita sosai cikin harshen larabci don ta nan bangaren ma ba'abar fadilan a baya ba Rayuwa aqasar da baka da kowa ba wanda ka sani bata fiya dadi ba ba kamar idan kana qasarka ta gado ba,to hakanne ya kasance ga fadila da zarar aliyyu ya fita ta kammala aikace aikacenta sai ta koma kan waya ko computer ta duba saqonni,idan ta gaji sai ta sanya hijabinta ta dawo balcony ta zauna tana kallon masu shige da fice,duk da cewa unguwa ce da bata da yalwar jama'a amma ba'a rasa masu wucewa jefi-jefi har wasunsu kan tsaya suyi mata magana ganinta baqar fata mutanen qasar mutane ne masu so da girmama baqo hadi da mutunta shi A irin wannan ne ranar bayan ta kammla aikinta da wuri ta hau social media dinta ta gaji ta dawo balcony kamar yadda ta saba,saidai yau da gobe sai Allah sai zaman nan din ma ya gundireta,wasu 'yammata su uku ta gani sunzo wucewa dukkaninsu akan kekuna suna tafe ajere suna hirarsu abinsu ,sai taji tana da sha'awar zaga koda layin sune zuwa qarshensa Cikin zumudin tunanin da tayi ta zqro wayarta ta dan yima aliyyu text, _*please zan dan fita qarshen layi*_ Mrs muhammad ce *WA YASAN GOBE?..* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 2* Ta kalmashe wayar a hannunta bayan ta tabbatar saqon ya je,ta miqe ta saya qofar don bata damu da sai ta kulle ba ta san qasa ce mai cike da tsaro A hankali take ratsa layukan duk da dan banzan sanyin dake bugarta amma yanayin yayi mata dadi sosai,tana tafiya tana cilla hannayenta gaba da baya fuskarta qunshe da murmushi ,unguwar ta burgeta matuqa babu yawan jama'a tunda dama can ita bata son hayaniya,sai yara jefi jefi dake wasa wasu cikin balcony dinsu wasu kuma a qogar gida duk wasannin nasu baya wuce tseran keke da buga qwallo(football) Abinda ta lura da shi shine su kamar ma sanyin bai damesu ba ba mamki ko don qasarau ce sun saba,har ta fita daga layin da shiga second street bata sani ba,yara ta gani su hudu babbar ciki ba zata wuce shekaru tara ba ma bi mata ba zata wuce takwas ba ta ukun kuma ba ta gaza uku qaramar ce mai alamun biyu amma da yake yanayin qasarsu ya bam banta da namu buka buka da su masha Allah,ball suke bugawa suka bugo mata saidai a qafarta ta sauka basu sameta ba Babbar cikinsun ce ta fara lura da wadda suka bugawan ta tabo mai bi matan tana mata rada akunne tana kallon fadila duk sai suka juyo suna kallonta,fadika ta sunkuya ta dauki ball din ta nufi inda suke fuskarta dauke da murmushi suma murmushin suke saboda ganin baquwa,ta ajjiye ball din agabanta tabuga ta ta tafi gabansu ai kuwa suka hau ysalle da murna suka dawo mata da ita,duk da bata jin yarensu amma ta gane dadin hakan sukeji A nan gurin yaran ta bata lokaci sosai ba tare da ta sani ba,yaran sun sake sosai da ita nan ta hada su dukkaninsu ta shige tsakiyar su tayi musu hotuna,suka shige gidajensu suna daga mata hannu,sai alokacin ta duba gari taga ya soma duhu hankalinta a taahe ta juya ta soma laluben hanya garin haka sukayi kacibus da mutumin nata (kare)shaf ta manta kare baya son gudu don a rude take tuni ta takure ta sheqa a guje shi kuwa ganin haka ya rufa mata baya Motar kamfanin ta ajjiye aliyun a qofar gida yayi sallama da su yana jaddadawa wanda ke gaban motar su tabbatar gobe early in d morning sun kawo engines din nan an qarasa kafasu agurarensu,ya amsa masa cikin girmamawa,suka ja moyar shi kuma ya juya ya shige gidan Qwan lantarkin na kashe yasa hannu ya kunna haske ya gauraye falon,neat yake kamar ko yauahe cike da qamshi ya jefa ri gar samansa da ya cire hade da jakarsa kan kujera shima ya zauna,a gajiye yake tubus ya soma zare takalminsa da safarsa sannan ya kalli inda ta saba ajjiye masa ruwa da lemo wandayake fara sha da zarar ya dawo,wayam babu sai abincinsa dake jere saman dining,yanmiqe ya bude freezer wanda basu kunnata sosai yanzu saboda yanayin sanyin garin ya ciro ruwan roba,ko cup bai nema ba ya balle murfin ya kafa kai sai da yasha kusan fiye da rabi sannn ya maida ya rufe Bedroom ya nufa don yin wanka hadi da alwala cikin zuciyarsa yana mamakin rashin jin motsi ko yaya cikin gidan,mamakinsa ya dadu ganin babu ita a dakin ya bude toilet babu ruwan wankansa wanda ya riga ya saba ya tadda shi yana jiransa,tunaninsa sai ya tafi ga ko tana kitchen,ya nannade hannun rigarsa ya daura alwala idan yayi sallar daga baya yayi wankan tunda yau bai samu ruwan ba,har ya shimfida abun sallah zai tayar sai kuma ya fasa zuciyars ta kasa samun nutsuwa,sai yakejin wani irin rashin ganinta amma sai ya alaqanta hakan da sabawa da yayi da ganin nataidan ya dawo Kitchen din ya nufa kai tsaye bata nan,wani dim yaji zuciyarsa ta harba ,ya riga ya sani tunda auke da ita bata taba fita koda qofar gida ne ba tate da izininsa ba,a hanzarce ya koma bedroom inda ya ajjiye wayarsa saman madubi call logs ya shiga da sauri da sauri yana dubawa dinta ko Allah zaisa yaci karo da number dinta,tsaf ya gama bincikensa bai ganta ba,ya saki ajiyar zuciya hankalimsa amatuqar tashe,sai sannan ne ma idonsa ya kai kan 'yar qaramar envelope dake maqale saman wayarsa wanda ke nuni akwai sabon saqo a wayarsa, Har zai maida wauar aljihu sai ya fasa ya jawo saman wayar ya shiga gun sms,numbers ne guda biyu daya ba suna daya kuma ta mr jake ne,yana gama karanta tex din ya tabbatar ita ta turo masa shi baisan sanda ya juya ba ya zira silifas ya fita a sukwane ,da sauri yake daddanna numbobin jumong daya daga cikin direbobin kamfaninsa wadanda suka fi kusa da unguwar da auke ciki yave ya kawo masa mota yanzu yanzu,bai iya ysayawa jiran mitar ba ya fita da qafafunsa yana ji ajikinsa cewa hanyar dawowa ta rasa A hanzarce yake tafiya,kasancewarsa giant ma'abicin kuzari sai gashi yayi tafiya mai dama kafin isowar jumong din Ta waiwayo cikin gudun dai bata fasa ba taqin dake tsakaninta da karen dan kadan ne,ta saddaqar cewa ta gama yawo,tuni tayi surrender ta tsaya cak lokacin da taga ya daka tsalle tana jiran taji ya yago ta,qyam tayi jinin jikinta adaskare,rungumeta taji anyi yayin da qamshin turarensa ya mamaye mata hancinta,tsawq taji ya daka wa karen ta bude idanunta ahankali yayin da dumin jikinsa ke ratsata,sum sum taga karen ya juya cikin sassarfa ya bar gun,sai da ya bace alayin sannan ya juyo ya kalli qwayar idanunta,idanunsa fal da fushi sai huci yake,hannunta ya fincika ya bude bayan motar ya sanyata sannan shima ya shiga jumong ya tada motar Bai ce mata uffan ba kamar yadda bai sake kallonta ba idanunsa na bisa titi har yanzu kana ganin fuskarsa kasan cikin fushi yake,kuka take kanta na qasa ita kanta ta rasa kukan kuma na mene tunda Allah ya taimaketa,sai da suka qaraso gidan sannan ta tabbatar aahe tafiya tayi mai yawa bata sani ba irin haka? Ya bude side dinsa ya fito sannan ya bude nata ya damqo hannunta ya fito da ita,jumong nata cewa"gudnyt sir" amma baibi ta kansa ba,saman kujerar ya cillat yana huci,shi kansa bai san me yasa yake jin wani fushi ba don ta bata hakanan yake jin wani tashin hankali da bai ganta ba,cikin jikinsa yake ji kamar *ZATA IYA GUDUWA* wataran tace zata barashi, Saman kujerar ya dora qafarsa yayin da ya sauke dayar a qasa yana tsayw gabanta,kukanta har yanzu take ci gaba da yi harda dan sautin sheshsheqa,hankalinsa gaba daya ya rabu biyu ,hukunci sosai yake son yayi mata saboda kada ta sake fita har ta bace agaba,yayin da qamshin turarenta keta rar aba masa hankali,ya kasa komai kukanta na ci gaba da shiga kunnuwansa,hannu ya dunquke ya daki kujerar da suke kai "keep quiet"ya fadu cikin tsawa,hannu tasa ta rufe bakin nata hawaye naci gaba da silalowa ,ya dage girars yana fadin"kiwa mutane laifi kuma ki sasu a gaba kina masu kuka?ko don kinga bakinki yafi nawa iya