← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 84

Sashe 78

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

cikin ruwa nan ta jefa aslam ci........" Kafin ta qarasa fadi tuni ya tsunduma ciki cikin wani irin nau'in tashin hankali,minti biyu kacal ya ciro yaron, Suna tsaye cirko cirko Fadila na rungume da Muslim Hawaye ne kwance male male bisa kuncinta ,yayin da Islam ke a Hannu Samira,salima kuwa na tsaye tana bari kamar wadda aka sheqawa ruwan qanqara a tsakiyar hunturu,tuni fits ri ya gama bata ta,Kallon da aliyyu yayi mata yasa a take wata gudawa mai dumi ta balle mata,zuciyarta ta nemi tarwatsewa saboda tsananin tsoro da razani *Mrs Muhammad ce [1/29, 9:51 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?........* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 3* 3 Wani lafiyayyen mari ya sakar mata wanda yasa jinta da ganinta ya dauke na wucin gadi sai gata ta zube a qara warwas Babu numfashi ko alamarsa a tattare da aslam,hankalinsu idan yayi dubu ya tashi,asibitin doctor sa'adah tana masa gyare gyare saboda haka suka wuce kai tsaye d shi *get-well women and children hospital* dake rijiyar zaki,asibiti ne mai kyau saboda haka suna Zuwa aka rufu.kan yaron,sun kasa zaune sun kasa tsaye,Zuciyar Fadila tayi rauni matuqa,qauna da tausayi irin ta da da mahaifi ta dinga taso mata,Hawaye ne kawai ke sintiri kan fuskarta ta kasa controlling din kanta,tana jin wanne irin laifi ta yiwa salima har haka da zata yi mata irin wannan hukuncin?,me ta state mata a duniya?,don kawai sun hada miji daya?,Samira ce mai dan bata baki Aliyyu kam bai ma tantance a wanne halin yake ba,mintina talatin doctor ya fito,d sauri suka tunkareshi Tun kafin ya kai ga qarasowa "Doctor ya ake ciki?" Ya danyi Jim sannan yace"saidai Kuyi haquri,munyi iy bakin qoqarimmu,amma Allah bai qaddara........" "Doctor! Doctor!, numfashinsa ya dawo"cewar daya Daga cikin nurse din,da azama likitan ya juya ya koma cikin dakin,Kasa jurewa aliyyun y yi ya riga masa baya *Zakaran da Allah ya nufa da cara* cikin ikon Allah suka samu ya far fado numfashinsa ya daidaita,nan suka bashi gado dakin mutum daya,kafin lok tuni salima ta jima cikin cell Duk Wanda ya zo dubiya sai yayi mamakin rashin imani irin na salimar,domin ana zaton wuta ne a maqera sai aka sameta a masaqa,tuni jikin samira yayi sanyi matuqa,Duk iskancinta abunda salimar tayi yayi Mutuwar dau4e mata kai,don a zahirin gaskiya ba zata iya koda kwatanta hakan ba Lokacin da salima ke musanta abinda ta aikata aliyyu baice komai ba,na'urar c.c.t.v din ya dauko,inda take Adana bayanan ta ya shiga,tiryan tiryan har shigowarta cikin dakin ta bayyana har yunqurin shaqe muslim,wannan ya zama hujja mai qarfi a gurinsa,mataki mai tsauri ya dauka a kanta,inda yasa aka sakaye ta babu Wanda ya isa ma y je ganinta,babu yanda iyayenta ba suyi da shi ba yasa a fito da ita ko kotu ne suje akan ajiyar da yasa aka yi mata amma yace ina bai da lokacinta,koda zaiyi shari a da ita a yanzu ma to sai yaronshi ya warke,don Tun ba yauba take yin yunqurin kisan kai tun Daga kan 'yarta iftihal ya tabbatar ita tayi poisoning din fadilar a baya,ya sake gasgata hakan fada masa da Samira tayi ganin da ta yi mata a bakin window din fadil ,ya sake hada hujjarsa da irin firgicewar d yaga tayi lokacin da yake Sanar da haihuwar fadilan Tun suna bashi umarni cikin gadara har suka dawo lallashi amma fir yaqi sauraronsu sai suka dinga biyowa ta gun Momi da suka fuskanci abun na yi ne, "Babu ruwa na don bani na Haifa musu dan ba,haqqinsu ne ba na wa ba"haka ta sanar da su,suka yita Neman uncle abba da suka ga babu nasara ta bangaren Momi to shi b ya qasar ma ya tafi turkey duba company dinsa na yin carfet dake can Duk wuni gu Wanda suka San za'asa aliyyu ya fidda salima sunje amma abun yaci tura *sawun giwa ya take na raqumi*,ba su da dukiyar da zasu kara da shi,bai bari an saketa ba sai da yasa tayi attachment na wata uku cikin gidan yari ,zama ne na azaba da aiki mai tsanani,ta Fige ta palace kai Baka ce Salimar nan bace,nan ma cewa yayi shari'a zasu fara uncle abba yace ya barta hakan ma ko don 'yarsu iftihal,Kuma Allah ai ba azzalumin bawansa bane,zai musu sak walau a duniya ko a lahira Cikin station din da aka dawo da ita ya barsu,yana shirin bude motarsa ta tareshi,yaja da b ya saboda wani shegen tsami da take bugawa,ta zube a gabansa tana ya yafe mata sharrin shaida ne" "Ta riga ta wuce,idan ba hakan ba ai da baki isa ma ki tsaya haka a gabana ba,Kuma shaidan din dake zugaki kinga ai Abu yayi kyau kenan ko?,abinda zan baki shawara kada ki kuskura ki sake yin gaba da gaba da ni,idan tak darki ce kuma already na danqawa d.p.o babu Kare bin damo" Kafin ta sake ce wa wani Abu tuni ya shige motarsa ya bule mata idanu da qasa ya wuce abinsa,a take a nan ta sul le ta fadi sumammiya ,bata tashi farkawa ba sai a gadonn asibiti,ta farka tana surut i da buge buge "Ni aliyu zaiwa haka akan Fadila da tsinannun yaranta?,to wlh sai na dau fa "sai da aka zurkuda mata allurar bacci aka samu sa'ida *** *** *** *** Rayuwar gidan ta soma sauyawa,wata nutsuwa ce ta zowa samiran, son yaran take sosai,Tun Fadila na Dari Dari har ta s kar mata jiki,cikin lokaci qanq ni tad fuskanci babu abinda ya cuci samirar illa tsantsar jahicin ilimi addini da sh idanun lqawaye dake zugata,amma baya ga haka bata da wata illa Aliyyu kam ya daukewa Samira wuta matuqa da gaske,don yace it ma bai yarda d ita ba,Mara baki ma ya aikata ina ga mai baki,kuka ta dinga yi masa tana rantsuwar wlh ko kaza ba zata iya k shewa ba,har tausayi ta bawa fadila,ta dinga masa mita kan ya dain yi mata haka,ita ta sashi ya siyowa samirar littatt fan addini ta samu lokaci tana karanta mata,tun daga kan su ahlari,qawa'idi,iziyya,arba'una hadith,umdatul ahkam,usulus-salasa dadi makamanta su qananu wadanda za suyi mata sauqin fahimta *_SHIN MENE MAKOMAR RAYUWAR SALIMA ANAN GABA?_* *_SHIN YA RAYUWA Z TA KASANCE TSAKANIN SAMIRA DA ALIYYU?_* *_RAYUWAR GIDAN ZATA DORE A HAKA_* *_amsar sai 'yan mutan huguma,kuci gaba da haqurin bibiyarta mun kusa da yardar Allah_* *Mrs Muhammad ce [1/29, 9:52 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.......* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 3* 4 Cikin ikon Allah ta soma fahimtar rayuwar da take abaya rayuwa ce mai cike da jagwalgwalo da qazanta,tabbas rashin ilimin addini ciwo ne da bashi da magani,makanta ce da ka iya yima mutum jagora Zuwa ga halaka,haka nan duk ilimin zamanin da ba'a hada nemansa da na adidni ba sunansa kwado ko Kuma ince jahilci,sannu sannu kuma zai iya kaika ga ramin da zaka gaza fitowa,ilimin dadi ni gaske ne da kullum yake zamowa dan jagora ga rayuwar bani adam
Chapter 78 · 0% Book details