← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 84

Sashe 3

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka gayan"ya qyalqyale da dariya yace"anty ke dai ba dama mutum yayi hira dake sai kice ya dameki shi yasa yaya farida ke burgeni ke halin ya ahmad kikayo kun fiya kwafsawa wlh,ta harareshi sannan tace"ai da itan da kai duk zamuce ta tadda mujemu idan mutum baiyi surutu ba baya burgeku,kada Allah yasa mu burgekun muyita kwafsawar,idan ka qara magana kuma sai na saukeka anan" take ya rufawa kansa asiri yayi shiru Taso makara saboda ajiye muhammad da tayi don ita ta saba da wuri take zuwa don ta samu sit din gaba,bata da wata qawa bare ta tarar mata hakan ya jawo batayi parking din motar ta daidai ba ta nufi ajin cikin sauri Lacture din ta daukesu awa uku har da mintina,kanta ya dauki chargy sosai,don haka da fitowarta ta samu wani guri dake nesa kadan da ajinsu bashi da yalwar jama'a sosai yafi kusa da inda suke ajjiye motocinsu idan sunzo,gurine mai wadatar shuke shuke ita kuwa ma'abociyar son tsirrai ce [8/8, 3:24 PM] LOADING...... gun na burgeta saboda son tsirran da take dashi,tamkar a cikin iska ta ke jiyo qamshinsa,gabanta ya tsananta faduwa,ta gefan ta ya wuce saidai bayansa kawai take iya gani,ahigar suit ne a jikinsa masu dan karen kyau da sheqi,kayan baqaqene sai tsintsiyar hannunsa da ta gani wadda yake daure da agogon fata baqi,gefansa wani ne ke biye da shi riqe da takardu da brief case,sam sai ta kasa dauke idanunta daga kanshi ,hakanan gabanta yaci gaba da faduwa cikin zuciyarta take fadin inna lillahi wa inna ilaihir raji'un"har ya danyi nesa da ita sai taga ya waiwayo,cikin wani irin sauri ta dauke kanta tayi wani sashen da shi zuciyarta kamar ta tsinke ta fado,ganin yayi gaba tayi hamdala da Allah yasa bai lura da ita ba,tana tsammanin jikinsa ne ya bashi ana kallonsa ,a sace taci gaba da kallonsa har ya bacewa ganinta,taja ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kallon hanyar ta jawo jakarta ta zuge ta fiddo da wayarta tana danne danne,ta doshi kusan minti aahirin a gunbtana hutawa sai sannan ta tuna zata fa gidan ya ahmad,da sauri ta miqe tana gyara yafen gyalenta,atamfa ce ajikinta dinkin riga da skirt ne,atamfar England ce dark green mai ratsin yellow,sai mayafinta da takalminta agogo da jakar hannu duk yellow,fadila ba qarya ta iya daukan wanka don duk munin atamfa takai aka mata dinki ya saka komai kushe da hassadarka baka isa kace batayi kyauba haka Allah ya bata wannan baiwar,tana tattare komatsanta tana sanyawa a jaka taji ana kwada mata kira,a nutse ta dago tana neman daga ina wannan kiran mafarautan ke fitowa?,wata class mate dinta ce binta auwal fadila taci gaba da binta da kallo har ta qaraso,"fadila abbas yaufa kinyi tabargaza"abinda ta soma cewa kenan,fadila tace"kamar ya fa?"tana dubanta tace kinyi wrong parking kin toshewa A.s mai tama hanya"ta sake dubanta cikin rashin fahimta tace"waye haka kika bi kika rude?'binta ta zaro ido tace"kar dai kice min baki san a.s mai tama ba,hadadden guy din da duk nigeria bama kano ba ansan da zamansa"fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"na gode"taci gaba da mayar da kayanta jaka Iya dube dubenta ba wanda ta gani sai mutum daya ,a tsammaninta idanunta ke mata gizo,sai dai har ta qaraso gun shi din dai ta gani,yana tsaye hannayensa harde a qirjinsa fuskarnan a murtuke,ta qaraso ne da niyyar bashi haquri sai dai lura da irin kallon qasqancin da yake mata mata yasa tayi banza da shi kai tsaye ta nufi motarta ta bude,ta zauna a seat din tana qoqarin jan murfin ta rufe taji an dafe murfin motar,ta dago ta dubeshi,yana tsaye yana mata irin kallon dazun,cikin qasaita taji yace"baki da ladabin bada haquri ga wanda kika aikatawa laifi?"duk da yadda zuciyarta ke sake ninqaya a zuciyarta,muryarsa mai sanyi ta kwanta a zuciyarta,amma ta dake gami da cewa cikin zuciyarta"duk da dumbin qaunar da nakeji taka a zuciyata hakan bazai sa na bada girma da jan aji irin na 'ya'ya mata,ta dauke kanta sannan tace"ai shi wanda akawa laifin baisan darajar bil'adama ba"ya saki murfin motar hadi da watsa hannayensa yace"ok,ba laifi"ya saki murfin motar,cikin wata iriyar gaggawa taga ya amshi key din tasa motar daga hannun wanda suke tare ya bude motar sa ya shiga cikin gwaninta ya take motar ya kurda ya matse motar fadilan ta yadda itama bata isa ta fita ba harsai da ya gogeta,ya kashe motar ya zare maqullin ya rufe motar ya fito yana cilla maqullan yana cafe wa ya danyi tsalle ya haye bayan motar ya zauna,da hannu ya kirashi yadan yi masa rada ya amshi tak ardun hannayensa shi kuma ya juya da sauri ya bar gun Sarai fadila ta fahimci abunda yake nufi saboda haka ta zaro wayarta ta nemi number farida ta kirata"hello farida kin shigo school?"tace"eh ya akayi?""kizo ina parking space ki daukeni mu wuce"farida tace"me ya sami motar ki?""kinga idan zaki zo kawai kizo malama""ok sister gani nan" Cikin 'yan mintina sai ga farida horn tayi mata ta miqe ta fito ta kulle motar ta gabansa ta shige ta nufi farida,dai dai lokacin ta jiyo saukowarsa daga bayan motar,wata yar qaramar mota ce tayi parking a gabansa kusan tare suka shige motocin,ta madubin motar farida suka hada ido ta sakar masa tsaki hadi da murguda baki,cikin zafin nama ya balle murfin motar ya fito da sauri tacewa farida"yi sauri ki bar gurinnan,tamkar kuwa tasan meke faruwa ta figi motar ta bar gun Muje zuwa [10/16, 12:21 PM] Salma Wa yasan gobe? Safiya Abdullahi musa huguma Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata"gidan ya ahmad fa zamu"ok" inji farida,"sister wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?"taja tsaki tace"wani dan rainin hankali ne yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci ba"ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe ma juna hanya da sukayi,me farida kuwa zatayi idan ba dariya ba,"kefa 'yar wulaqanci ce shi yasa ban fiya saki cikin lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye suka nufi falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar bafullatana,tana ganinsu ta saki fara'a cikin barkwanci tace"lallai yau baquntar tamu ce"suka saki dariya dukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu cikin kulawa tana tana tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro packet na chaculet tace gashi injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema anty?""tace yau ai ranar school ne suna can amma suna hanya don bala ya tafi dauko su,""na manta wlh"ta fada tana qoqarin kwanciya bisa doguwar kujera"anty hafiza tace"ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin lafiyar kujer?"fadila ta dan murmusa tace " anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake ji""na miki"inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace"qyaleta anty muje na canjeta yau tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na ceceta ba""tab wucenan wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita? ""fada mata dai anty "cewar fadila,suka shige kitchen nan suka barta a falon Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S mai tama binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da zuciyarta,"to me A.S mai tama take nufi?"A dai duk inda aka zaga farkon sunansa ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya subuce mata sai tunaninta ya dawo kan abinda ya faru tsakaninta dashi dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunnenta,kyawawan idanunsa yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace lokacin data murguda masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,"lafiya kuwa?"ta tsinci muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace"lpy lau me kika gani?"farida ta dan tabe baki tace"hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta fara soyayya"da sauri fadila ta kalleta tace"lallai yarinyar ni kikewa wannan titsiyen?to gyada na zama na soye qarewar soyayya"anty hafiza dake zaune saman kujera bata sa baki ba sai yanzu tace"um um yaya fadila wannan fa sign ne na falling in love "fadila ta miqe daga kwanciyar tana cewa"kai anty,please kada ki biyewa shirmen farida,ita 'yar sa ido ce komai ta gani idonta na kai,kuma sai ta sanya ma question mark ",ta gyada kai sannan tace " alright idan tayi wari maji,Allah yasa alkhairi ne""amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty",nan gidan suka wuni har 'yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su kadaine jikokin gidan nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya ahmad ya dawo ya tarar da su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu turarurruka. to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S maitama,duk da ta danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a duniya,koda bazai iya shaidata ba bare tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari da taje school bai janye motar tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya cire,a gida tace ne kawai tana tana garage ana duba mata ita Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa da wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma'aikacin gidan radion khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar. cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa da riganshi wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta maqala qananun fashion na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai madauri sai mayafi data yafashi a kafada bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon gashinta ta qasan daurin,jakarta ta dauka 'yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar hannu ta feshe jikinta da turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da ita,farida dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta"gsky yaya fadila kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki kama mita bayan
Chapter 3 · 0% Book details