Sashe 33
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
3 Kusan kimanin minti biyar idanun nata na lumshe ta kasa budesu saboda wani abu da takeji a jikinta wanda tasan baya rasa nasaba da tsan tsar kishi,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bude idonta ta dora su bisa screen din wayarta tana ci gaba da qoqarin kammala bude account nata na Facebook duk da wani bari na zuciyarta na ci gaba da mintsininta,cikin zuciya lallai ta godema Allah da bai qaddara ta zubda ajinta ta bayyana abinda ke zuciyarta ba har ta kai aliyyu ya fuskanta bare ta samu nata kason cin zarafin kwatankwacin wannan wanda it may break her heart Tabbas ta sake yarda cewa so masifa ne musamman son da hausawa kema laqabi da son maso wani,babu irin baiwar da tabbas bata da ita iya kyau Allah ya mallaka mata shi ilimi hankali da nutsuwa,tasha jin mata yan uwanta da yawa na yaba ta bare tarin maza dake kara kaina a kanta Ta sake satar kallon nasa wannan karon maimakon ta tadda shi yana aiki kamar dazun yanzun takardun na watse ne a gabansa ya jingina kansa harda bayansa a jikin kujera dukkanin tafin hannunsa ya tallafe bayan kansa da su idanunsa na rufe,gashin idonsa yayi ma idon rumfa tamkar an jera su "Bani abinci"ya fada idonsa na a rufen,ta miqe ta shirya masa komai still dai idanunsa na arufen har ta gama ta koma ta zauna,a hankali ya bude idonsa ya kalli warmers din"u mean ni zan zuba kenan da kaina?" ta girgiza kai sannan ta taso ta zuba masa white rice ce da miyan kaza sai hadin coleslaw tana kammalawa ta miqe da niyyar fita "ina zaki je?"ya tambayeta cikin izza,ta kawar da kanta sannan tace "sashina zan koma" yaci gaba da cin abincinsa sai da ya mula don kansa sannan yace "ban baki izini ba"cike da haushi da takaicin irin mulkin da yake mata ta koma da baya ta zauna kanta a qas Cin abincinsa yake with calmness ba abunda ya dameshi ya shanyata abunsa,har ya kammala bai dubi sashenta ba already ta soma gundura da zaman ga bacci ya soma mamayarta ga kuma fita office gobe early,sai da ya kammala duk abinda yake har ayyukan da yake shigarwa cikin laptop dinsa apple sannan ya tattare kayayyakinsa ya maida jakar laptop din yana shirin shiga bedroom dinsa yace da ita"ki hadomin coffee ki kawo min" Kamar zata fashe da kuka ta shiga kitchen cikin mintina biyar ta hada masa ta juye cikin cikin wani set din butar shayi irin na larabawa na silver da cups dinsu yake hade da tray Hade da sallama ta shiga dakin yana cikin lallausan bargonsa cikin shirin bacci ba haske a dakin sai na fitilar gefan gado,yana receiving call har ta shigo ta isa bed side ta dora plate din daidai lokacin da ya kammala amsa wayar ya kasheta gaba daya ya cillata bayansa tana tsaye har ya kammala addu'o'in bacci sannan ya juya mata baya yana gyara kwanciyarsa hadi da jan bargonsa "kina iya tafiya" dama a gundire take Allah Allah take ta bar masa dakin ta juya ta fice abinta Tana shiga bedroom dinta nightgown kawai ta sanya ta fada gadonta tana addu'o'in kadan kadan har ta gama,a hankali ta lumshe idonta tana da muradin yin bacci amma ina sai tunanin da akullum yake zame mata na qarshe a rayuwarta shi ya lullube qwaqwalwarta,duk yadda taso bacci yayi awon gaba da ita abun ya faskara har sai da ta dade tana ninqaya a duniyar qaunar aliyyu haidar sanan baccin yayi awon gaba da ita bacci ne mai cike da mafarke mafarken aliyyun Cikin hukuncin ubangiji rayuwar ke tafiya da bawa wani lokaci ta zo maka uadda kake so kake tsammaninta wani lokacin kuma ka samu akasin haka yau fari kenan gobe tsumma jibi nasara gata asara duk cikin hukuncin ubangiji ne da yadda yaso rayuwar bayinsa ta kasance,to bawa mai cike da tauhidi da imani sai ya godewa masa don kamar yadda haka yake ga fadila,shekararta guda kenan cikin igiyar auren aliyyu,shekarar da ta ga abubuwa daban daban ta fuskar qalubale da nasara Zamu iya cewa babu wani abu da ya sauya dangane da salon mu'amala da alaqa dake gudana tsakaninta da shi baya ga wadda muka riga muka sani,nasara daya ce zata iya daga hannu ta fadeta cike da alfahari shine duk cikin samira ko salima babu wadda take iya sarrafawa aliyyu girki da tsaftar muhallinsa kamar ita Abunda suka fi qwarewa ciki sune kowacce ta fito tana tunqaho da hura hancin Aliyyu yafi sonta akan sauran 'yan uwanta,takan kau da kai cike da yakanah tayi kamar bata san abinda suke yi ba,wani lokacin kuma sukan bata dariya har ma ta murmusa takan daukesu ne a matsayin wadanda basu san mai ya kamacesu ba duk da kuwa duk sun bata wasu shekaru sun kuma girmemata sosai tana ganin tutiya bata kamacesu ba a irin wannan rayuwa da suke,ta sanu da gayya suke mata wani abun ganin cewa bata taba daga ido ta kallesu ba bare suyi 'yar tankiya So suke ta zamo daya daga cikinsu domin kuwa fada tsakaninsu sun koma tamkar 'ya'yam tumaki har bangarenta tana jiyo hayaniyarsu,sukan ji kasiririt ne idan aliyu yana gida don ko giyar wake suka sha a yanzun basu fada gabansa tun tuni yayima tufkar hanci ya kuma tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta kuma ji din saidai su yita 'yan habaice habaice wadanda shi da yake namiji me bai ma fuskantar me suke Ta riga tuntuni ta saddaqar da cewa soyayayyar aliyyu wani gine ne daga Allah cikin zuciyarta,tayi imani koda bai sonta ba koma zai sota din ba kamar yadda yayi mata tunqaho Allah bazai taba wofintar da ita darajar biyayyar aure da take hidima a gareshi da kayutata gami da girmama buqatunsa,duk da babu wani sauqi da take ganowa a tattare da aliyyun amma har kulluma tana bawa kanta confidence kan hidimar da take masa especially a duk sanda haduwa ta hadasu da uncle abba momi abbanta ko umminta taga yadda suke nuna jin dadinsu har yau da wannan aure nata sai taga zata iya ci gaba da faranta ransu indai hakane Saidai abinda bata sani ba shi kansa yakan samu kansa cikin nutsuwa a duk ranakun da suka zamo nata ne ko banza ya san yana sakewa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma cike da gamsa shshen dan dano irin wanda yake so duk da babu ruwanshi da ita,some times ma kafin ya dawo ta hada duka abinda yake so ta bar masa bangaren,mutum ne aliyyu maciyin abinci bao wasa da cikinsa ko kadan hakanan halittarsa take,duk qwaqwar mutum bai isa yayi indication wasu sign da zai nuna yana jin dadin hidimarta ba Mrs muhammad dinku ce [8/25, 3:45 PM] +234 812 673 9684 : 5:08 pm 20/08/2016 *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *PART 2* 5 Cikin watannin da basu gaza biyar zuwa shida ba fadila ta samu gagarumar nasara ta bangaren aikinta,nasarar da bata taba tsammanin zata sameta in a few months ba,ta soma aikine cikin sa'a,farin jini sosai take da shi,sunanta ya fara fantsama cikin al'umma shirye shiryenta sun samu karbuwa matuqa da gaske,ki ina ka zaga zancan matashiyar 'yar jarida fadila Abbas wakili ake,ita kanta tana mamaki with her few age ta samu daukaka haka,saidai da yake mai hankali ce takan godewa Allah domin tasan babu wanda ya isa yayi mata haka sai Allah,hakan yasa ta sake daura damarar riqo da aikinta cikin qwazo amana da kuma gaskiya da kuma manufa kyakkyawa da zata kawo gyara da ci gaban al'ummarta,bata mantawa da ya ahmad da abbanta wadanda su suka jagoranci samuwar ci gaban nata Bayan ta kammala duk wasu ayyukanta kamar yadda ta saba,ta shirya masa komai hatta da tissue bata barta ba,sauri take ta yi ta fice daga gun kafin dawowar tasa,saidai kash bata ci nasarar hakan ba don kuwa a bakin qofa suka yi kacibus kadan ne ya rage basu bige juna ba,da sauri taja da baya tana shaqar numfashin ta dake gudu sakamakon tsoratar da tayi,qasa tayi da kanta tana murza tafin hannunta gami da cewa "sannu da zuwa" Kusan minti biyu taji shiru shi bai wuce ba ba kuma alamun juyawa yayi,ita kuma ya bashi dama ne ya fara wucewa duk da sauri da take ta koma bagarenta ta cire pad din jikinta ta sauya wata,ta dago kanta don taga me yakeyi ne haka yana tsaye hankalinsa kwance kamar bai tsarawa kowa hanya ba don bashi da wani alamu na matsawa hasalima tie dinsa da coart yake cirewa a nutse Ganin haka yasa ta raba gefansa don ta shige ashe bata sani ba ya sanya mata qafarsa dake saye cikin sau ciki sam bata lura ba don hankalinta yayi gaba,luuu tayi baya ya goce sai kuwa ta bugu da qofan falon ,cikin azabar radadi ta dafe gun ta dago a hankali ta kalleshi sai taga tamkar ma baisan mai yayi ba agogon hannunsa na gucci yake cirewa,malolon takaici ya kama mata maqogaro tuni kuka ya kufce mata tasa kai tanashirin bar masa gun tana dafe da goshinta Ji tayi ya jawota baya ta dawo tayi kamar zata sake faduwa Allah ya taimaketa ta tsaya da qafafunta bayan taga tagar da tayi "sama fa qasa ya kalleta sannan yace " baki da kunya ko?,ni zaki buge ki wuce kenan?"tafin hannunta tasa ta kate fuskarta tana ci gaba fa kukanta shi kuwa ya zuba mata ido ba tare da ya sake cewa komai ba, sai da ya gama ikon nasa don kansa ya kauce tare da wucewa ya bar gurin Da gudu ta fice tana ci gaba da kukan ta wuce bangarenta,dispenser ta kunna tayi heating gurin sannan ta koma bisa gadonta ta kwanta tana maida ajiyar zuciya,me ta masa?ma ta tsare masa banda tsabar cin zali kawai don ta rabe zata wuce sai ya mata wannan muguntar?" Ta danyi qwafa kadan a ranta tana ayyana zata rama Su biyar ne zaune cikin office din fadilan sai fauziyya fa'iza aisha da halima dukkaninsu abokan aikinta ne matasa ne son saidai duk sun girmemata aqalla zasu bata shekaru uku zuwa hudu,amma nutsuwa da kaifin hankalin fadila yasa ta saje cikinsu suna jin dadin zama da ita sosai duk da miskilace saidai akwai karamci da