← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 84

Sashe 46

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana gain yadda yake ta mutsu mutsu cikin ranta take munafuncin haka yake wai baccinsa ne shi,tun tana kallonsa har bacci ya rufe idanun nata,taso tayi daddan bacci mai tsawo a a lokacin saidai saidai hakan ya gaza samuwa don ta tashi yakai sau nawa saboda rashin sabo duk kuma tashin da zata yin idanunta na kan aliyyu sau uku tana ganinsa yana canza gurin kwanciya ana hudu ne ta ruskeshi yana qiyamul laili tuni ta miqe don ita din ma lokacin tashi yin tata sallar yayi Aliyyu na bisa darduma yaga tashinta a zatonsa fitsari zata yi sai yaga bayan ta fito ta tayar da sallah shi da zuciyarsa yaje gulmar isha'i ne bata yi ba kota tsammaci asuba ce tayi?,shi kadai ke kida da rawarsa ita kam ta kafu gaban ubangiji,har ta idar idanunsa na kan fejin qur'anin dake hannunsa yana karantawa yana shafin qarshe ne cikin suratu anbiya'i,kusan yare suka sake miqewa suka tada sallar asuba kowa yayi tasa,yana so ya samu falalar jam'i sai dai girman kansa bazai barshi yayi mata tayi ba,bata jima da soma azkar dinta ba bacci ya sureta ko gamawa bata yi ba Sanda ta farka ta duba agogon dake ajjiye kan side drawer tayi mamakin yawan baccin da tayi,ta yunqura da niyyar tashi sai ta ganshi shima kwance kan abun sallarsa yana baccinsa cikin nutsuwa da alama shima surarsa yayi bai shirya ba kamar yadda yayi mata,ta dan zubawa kyakkyawar fuskarsa ido wanda da idonsa biyu bata isa ba ,fuskatsa tayi mata kyau tayi wani fresh,ta dan girgiza kai ta miqe tsaye ta soma gyara gadona a nutse cikin taka tsantsan don kada ta sheshi sai da ta kammala tayi mopping ta wanke bandaki duk da baiyi komai ba ta sake kintsa falo,ta koma ta buda jakarta ta fiddo da turaren wuta ta jona abun turaren wuta mai amfani da wutar lantarki ta zuba cikin qanqanin lokaci gidan ya dumame da qamshi har ya leqa moqata ma,cikin sanda ta koma dakin gadon tayi saurin shiga wanka tun kafin aliyyu ya farka ta kasa sakewa Shigar shadda tayi pink dinkin riga da skert ne sun mata cif sun zuna das ajikinta babu inda yayi kwarara kai ka rantse a jikinta aka dinka su,hida lip glosses sai kwalli kawai ta saka ta taje dogo kuma baqin gashinta ta kameshi da ribbon pink,ta ware dankwalinta tayi daurinta na zamani wanda ake sokeshi(ture kaga tsiya)hakan ya bawa jelar gashin nata damar zubowa ta qasan daurin,rigar sanyi ce wadda ko ciki bata rufe ba mai gashi dogon hannu ne da ita ita ta sanya light blue,ita kanta sai da ta juya ta sake kallin kanta duk da ba wani make up tayi ba amma ta zuba kyau ta dauko turarenta ta shafe lungu da saqo na jikinta,har ga Allah tana jin dadin qamshin turaren yayi mata ta maida shi sannan ta koma kitchen din shirya break Mrs muhammad ce [10/16, 1:56 PM] Salma *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* Tun acikin baccin ya soma jin qamshin na ratsa qofofin hancinsa,duk zuqar numfashi daya da zaiyi yana zuqarsa ne tare da qamshin,qamshin yayi masa,tun yana tsammanin ko amafarki ne har ya soma gasgata cewa a zahiri ne ido biyu ne,sannu a ahankali idanun suka ci gaba da buduwa ya soma zagaye dakin da idanun nasa ,ko ina fes sai qamshin turaren wuta ke tashi da na wannan turaren nata da har yanzu ragowar qamshin bai bar dakin ba Komai na dakin a kintse neat " I like it" ya fada can qasa,hakan yakeso ko da wani lokaci area din da yake rayuwa ta kasance,ya dan miqa hannunsa ya jawo wayoyinsa da ya dora kan center ya duba agogo,lokaci ya gani ya ja sosai din kuwa qarfe goma sha daya agogon china qarfe shida agogon gida nijeria,ya duba call logs nan ya tadda missed call na mr lin,babban dan kasuwa ne dan qasar china saidai sananne ne a qasashen duniya hakanan yana da companies anan gida nijeria sai missed call din andi biyu sai na salima guda biyar da ya biyo baya,duka baiji ba don a silent wayar take mantawa ma yayi bai kasheta ba don baya kwana da waya a bude saida babban dalili A hanzarce ya miqe ya watsar da fulallukan da yake kai ya nufi toilet,as usual tun a gida a nan ma haka ya tadda ruwan wanka ready cikin bathtub shigewa yayi kawai abinsa,mintina talatin ya kammala wankan a gurguje ya fito ya shirya kansa cikin baqaqen suit harda baqar safar hannu saboda sanyi sunyi matuqar haska farar fatarsa yayi kyau kamar wani bature tabbas aliyyu badai kyau ba Da hanzarinsa ya wuce kitchen kai tsaye kamar yadda ya zame masa aladarsa shan ruwa cup guda da safe kafin yaci komai,tun daga falon qamshin girki ya marabceshi,hancinsa ya bude sosai yana sheqar qamshin son ransa ,cikin kuzari ya qarasa kitchen din tana tsaye gabn gas tana kwashe chips don shi kadai ya rage mata dama ta kammala,bayanta yake bi da kallo tayi kyau kamar wata 'yartsana don kayan sun mata cif cif ajiki ya bi gashinta da kallo wanda ke reto a bayanta sai ya tsinci kansa cikin birgeshi da hakan yayi don shi kam ma'abocin son gashi ne tun yana qarami,ya dauke idonsa ya maida kan freezer bayan ya budeta yana jawa kansa kunne Sam bata san da shigowarsa ba qarar rufe freezer din ita ta ankarar da ita,ta dago ta dubeshi yana shirin ficewa ya dan lumshe idanunsa sanda yake qoqarin barin kitchen din saboda feeling da yake ji sosai irin na jiya da ya hanashi sukuni da bacci mai dadi,bata ce komai ba ta biyo bayansa,har ya samu hannun kujera ya zauna numfashinsa na fita da sauri da sauri,cikin hanzari ya balle hancin gorar ruwan ya kai bakinsa ya soma daddaka Bai ajjiye ba har sai da ya shanye tas ya wurga robar cikin dust bin dake kusa da shi yana maida numfashi bayan ya rufe idanunsa "Your breakfast is ready"yaji muryarta kusa da shi tana fada,a hankali ya bude idonsa bai ganta ba don tuni ta wuce sai ragowar bayanta da ya gani sanda take qarasa shigewa kitchen,bai sake komai ba illa wucewa dining da yayi don gwada cin abincin Ta zuba masa komai hatta tea ta hada masa a cup ya sanya cokali yana motsa shi,mamakin kanshi yake yana kuma tambayar kanshi *meke faruwa?* da shi,ta fito daga kitchen hannunta dauke da dan qaramin cup data hada black tea ta zauna cikin falon tana kurba a hankali qamshin ne yaci gana da buwayarsa ta hanyar iska dake kado mishi shi Ya maida hankalinshi kan tea dinsa yana kurba kadan kadan,comfortably yake jin zamansa kan dining din shi daya,ya debi chips da pork ya kai bakinsa yana ci gaba da monitoring movement dinta da idanunsa,"hey" taji yace ta dago da kanta ya dan dago hannunsa ba tare da ya dubeta ba"come here"ya kirata sai taji ban barakwai,ta ajjiye cup din hannun nata a hankali ta qarasa dining din,ya sake kurbar tea din idanunsa na kan ruwan tea din da yake sha "sit" yace da ita,ta ja kujerar gami da kasa kunne tana sauraran mai zaya ce mata Bai ce komai ba har ya kammala breakfast dinsa,qamshin da yake ji ne ke rudashi ya rasa wanne irin mayen turare take amfani da shi ya zaro tissue daga cikin tissue dice box yana dan goge hannunsa inda ya bacin "as from today kada ki sake kawomin abinci ki bar gun har sai na kammala understand?"(nikam cewa nayi hmmmmm,fadi gaskiyarka na daure.......) "mutum sai shegen mulkin tsiya ba haka nake masa ba a nijeria wani lokacin bai taba cewa don me ba sai yanzu?wato zai fara fidda sabon salo don yaga ba'a gida muke ba"cewar fadila ita da zuciyarta,a fili kuwa gyada kai tayikata na a qasa "hey" ya sake cewa ta dago ta dubesa ta sake sadda kai "open ur mouth u r not a bruise" to tace masa cikin qosawa da zaman Har ya ja kujerarsa baya yana niyyar tashi don ya tabbata ya sake qara wasu mintina a gaba bai bar gun ba tabbas bazai iya mallakar kansa ba,abunda yake ji a cikin gangar jikinsa is very strong feeling,yana so yace ta daina amfani da perfume nata amma girman kai ya hana, yana ganin idan ya fadi mata zatayi tsammani ya damu ne da wani abu nata,he feel he can sustain whatever zaici gaba da ji,wayarsa da ta soma kadawa cikin tattausan ringing ita ta dakatar da shi daga tashin da yayi niyya Mrs muhammad ce [10/16, 1:57 PM] Salma *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* Ya ciro wayar ya duba mai kiran ya dan saki ajiyar zuciya kadan sannan yayi pressing ok,sunan da taji ya ambata ya sata gane da wadda ya ke wayar,salima ce,hira take yi masa sosai yana dan biye mata,hirar da tasa fadila kasa jure zaman gurin ,satar kallonsa take ta qasan ido gaba daya launin idanunsa sun canza muryarsa ta sake zama so cool Idanunsa na kan fadila lokacin da ta miqe don basu guri don zuciyarta ta samu salama daga mugun kishin dake taso mata,ya dan daki table din da hannunsa wanda yasa fadila daje shirin sauka juyowa suka hada ido da shi,fararen idanun nan nasa da sukayi returning zuwa ja ya lumshe su sannan yayi mata alama ta koma ta zauna,kamar ta zura da gudu tabar gurin haka taji saidai ba yadda ta iya ta koma din Minti biyu tsakani yayi sallama hadi da kissing wayar sau uku,lumshe nata idanun tayi tanajin wata dalmar kishi na digar mata cikin zuciyarta,bata bari shaidan ya kitsa mata komai ba ta soma karanta *hasbunallahu wani'imal wakil*,wani gumi ta gani yana tsatstsafo masa ya maida jikinsa ya jingina sosai da makarin kujerar idanunsa a rufe wani weakness yake ji sosai cikin jikinsa ya dauki aqalla minti goma sha biyar a haka kafin mood dinsa ya dan saisaita ya dinga sakin 'yar qaramar ajiyar zuciya a jajjere,har a lokacin fadila na satar kallonsa tana mamakin meke damunsa haka mood dinshi yayi bala'in canzawa within few minutes,ya sauke doguwar ajiyar zuciya lokacin da yake bude idanun sa,caraf ya kamata tana kallonsa sai yayi wani kicin kicin da rai yana
Chapter 46 · 0% Book details