Sashe 13
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani sabon bikin suke sakewa,ba bainda auke illa aikin dafa abinci da kade kade,shiba wannan ne damuwarsa ba hayaniya ce baiso sam ko kadan,musamman wannan lokavi da tun daren jiya zuciyarsa ke a cunkushe,lamarin na taba ransa sosai yanayin da ya samu samira a daren jiya tun daren bacci ya qauracewa idanunsa,yaja siririn tsaki a ransa yace"wai duk haka matan suke ne?"bashi da mai bashi amsar tambayarsa don haka ya nufi sashensa Damuwa ita ta haddasa masa gajiya da kasala ya zauna bisa kujera ya miqe duka qafafunsa kan kujerar ya hardesu yasa hannunsa na dama yana shafar sumar shi,tunani ya masa yawa ya rasa da wanne zai fara,yana a haka yaji knocking kafin ya nada izini har ta shigo,tafiya take tana wani karairaya kamar mai ahirin tsinkewa ta kafa masa ido tana murmushi,sam ko kusa bata burgeshi ba hasalima wani tsanarta da baqinta yake gani,ta haue kujerar da yake kai kamar zata koma cikinsa"sweet aly ina ka shiga tunda ka kawo kayan abinci ka fice"ya dauke kansa yana qoqarin janye jikinsa yace"na koma kasuwa ne" Ta dan bata fuska ganin yadda yake nuna kamar yana qanqyaminta tace"haba sweet wai meke damunka tun daren jiya fa ma lura da sauyawarka,bayan wannan lokacimmu ne da ya kamat ace mun moreshi,pls kada ka bari wani dan qanqanin abu ya tarwatsa mana jin dadin wannan lokaci da muka dade muna tanadin zuwansakada ka lalata mana suitable moments dimmu"kallon da ya watsa mata shi ya firgitata ya kira sunanta da wata murya da ta qara razanata "Kin dade da wargaza farincikin wannan lokaci tuntuni da hannunki"ta dan zaro ido cikin duniyanci tace "kamar ya wai me ya faru?"ganin tana shirin raina masa wayi yasa ya.miqe gami da jan tsaki yace"ni zaki mawa silly question irin wannan?"ta kama gefan rigarsa tana shirin kecewa da kukan kirsa tave"din Allah ka gayamin me na maka?",ransa tafasa da suya kawai yake,ya dawo da baya yana huci ya ranqwafo kanta tamkar maiahirin fadowa kan nata har tana jiyo hucin numfashinsa,ya ware sexy eyes dinsa soaai a kanta wadanda bata san suna da girma ba haka miuyarsa a shaqe yace"u mean bakisan kinyi loosing virginity dinki ba,u did not know u r not a virgin!! A ina kika bada kanki samirah!!!"ya qaraahe cikin qaraji saboda wani kishi dake sukarsa, Wani kuka ta rushe masa da ahi harda dora hannu a ka kasancewar tasan halinsa baisan kuka ko da na yaro ne qarami yanzu zai dameshi,gunji take sosai hakan yasa temper dinsa ta fara raguwa,ya koma da baya ya zauna sosai,ta qasqantar da kanta tamkar wadda zata masa sujjada ta muzanta sosai,ta tsara masa qaryar fyade aka mata tun tana qanqanuwa"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"ya dinga mabata ahankali har yaji zuciyarsa ta fara sanyi duk da wani bangaren na zuciyarsa ya kasa gasgata labarinta,ya amince haka qaddararsa take,shi kam ya sani bai taba koda kusantar zina ba bare ya aikata ta amma Allah ya jarabceshi da samun mata har biyu da suka zo masa babu budurci,harda matarshi ta fari "Ya isa,is ok "yace da ita,"hakan baza ta sake faruwa ba"yaci alwashin hakan,ta ruqunqumeshi tqna ta zuba godiya xikin zuciuarta tana godewa allah da asirinta baitonu ba don bazata iya jure rashin aliyu ba,baiga alamun tayi wanka ba don haka ya tambayeta,ai kuwa ta narke murya tave"na manta yadda ka koyan jiya da daddare"cike da madaukakin mamaki yake kallonta mace yar kimanin 25yrs amma ace bata iya wankan janaba ba ya koya mata ta kasa daukewa ?tun asubar jiya kuma tana zaune da janaba ajikinta bata damu ba to ina ga ban sallah kuma?ya jin jina kai yana hamgo girman aikin da ya sameshi,duk kuma yawan yanuwanta da sukazo a rasa wanda zai kwatanta mata harkar gabansu kawai suke,ya fuskanceta sosai ya sake koya mata ,nan toilet dinsa yasa ta shiga bai barta ta fita ba sai da yaga ta kammal ta kuma rama dukkan sallolin dake kanta Tofa masu karatu muje zuwa Mrs muhammad bello [10/16, 12:30 PM] Salma Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Har magariba fadila na bisa kujerar ta kasa tashi,kudin da ya jiye mata na gefanta tafa ce ta dubu dubu guda biyu,tasa hannu ta sake juya kudin a karo na barkatai "nafi buqatarka Aliyu fiye da kudinnan fiye da komai ma,me zaniyi da kudi"ta raya haka a ranta,kiran sallar magariba da aka qwalo a masallacin qarshen layin shi ya kawo qarshen zaman dirshan din da take,wanka ta soma dama ita gwanar sa ce don wani lokacin farida kan tsokaneta da agwagwa sarkin wanka ta hado da alwala bayan ta fito ta sa hijab ta gabatar da magrib sannan ta zauna tana azkar tana kuma jiran kiran isha'i Minti arba'in tsakani ta jiyo kiran isha'in saboda haka ta tashi ta bada ita ta kammala da addu'oi ta shafa sannan ta isa madubinta dake cike da kayan kwalliya,kwalliya ta yi mai qayatarwa bata hauka ba mai cika fuska da yake ba baya bace gurin kyau sai kayi tsammanin bata lokaci tayi gurin yinta ta amsheta sosai ta kuma dave da yanayinta,ta bude duk sif dinta ta zuba mata ido tana tunanin wanne kaya zata saka?,hankali take shafa su har hannunta ya kai kan wani material Pink ne mai adon dark blue da dark green din zare da golden sai wasu dutsuna da aka caba ado da su masu sheqi suma golden colour,dinkin doguwar riga ne da mayafinsa material din yake zuwa,yana da sulbi da taushi ba santsi ba yana shaking kadan a jiki don haka da tasa sai yabi jikinta ya lafe ya kuma haska kyakkyawar chaculet din fatarta fashion na dutse ta dan madaidaici ta maqala a kunnenta sai siririyar sarqarsa data lafe a dogon wuyanta sai zobe blue shima qwaya daya da ta saka a yatsan tsakiuar hannunta,ta shafe jikinta da tutaren asaal da ahlamul arab tame suka gauraya suka bada wani daddadan qamshi mai sanyi ta zura plate shoe pink ta dau mayafin kayan ta nade kanta da shi Sannu ahankali tame ratsa gidan sai yanzu ta qarewa gidan kallo ita kam ya burgeta tsarin sosai,tamkar kana turai,ta sauke ajiuar zuciya sanda zuciyarta ta raya mata dama ita da Aliyunta ne kadai ke rayuwa cikin gidan rayuwa kuma irinta soyayya cikin takun nutsuwa ta nufi qofar da zata sadata da bangaran nasa ido ta saki tana kallon ko ina,tako ina bangaran nasa yafi naau kyau da tsaruwa sosai,tun daga varender dinsa take jiyo sassanyan qamshinsa,ta shiga falon a nitse falone da ya tafi da gaba daya tunaninta tamkar gadar shugaban qasa,haduwarsa da tsaruwarsa tafi gaban kwatance Idanunta suka sauka kanta tana hakimce kan kujera tana fuskantar t.v tana sanye ne da riga body huge da wando na jeans wadanda suka mata dam dam,ta baza kitson attachment din da aka jibga mata aka har gadon baya,fara ce sosai don har wani kore da yalo gefe da gefan fuskarta yake tabbacin kaso saba'in cikin dari na farin nata ya qara shi ne da man kanti,tana da jiki amma ba can ba da alama nan gaba kadan ta samu hutu zata narja qiba ne,tabbas ba don farin da ta aro daga kanti ba kana mata kallon farko zaka saka ta a sahun muna na amma sai farin ya boye kaso hamsim cikin dari na munin nata Fadila ta sake jadda da sallamarta a karo na biyu sai Aliyu ne dake zaune bisa step kan dining ya amsa yayin da samira tayi saurin dago idanunta tana kallon mai shigowar idanunta suka fada kan fadila wani faduwar gaba taji amma ta maze don bata son fadilan ta fuskanci ta razana da ganin da ta mata,maimakon haka ma sai ta mata wani kallon raini na sama da qasa sannan ta janye idanunta ba tare da tace kanzil ba Bata ma lura da kallon ba tana qarasowa cikin falon ta yiwa kanta matsugunni bisa tattausan carfet din da ya malale dakinta jingina jikinta da kujerar dake bayanta,wani abu ke tsunkular zuciyarta game da kishi duk da ta godewa Allah da ta tarar samirah bata fita da komai ba sai farar fata don ta tsammaci aliyu zai so matar da ta fi samira ne ba kamar samiran ba cikin ranta take cewa lallai so hana ganin laifi,to ganin samiran ko sashen da take bata kalla bayasa itama ta dauke mata kai sai ma ta zaro wayarta ta shiga latse latse To shima Aliyun sai da ya kammala abinda yake ya shiga bedroom dinsa ya dan jima sannan ya fito ya samu kujera daya ya zauna ai kuwa tsam samira ta bar gurinta ta dawo jikinsa ta lafe kamar mai shirin komawa cikin sa ta gefan ido take satar kallonsu wani abu mai daci na damunta,amma a haka idan ka kalleta sai ka rantse da Allah batasan Allah yayi ruwansu ba don bata fasa danne danne a wayarta ba Da bismillah ya fara yayi salati ga fiyayyen halitta yaja dogayan addu'oi wandabhar samira ta fara nuna masa tafa gaji,fadila ita mamakin yadfa Aliyu ke zuba addu'a take tamakar ba daga bakinsa suke ba(hmmm fadila kenan bakisan waye Aliyu bane )ya kammala sannan ha shafa,ina godiya ga Allah bisa ni'imomi da ya yimin a rayuwata tun daga haihuwata har kawo yau,ya kalli samira yace ga abokiyar zama nan Allah ya qaddara tare zan aureku sai kj zauna lpy bana buqatar hayaniya ko tashin hankali a gidana kowacce ta kama kanta ta tsaya inda Allah ya ajjiyeshi.... Ya dan sarara sannan yace idan da mai magana bismillah ya koma ya jingina da kujera yana jiran cewarsu,samira ta saci kallon fadila tana jiran taga zata tanka sai taga ma Sam idanunta bai kansu ta aza su ne bisa carfet,ta gayara zama cikin iyayi da kisisina tana kuma yatsuna tace"to nidai bana son shishshigi kuma bana son raini ehe.....kuma kowa ya kwana lpy shi yaso,sweet banji kayi rabon kwana ba?"ya daga kafada yace"its un 2 u ai"tayi wani fari da ido tace"zamu raba kwana dai dai ne yayi aiko?"ta tambayeshi ya sake faga kafada yace taakaninku ai nikam ban iya yawon bin bangare bangare ba,"hmmm shegen girman kan tsiya"fadila ta fada a zuciyarta,duk da idan ka kalleta zakayi tsammanin bata tare da su,yauwa sweet ina kuma da buqatar masu aiki do.....cikin dakiya ya tari numfashinta,ba'a gidannan ba ,inji aliyu,ta narke murya,please sweet pls mana"bani