← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 84

Sashe 5

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunani naka yayi kyau qwarai da gaske,domin samun nagartacce kamar Aliyuna a wannan zamanim abune mai matuqar wuya qwarai da gaske,fadila'yar ka ce halak malak kuma ko wani kaso bata wlh zaka iya bashi bate aliyu,na bawa aliyu ita har abada abokina"alh salim yace"a'ah abokina kada kayi saurin yanke hukunci ba tare da kaji ta bakin ta ba ka bari su gana taga idan har yayi mata"alh abbas yace"haba salim Haba salim yaya zaka ce haka bayan kasan yarinya budurwa ubanta ne ke da ikon zaba mata mijin aure ballantana duk yaron da zata zaba mawuyacine yakai nagarta da ingancin aliyyun,ai magana ma ta qare dama dab suke da kammala attachment dinsu nafison ace da zarar sun kammala su tafi dakunansu" Alj salim yaji dadin maganar yace"amma fa wani hanzari ba gudu ba,akwai yarinyar da aliyun zai hada su ya aura tare,to ya kamata a sanar da ita kasan yaran yanzu basa son abokiyar zama kaga ya kamata ta sani kafin ayi"alh abbas yayi dariya yace"shirmen banza ne iri na 'ya'yan yanzu zan sanar da ita kada ka damu,bamu buqatar duk wasu kaya na bidi'o'i"alh salim yace"a'a kaima ka sani momimta haj maimuna ba zata yarda ba yadda za'a yiwa dayar itama sai an mata"suka sa dariya gaba dayansu cikin farinciki,cike da godiya bisa karamcin da amininsa yayi masa"alh abbas yace ka daina godiya da Aliyu da fadila duk daya ne a gurina"alh salim yace"na sani amma duk da haka godiya ta zama dole duk wanda yayi ma jininka kyautar da sukutum da guda ai ba qaramin masoyi bane,cikin girmamawa da mutuntuna juna sukayi sallama Safiyya(mra muhammad bello) [10/16, 12:22 PM] Salma Wa yasan gobe? Safiyya Abdullahi musa huguma Cikin daran alh abbas ya sanar da mai dakinsa,tayi murna qwarai don tasan amincin dake tsakanin mazajan nasu da irin tarbiyyar dake gidan alhj salim,sai dai tace wani hanzari ba gudu ba alhj ba lallai yaran su so junansu ba fa?,abba yayi dariya yace"duk soyayyar yqnzu shirme ce,ina soyayyar take zuwa?daga anyi auren ta mutu sai ki rasa ranar da tayi musu,wani auren hadin ba yafi qarko da albarka ba,ga auremmu ya isheki misali sai da aka kawo ki muka ga juna ko kin manta,gashinan haryau shekara kusan talatin da biyar ba fada bare yaji"ya dan kalleta ta sigar tsokana yace"nasan dai abu daya kikayimin kin shanye ni na kasa qaro miki abokiyar zama"kunya ta kamata tadan rufe fuskarta da tafin hannunta tana cewa"kai alhaji"shina dariyar yayi yana bude mata fuska yace"ai gaskiya ne" Misalin goma na safiyar washegarin ranar alh salim da kansa ya sanya aliyu a gaba ya tuqoshi zuwa gidan aminin nasa alhj abbas don kawo sadakinsa,aliyun yayi kyau abinsa cikin shadda gezna dinkin tazarce farace qal sai maiqo take,ya saye idanunsa cikin farin glass wanda bai hanaka tozali da farar qwayar idanunsa,takalminsa baqi ne na kamfanin batozi sai baqar hula duk da bai sanya ta ba tana riqe ne ahannunsa,kana nazaratar fuskarsa zaka karanci damuwa a tattatare da shi,sam alh salim bai bi ta kansa ba don yasan kwanan zancan,ya sani cewa gata ne yake son ya yiwa aliyun wanda ko bayan ransa zaiji dadinsa. A nutse yake murza sitiyarin motar har suka iso cikin gidan,alhj abbas da kansa ya fito yayi ma abokin nasa iso zuwa cikin gidan bayan sun gaisa da Aliyu suka barshi cikin motar,ya dan kwantar da kujerar motar yayi rigingine yana kallon yanayin ginin gidan, Alhj salim ya fiddo da daurin bandir na dari biuar biyar rafa daya ya ajjiye a gaban alhj abbas yace "ga sadakin aliyu ga 'yata fadila"alhj abbas yace "amma ai a yimin kara ko ni na biya ai"alhj salim yace"ni da kai ai duka dayane babu komai wlh"alhj abbas yace"Allah to ya yiwa auren albarka yasa ya zamo farinciki a gurimmu da gun yaran gaba daya""ameen"ya amsa masa"auren zai kama nan da sati shida dai dai lokacin da zasu kammala attachment dinsu"alhj salim yace"anya ba'ayi gaggawa ba?""wani irin gaggawa kuma me zasu zauna su yimin agidan ?"to shikenan abbas Allah yasa ayi a sa'a""amin dama ban sanar da yarinyar ba niyyata dama yau ta sani amma munyi zancan da mahaifiyarta,to tunda ga sadakinta ga kuma mijin sai a kirata tasan komai""to ba laifi"inji alh salim Tana ysaka da baccinta taji ana dukan saman qafafunta,ta daga kanta idanunta cime da bacci tana kallon muhammad da ya tashetan cikin jin haushin tashin nata da yayi tace masa"meye?,ba nasha gaya maka idan ina bacci ka daina damuna ba"ya hade hannayansa yace"am sorry anty,abba ne ke kiranki""abba kuma? "ta ta tambayeshi cike da tsoro saboda ta tuna agender su,ya gyada mata kai cike da tabbatarwa,tace jeka ina zuwa"tuni ragowar baccin da take ji ya gudu daga idanunta,ta dirgo daga gadon ta shige toilet ta wanke fuskarta tayi brush sannan ta dawo cikin dakin ta daura zani kan rigar baccin ta ta fesa turare sannan ta zira zumbulelen hijabinta mai hannu,a falo taci karo da umminta tana saka turaren wuta,ta gaidata sannan fuskarta kamar mai shirin rushewa da kuka tace"ummi wai abba ke kirana"ta kalleta tace"to kije mana na ganshi da alhj salim"gabanta ya qara faduwa ta juya ta bar falon A salube tayi sallama a sitting room din,dukkansu suka amsa mata,ta samu gefan kujera ta gaida uncle abba(hka suke ce masa)kasancewar sun gaisa da abbanta tunda asuba,uncle abba ya amsa yana mai qara nazaratar nutsuwa da ladabinta,abbanta ya kalleta yace"fadila ina son ki bani aron nutsuwa da hankalinki "tace"to abba ""kin sani cewa shekarunki sun isa ace kina dakin mijinki tunda an aurar ma da wadanda basu kaiku shekaru ba,sannan na baki dama ki fito da wanda kikeso kamar yadda qanwarki ta fiti da shi amma har yanzu baki cemin komai ba,na qyaleki har lokacin da nabaki ya qare ban tanka miki ba duk da cewa ina da iko in zaba muku miji amma na baki damarki "ta gayada kai "hakane abba yace"fadila"ta amsa "na'am""abbanki ya nemawa yayanki aurenki kuma na bashi"wata mummunar faduwar gaba ce ta risketa tamakar an daddaure jijiyoyin jikinta taji,hakan yasa ta kasa dago idanunta ta kalli kowa bare su fahimcin halin da ta shiga,ya dora da cewa "yanzu haka ga sadakinki a hannuna"jin hakan yasa ta qarasa rikicewa sauran dauriyarta tuni tayi qaura,addu'o'i ne barakatai suka dinga zuwa bakinta tanayinsu cikin zuciyarta,shikenan na rasa aliyuna?shikenan zuciyata ta rasa muradinta?shikenan mafarkina ya zama hasashe?,abinda take jujjuyawa kenan kawai a zuciyarta,duk maganganun abba ba wanda ta ji ko ta fahimta sai maganarsa ta qarshe wadda sauran qiris ta sa numfashinta ya dauke"kije kuga juna yana falon waje duk da shekarun baya kun sanshi amma saboda tsawon shekarun zaki iya mantashi ya kwana biyu baya qasar"uncle abba ne yayi saurin cewa"a'a saurara ina da magana ke fadila gayamin gaskiya idan bakiso kina da wanda kike so"tabbasa da zata iya da ta fayyace musu sirrin dake zuciyarta ko zasu tausaya mata su bar zuciyarta taji ma da masifar da take ciki,amma ko kusa batajin zata iya kunyata abbanta,bayan ya isa da ita yana da iko da ita fiye da yadda take da iko da kanta yayi mata komai a rayuwa ya bata dama masu yawa a rayuwa irin wadda kowane mutum ke son samu,duk ma a ture wannan gefe baza iya daga iso ta budi bakinta tace da aminin mahaifinta wanda yake tamkar uba a gareta cewa batason dansa jininsa ba,hakan yasa tayi saurin girgiza kai tace"ko daya abba na gode da zabin da kukayimin,Allah ya saka muku da alkhairi"ita kanta ta jinjinawa kanta kan namijin qoqarin da tayi na furta haka,uncle abba har zuciyarsa yaji dafi matuqa tare da sake gode ma allah da zata zamo daya dqga cikin ahalin gidansa,albarka suka sa mata sannan abbanta ya umarceta taje su gana Takai kusan minti biyar a qofar sitting room din ta kasa shiga,gaba daya a rude take zuciyarta a cunkushe take,daga qarshe taga tsayuwar batada wani amfani don haka ta tattaro dukka nutsuwarta da dauriyarta ta kutsa kai hade da sallama kanta a qasa ta lalubi kujera daya ta zauna cikin fargabar wa zata daga kai ta gani,muryar da taji ta masa mata ita ta razanata da sauri ta dago kai ta gani ahin da gaske ne ko kunnuwanta da zuciyarta ke yaudararta yadda suka saba?idanunsu suka hadu da juna wanda hakan ya tabbatar mata da tsammaninta,ba qaramar razana tayi ba duk da bata nuna hakan ba,A.s mai tama Aliyyun uncle Abba?,take ta jera sunayan a zuciyarta,komai tsaya mata cak yayi,tunaninta ya kasa gaba ya kasa baya,shiru daki ya dauka ba wanda ya tankawa dan uwansa wanda hakan ya sanya fargabarta daduwa,bata kuma sake kallonsa ba bare taga a wane irin yanayi yake ciki ba,sun jima a haka sannan ta jiyo alamar miqewarsa,har ya kai bakin qofa yayi taku uku ya dawo da baya,kallon nan nasa da ta fari gani a qwayar idonsa ta kuma tsaneshi shi yayi mata sama da qasa sannan yace cikin izza da qasaita"ban iya qarya ba kuma bazan fara taba saboda ke,bazan iya tafiya ban amayar da binda nake ji cikin zuciyata ba,bakimin ba baki dace dani ba,baki ma dace da tsarin rayuwata ba,ke da kanki shaidace ce idan dq zaki iyq yiwa kanki adalci bamu dace da juna ba,baki ma da zubi da tsarin da nake so gun mace,idan banda tsaurin ido ma irin naki taya zaki hada kanki da ni?kinga nayi kala da ke?gaskiya kin cuceni,god forbid ki zama matata,kada kuma ki soma yaudarar kanki ta hanyar zato ko tsammanin nan gaba zan iya sonki harki cuci kanki ki aure ni,wannan maganan daga cikin zuciyata direct take fitowa Wani mugun takaici da baqinciki ne lokaci guda ya rufeta,tunda take babu wani da namiji da ya taba mata munanan furuci makamanta wannan,ta tuna uawan samarin da ke kara kaina a kanta,samari masu ji da kudi kyau nasaba isa da qasaita,ba wanda ta bawa dama a cikin su,wasunsu dama suke so ta basu koda ta friendship ne amma basu samu ba,samari da dama sun sha kuka a gabanta kan ta mallaka musu zuciyarta,amma yau wani daya daga cikin jinsin maza ke gaya mata wadannan kalaman,ji take a rqntq matuqar ta barshi ya tafi haka ba ta da ta mayar masa da martani ba wanda zai dade yana cizon zuciyarsa ba to ba shakka tayi faduwar baqar tasa"hey "tace da shi sanda ya sanya kai
Chapter 5 · 0% Book details