Sashe 47
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ganin kamar tasan meke damun sa,sunkuyar da kai tayi shi kuma ya zark handkerchief ya share ragowar zufar fuskarsa Sauka yayi a ahankali daga dining area din ya shige bedroom,tana zaune a gun ya sake fitowa wannan karon yellow and coffe din suit ne ajikinsa da alama kaya ya canza koma wanka yayi ne oho wa yasan masa ,hannunsa riqe da brief case yana amsa wayar mr lien a hanzarce yake tafiya ya sanya hannu ya bude pocket din sa ya zaro yuan dari ya ajjiye mata(five thousand kudin naija) kana ya dago suka sake hada ido dukkaninsu sunji jiki ita ta sunkui da kai shi kuma ya fice a hanzarce,ta kalli kudin ta tabe baki "ne me zanyu da kudin qasarsu?tabdijan" ta fada a fili amma qasa qasa kamar mai gunguni Yana fita lukas da andi na qofar gida cikin motar kamfaninsa da yake shirye shiryen budeshin *maitama group of companies* haka yake kowa yasan da su,da fitowarsa suka sara masa kamar wani soja sukayi handshake kamar yadda yake a al'adar sa don dabbaqa value ba addininsa a ko ina yake,lukas ya bude masa qofar zungureriyar motar ya shiga suka rufa masa baya Driver din ya bawa umarnin yabi ta lujing road huangtian street zasu fara shiga yueyang hotel yana son ganin ramzan dan india ne wanda yana daya daga cikin wadanda ya bawa contract na ginin factory din nasa,factory ne babba na qashin kan aliyyu wanda ya narkar da maqudan kudade gurin samar da shi,factory ne da zai dinga manufacturing kayan babies blouses na maza da mata Wunin ranar cikin zirga zirga mai yawa yayi ta ahiga can fita nan,hakan ya taimaka masa sosai gurin rage masa abinda yake ji cikin jikinsa,yayin da a daya bangaren fadila ta wuni kwanciya sai bayan ta idar da sallar la'asar sannan ta shiga kitchen,pepe chicken couse couse da miyar qwai sai mutuminta lemon kwakwa da ya wadatu da madara da flavour wannan shine jadawalin abincinta na dare Nan da nan ta gama kasancewar gas din nata mai hudu ne,ta turare gidan nata da turaren wutanta bayan ta zuge duk wani glass da window dake gidan,sai gidan yayi wani dumi mai dadi daya gauraye da qamshi,cikin ruwa mai zafi sosai tayi wanka saboda sanyin dake damunta na garin,riga da wando tayi shirya kanta ciki wandon dogone har qas pencil rigar kuma da kadan ta rufe cikinta jacket ta saka mai kauri ta mata wanda ta sauko har qasan gwiwarta tana da dogon hannu sai manyan maballai guda shida masu fadi da aka jera daga gaban rigar kusan sune kadai adonta,rigace da yawanci a turai matansu ke amfani da ita musamman lokacin sanyi Gashinta ta gyara sosai ta kamashi da band ta saya socks qafa da hannu ko zata samu sauqin sanyin,da turarenta ta shafe jikinta ko ina ciki da waje,ta maida ta tattare abinda ya dan yamutse a dakin ta gyara shi sannan ta ciro jakar laptop dinta da sam ta manta da ita ta cirota tasan saqonnin email na nan na jiranta jingim ta dauki wayarta ta dawo falo Sai da ta zauna sannan ta duba agogo don ganin ko lakacin sallah yayi don bata tsammanin akwai masallaci anan inda suke tun da tazo bata ji kira ba da agogo kawai take amfani ko dazun ma sauran kadan sallar azahar ta qwace mata,lokaci kadan ya rage lokacin sallar ya shiga don haka sai ta jona chargy na laptop din nata sannan ta zira hijabi ta shimfida dadduma ta tada salla Bayan ta kammala ne ta ninke hijabin hadi da daddumar ta maida daki sannan ta dawo kan computer din tata,aikam ta tarar da saqonni masu yawa anty hafiza sumayya rabi'ah na sister farida ne akan gaba harda pictures din baby humaira masu yawa har da na ya ahmad ragowar kuma duka na masoya ne na gari dake qaunarta ,na 'yan uwanta ta soma dubawa kowanne na tambayarta ne sun iso lafiya? Da makamantansu,dai sai taji kewarsu ta cikata take ta shiga maida masu amsa lallai duk wanda yabar gida gida ya barshi,sai data gama da su sannan ta soma duba na sauran jama'a wanda ke da muhimmanci ta maida masa amsa mara amfani ta goge shi A hankali ta daga kai karo na farko ta duba agogo,tara da mintina goma sha biyar,duk da cewa unguwar da haske ta dan soma duhu alamun dare ya soma kenan wasu sun kashe qwayayensu "me ya tsaida shi tun safe har yanzu?" Fadika kewa kanta wannan tambayar da ita kanta bata san amsarta ba,fargaba ta dan soma shigarta da tsoro lokacin da idanunta ke ganin kamar ana gilmawa ta cikin balcony dinsu,ta miqe a dan tsorace ta maida hijabinta bayan ta zare computer din daga jikin socket ta maida daki ta dawo falon ta tayar da isha'i Har ta idar babu aliyyu ba alamunsa,zama tayi kan daddumar jiki a takure,kewa ce sosai ta kamata,ita ba layin qasar cikin wayarta bare tayi kira,a gogon ta sake kalla ya nuna mata qarfe goma da minti biyu,tsoro ya sake shigarta musamman da taji unguwar ya sake yin shiru ba komai ke tashi sai haushin karnuka da keta kai kawo Dif wutar gidan ta dauke gaba daya,gabanta yayi wani matsanancin bugu yadda duhu ya mamaye gidan ko tafin hannunta bata iya gani,tuni jikinta ya soma rawa ta dunqule guri guda tsoro ya mamayeta haushin karnukan sai take jinsa kamar a qofar gidan Bata san sanda ta wuntsila tayi bayan kujera ba jin haushin karen a bakin qofar falon hadi da tsaiwar mota wadda aka yiwa full light aka dallare gidan gaba daya daga baya aka kashe,ai bata san sanda ta saki kukan tsoro ba dumin hawayen kawai itama taji,cewa take shikenan na banu,kusan minti biyar sannan ta daina jin motsin karen,zama tayi dabas a qasa hadi da dafe goshinta da tafin hannunta,kuka sosai ta saka,tana bala'in tsoron kare arayuwarta,don duk gidan da zata matuqar suna da kare to komai mutuncin da kuke tafa bar zuwarmuku kenan daman yaya lafiyar kura,yana daya daga cikin abinda yasa bata saba da gidansu aliyyu ba bata zuwa kenan da can suna da karnuka har biyu kafin daga bisani uncle abba yasa aka fita da su Sam bataji shigowa ba sai takun sawaye ta ji,a guje ta miqe tana neman mafaka a rude ,ji tayi an cafkota cikin duhun,ihu ta bude bakinta da niyyar yi ko da wanda Allah zai sa ya kawo mata dauki sai taji ansa hannu an toshe mata baki dai dai lokacin wutar ta dawo,fuskarsa cikin tata yake kallonta ya zuba mata qwayoyin idanunsa,fuskarta tuni tayi jage jage da hawaye jikinta sai bari yake don sai da wutar ta dawo ta gane ashe tuni har hular kanta ma ta cire saboda tsabar rudewa Ita ta fara janye idanunta hadi da kawar da kanya gefe ganin shi bashi da niyyar janye nasa sexy eyes din da ya zuba mata,qoqarin zame hannunta take har a lokacin kanta na gefe tana kuka mara sauti don iya tsorata ta tsorata,jikinsa a mace yake murus ga gajiyar zirga zirga da ya wuni yana yi tuni rigarshi ma ta saman ya cireta a hannu ya shigo da ita,yaqi sakin hannun nata yayin da yake qara zuba mata wani dafin mai illa ga ruhinta har cikin qwaqwalwarta don baisan me riqe mata hannun ya jawo mata ba,ta kuma rasa me yake yi a tsayen har lokacin don qeya ta juya masa idanunta bai kansa ta kuma qi kallonsa Gashinta yake kallo dake ta sheqi shigar ta karbeta sosai kamar yasa hannunsa ya shafa gashin saboda sha'awar da ya bashi sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi "zaka jawowa kanka raini" a hankali qamshin turarenta ya ci gaba da sakar masa da gabobi da qyar ya Iya dauke idanunsa yana jan tsaki cikin ransa yana jin haushin kansa Mrs muhammad ce [10/16, 1:58 PM] Salma *WA YASAN GOBE?..* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 2* Ji tayi an janyota baya an zaunar da ita saman kujera ta dago kai suka hada ido fuskarnan tasa kamar dai koda yaushe,ta sunkui da kai hawaye naci gaba da zuba,tana jin tausayin kanta ne cikin zuciyarta soyayyar aliyu ta gama yi mata illa,yana tsayen dai yayin da ya sauke dukka qwayoyin idanun nasa a kanta yana kallonta ita kuma kukanta take haiqan mara sauti lokaci lokaci tana sa tafin hannunta tan rage ruwan hawayen ta hanyar sharesu hadi da jan majina Kusan minti biyar sannan taga ya dora mata handkerchief saman cinyarta qamshin turarensa da yake jikin handkerchief din ya daki hancinta,briefcase dinsa ya dauka ya wuce daki,saman gadon ya fada yayi rigingine yayin da qafafunsa ke qasa hadi da cewa *"ya Allah"* Lokaci sosai ya bata yana maida numfashi tukun kafin ya miqe ya cire kayan jikinsa ya sanya rigar wanka ya wuce bandaki,ko cikin toilet din ma haka ya dade cikin bathtub kafin ya cude jijinsa ya fito,jallabiyya ya gani saka da short nikker gefan gadon a ajjiye bai kawo komai cikin ransa ba bayan ya tsane jikinsa ya shafa lotion dinsa sannan ta taje soft sumarshi ya feshe jikinsa da designers turarukansa ya jawo kayan ya sanya Har yanzun tana bisa kujerar saidai yanzu har jingina tayi lokaci lokaci ta na dan saki ajiyar zuciya irin na wanda ya sha kuka,kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa ita kam dama ko sashin da yake bata kalla ba don haushinsa take ji,sai da ya fara zuwa gun makunnin t.v ya kunna ya dauki remote ya qaro volume gidan talabijin dun qasar ne ke labarai ya maida remote din ya wuce dining,da kansa wannan karon yayi serving din kanshi sannan ya soma cin abincin,yaci abincin sosai ba tare d shi kanshi ya san yaci haka ba Tuni bacci ya dauke ya dauketa kafin ya kammala,ta takure kan kujerar kamar kwanciyar jariri cikin mamansa,ajiyar zuciya take saki kadan kadan cikin baccin,a hankali ya qaraso gabanta ya tsaya bayan ya kammala duk abunda zaiyi,ya zuba hannayensa cikin aljihun short nikker dinsa ya zuba mata ido "sleeping beauty" yaji zuciyarsa na fada,wata sha'awa matsananciya ta taso masa har wani yarrr yaje ji cikin jikinsa,ya tabbata da da salima yazo kai ko samira ce da tuni an wuce gun Itama ita gani yake kamar bada kaine ya tunkareta tunda dukkansu sun fita shekaru,ta sake jan