Sashe 54
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gashi fitar dole ta kamashi saboda yau baqinsa zasu soma isowa,dole shi zai kama masu hotel da zasu zauna andi kuma aikin da ya basu yayi yawa bare ya hada masu da wannan,ga mukhtar (abokinsa ne na kusa)bai qaraso qasar ba bare ya hada shi da aikin,don haka fiya ta kamashi dole,idan banda wannan dalilin kam baijin akwai abinda zai fidda shi daga gidan yau,ya gama shiryawa tsaf cikin suit kamar yadda ya saba sai da ya shiga kitchen ya hada mata tea ya zuba cikin flask ya soya mata chips da qwai ya hada da cups yayi dakin don kada ta tashi babu abinda taci,ya qaraso bakin gadon bayan ya ajjiye tray din kan 'yar locker din nan ta bedside yana sake kallonta,baccin take kawai ko motsawa batayi,shi kansa yasan dole ne kam tayi bacci,ya zira hannunsa a hankali ya sake maida mata gashinta gefe,karon farko cikin nutsuwarsa ya sanya tattausan lebensa ya sumbaci goshinta sannan ya maida leben nasa saman nata leben masu taushi da siranta,ya dan jima yana sheqar hucin numfashinta dake shiga hancinsa yana masa dadi yana jin kamar tana qara masa wata ruyuwar ne ta musamman Hot kiss ya bata wanda sai da yasa tadan motsa kadan ya miqe yana sake kallonta tare da hade tafin hannunshi da nata,baya son fitar ko kadan,ya sani tana da buqatar kulawa,sai da ya qoshi da kallon nata sannan can qasan maqoshinsa yace"i will back soon" tamkar yana magana da wadda ke idanunta biyu,ya fice a dakin yana waiwayenta hadi da ja mata qofofin gidan Cikin ayyuka yake da mutane saidai duk wani motsi da zaiyi qwaya daya tana manne cikin zuciyarsa,kaf hankalinsa na gida gangar jikinsa ce kawai a nan,har wasu abubuwan mancewa yake maimakon ya fadi sunansu sai yace "fadilah",sai kuma yace musu "am sorry I mean kaza.....",Allah Allah yake ya kammala abinda zaiyi ya koma gida saidai yana murna ya kammala sai kuma wannan ya bullo dole haka yake sake zama yayi settling Da kanta taji ta qoshi da baccin ta farka bakinta dauke da addu'ar tashi daga bacci *"Alhamdulillahil lazi aa faani fi jasady waradda alaiyya ruhi wa'a zina li bizikrihi"*,tayi niyyar miqewa kamar yadda ta saba saidai jin yanayin jikinta da ya canza shi ya tuno mata abinda ya faru da ita jiya tsakaninta da aliyyu Daki daki komai ke dawo mata,tana tuno moment din tar cikin kwayarta *"wanne turare kike amfani da shi?"* tambaya daya da ya maimaita mata ita sau biyu kenan a jiya,sannu a hankali tunaninta game da turaren ya soma dawo mata *"hasbunallahu wa ni'imal wakeel"* ta fadi cikin zaro ido da matsananciyar faduwar gaba,da sauri ta diro a gadon tuni ta mance wani ciwo da take,kai tsaye gun jakarta ta nufa inda taje rataye,tasa hannu ta cirota cikin rawar jiki ta soma laluben turaren ta ciroshi hadi da zuba masa ido tamkar yau ta saba ganinsa Da sauri ta daga jakar ta zazzage ta kafataninta,dukkayan ciki suka zubo,tarkacen magunguna da suka siya ne gun fa'iza,wannan turaren da nake shafawa shine?shine wannan turaren mahadin magungunan?" Jakar ta saki qasa hadi da komawa baya ta zauna kata ta dafe hadi da sakin wani irin kuka mai cin rai, _*"saboda sha'awa aliyyu ya tara da ita ba don so ba?turare shi ya ja hankalinsa kanta ba qauna ba?me yasa nayi gaggawar baiwa aliyyu kaina ne?me yasa na amince na yaudari kaina? Tabbas aliyyu bai sona kuma ta yarda bazai taba sonta din ba"*_,jikinta ne ya burgeshi ko me? Ta ci gaba da fada cikin zuciyarta,tuni ta gama sarewa,ta gama yankewa kanta qauna da zama tare da shi,babu irin abunda bata gwada ba amma babu nasara to sai yaushe?sai yaushe nasarar zata zo mata ne? Da gaske kenan hasashen anty hafiza na zai soki fadila wataran son da bai taba tsammani anawa wata diya mace irinshi ba,ai babu *wanda yasan gobe sai Allah* ya zama mafarki........?,tana jin wannan karon ya zama dole ta zare aliyyu daga cikin tsarin rayuwarta,ya zama dole ta rabu da shi haka nan ya zama dole ta nisanceshi,ta gama yin duk abinda ya kamata tayi.....ta gama duk abinda zata iya....ta gama bashi kuma duk wani abu da take da shi,kulawa.....tattali....tausayi da soyayya......kai harma da jikinta da zuciyarta gaba daya amma aliyyun ya gaza samuwa,to me yayi saura?,bata da wani ragowar abun bashi banda ta bar masa sararin rayuwarsa itama ko ta samu salama? Cikin azama tamkar ba mai ciwo a jiki ba ta hada kan kudaden(yuan) da ya jima yana bata su har take ganin basu da wani amfani a gurinta,ta bude locker da ta ajjiye passport dinta ta dauka,har ta juya tana shirin fita sai ta dawo da baya a hankali,ta yagi paper cikin takaddunshi ta dauki biro ta ja dressing chair ta zauna,tafi minti biyar da dora alqalamin kan takaddar saidai hawayen da ya cika mata ido ya soma diga kan takaddar ya hanata ganin komai,ta miqa hannunta ta yago tissue ta tsane hawayen sannan ta samu damar ganin ta,cikin kasala kamar mai ciwon 'yan yatsu hannayenta suka soma rubuta abinda ke qunshe qasan zuciyarta *amincin Allah a gareka* *duk da na sani cewa saqona ba wani abu bane da zai dameka ba,domin kuwa ina tsammani irin saqon da ka dade kana tsammani daga gareni* *aliyyu na soka irin son da ban taba yiwa wani halittar da namiji ba a duniya ba,na soka tun kafin na gama sanin wane ne kai,na soka son da ban yiwa kaina shi ba,na soka a fili na soka a boye* *saidai kash! Aliyyu ka qini qin da ban taba ganin ka yuwa wata halitta shi ba,ka tsaneni tsanar da na gaza canko mai na maka da zafi haka a rayuwa?,ka qinin ne kamar yadda ka fadamin gaskiyarka tun farko kace baka sona kuma ba zaka taba sona ba hakanan kada nayi tsammanin kuma cewa wata rana ko anan gaba zaka soni* *A lokacin na dauki zancan tamkar tatsuniya,na dauki zancen tamkar wani labari da wata rana zai iya shafewa ya gushe,ashe na tafka kuskure,nayi kuskure ba dan qarami ba,nayi abinda ni zan gushe ba zancanka ba,ashe ba zaka sonin ba har abada kamar yadda kace din,naji...na gani na kuma gamsu aliyyu...dama hausawa sunce jiki magayi,haka din ne ni ganau ce ba jiyau ba* *a yau na rabu da kai aliyyu kamar yadda kake bege....na fita a rayuwarka kamar yadda kake muradi.....,wata qila lokacin da kake karanta wannan saqo na dade da fita daga rayuwarka,kuma na yima alqawarin fita fita ta har abada.....koda sonka zai samo sanadiyyar daina numfashina a duniya,I promise I leave yiu forever......... *na sani ko ban roqeka ba abu ne mai sauqi in samu sakina daga gareka,to ina fata zata zamo rubuce jikin takarda don samun shaida ta kuma samu isuwa zuwa ga magabata na,na gode da jurar zama da kayi da halittar da baka so cikin inuwa guda.......na gode da da ci...sha.....suttura da ka dinga bani ba tare da zulunci ko gajiyawa ba thanks for everything,na gode na gode.... *fadila Abbas bashir* Ta ninke wasiqar cikin wani irin kuka mara sauti mai azabar cin zuciya da azabtar da rai,gefan pillow din da ta tashi ta ajjiye ta,cikin azama ta rataya jakarta ta fito hadi da jan qofar gidan,tana son koda sallama ne tayi da maqotan arziqi nadiya da mr lin amma bata son su fahimci wani abu har suyi yunqurin tsaidata,zuciyarta ta riga ta qeqashe duk radadin da ciwonta ke mata hakan bai dameta ba burinta kawai ta baf qasar,burinta ta fice a qasar ta china da take kallonta baqiqqirin Tana bayan taxi din ta ciro katin tana dubawa ta fada masa address din inda zai kaita branch ne na kamfanin ethopian airline taje ta fara rage bucking tunda tim din fitarta a qasar bai cika ba,cikin lokaci qanqani suka qaraso tace masa ya jirata yanzu zata fito Tana tsaye a gabansu cike da matsananciyar damuwa tana ta sharar qwalla,tsananta adsu'arta take ya Allah yasa ayau ta samu damar ficewa a qasar,burinta kawai ta nisanci aliyyun,bata son ta ganshi bare sonsa yasa ta karaya ta ci gaba da zama da shi,ma'aikacin dan qasar sin din na sake sauri gun duba mata jirgin da zai tashi yana sake bata baki cikin yaren English kasancewarsu masu girmamawa da tausayi ,cikin sa'a aka samu saidai zai sauka a ehopia kamar yadda aka saba sanann ya qarasa da su nijeria garin *kano*,sit daya ne ya rage suka gaya mata kudin da zasu cajeta suyi mata printing ticket?,cikin sauri ta gyada masa kai tun kan ya kammala printing din ta fito da kudaden ta ajjiye masa a gabansa,yana miqo mata da rawar jiki ta karba tana duba time da jirgin zai tashi awa guda ta rage mata *mrs muhammad ce* [10/16, 2:04 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 2* Da sauri ta koma gun mai taxi ta shige gidan gidan baya tana bashi umarnin su wuce airport,koda suka je kasa zaune tayi babu abinda take banda duba agogo hadi da sharar qwalla Da qyar aliyyu ya samu ya yage aiki da kuma jama'ar dake dakonsa,ya bawa jumong umarnin ya maidashi gida,cikin motar ya zaro wayoyinsa ya kira lukas yace kada a nemeshi ko menene ya taso shi ko mukhtar yayi handling dinsa,ya wuce gida ne madam ba lafiya,cikin girmamawa ya amsa masa,ya cire wayar daga kunnensa ya hada da wadda ke ajjiye kan cinyarsa ya kashe su gaba daya,ya zuba su cikin 'yar jakar laptop dinsa Jumong ya tsaida motar aliyyun ya fice,jumong din nata yi masa sallama amma hannu kawai ya iya daga masa ya shige gidan,fuskarta kawai yake da muradin kallo,ita kadai yake son gani,ta bashi wani abu mai tsada muhimmanci da daraja agun 'ya mace,ta bashi abunda ya kasa samu shekaru masu dama,abinda ya debe tsammanin ana samunsa gun matan yanzu,yana jinta sosai cikin jikinsa zuciyarsa ruhinsa...yana kuma jin wani matsayi da daraja mai girma nata cikin idanunsa Wullar da jakar tasa yayi kai tsaye ya nufi bedroom don yafi tsammanin samunta a can,yanayin yadda dakin ya dan yamutse ya danji mamakin ganin hakan,saboda bai saba gani ba ko tsinke bai taba katarin tsinta cikin kitchen dinta ba ballantana bedroom,to amma bai kawo komai cikin ransa ba sai ya dan ganta hakan da yanayin raahin jin dadin jikinta,saboda haka ya juya ya koma