← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 84

Sashe 67

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

masa kafin sallama, "ok gani nan"kawai yace mata ya maida wayar aljihun,fadila tayi lamo jikinsa kishi na sukarta,ya dago fuskarta yana kallo sai yaga alamun ta dan canza,yasan dalilin hakan saboda haka dadi ne ya kamashi don yasan abunda ake so ake kishi, "oya babe,give me"ya fadi yana sake dago fuskarta gareshi,wani hot kisses ta soma bashi wanda ita kanta bata san ta iyasu ba sai yau,sosai ta rudashi har suka gagara tsaiwa suka zube saman carpet,shigowar rabi'ah da komawarta da baya da sauri shi yasa fadila saurin zare jikinta,a kasalance ya maida idanunsa kanta,kanta a qasa tana tattare gashinta da ya yamutse tana maida shi cikin ribbon,ya sake maida idonsa bakin qofa inda rabi'ah ke tsaye a bayan labulan ta yadda yanzun bata iya hangosu "yaya,momi ce ke kiranka" "bace min a gun stupid kawai,baki iya sallama ba zaki shigowa mutane daki kai tsaye?" Sum sum ta juya tana tabe baki cikin ranta tana cewa "sallamar miliyan nawa kakeso nayi muku ,ka shiga wannan yanayin koda ganga nake sallama taya za'ayi kaji,su yaya aliyyu ashe haka aka iya soyayya?" Sai ta qyalqyale da dariya ita kadai,yasa yatsunsa ya dago da fuskarta yana son kallon qwayar idonta amma taqi yarda "I need more please..."ya fadi muryarshi qasa qasa tamkar mai rada,tuni ta shagwabe fuska tana cewa "please.....Please,na yima fa,kuma momi ke jiranka fa ma"ya yunqura ya miqe yana gyara botiran rigarshi da suka balle yana cewa "ok"sai da ya gama ya miqa mata hannunsa har lokacin tana zaune kanta a qasa "oya get up"a hankali ta dora hannunta saman nashi ya dagata,sai jirin nata ya kwasheta tuni ya riqeta don kada ta sha qasa "fadeela I think you are not well" "am well" "A'ah,ki shirya gobe zan daukeki ta office in kaiki kiga likita" "Amma....ai zan...."ya tsansa ya dora kan lips dinsa "shshshsh...kada kice komai"shirun tayi ya leqa fuskarta "zaki rakani gun momi muyi sallama?"girgiza kanta tayi "um um"yayi murmushi "shikenan to kwanta abinki"ya zaunar da ita gefan gadon,system din ya fara kashe mata ya maida mata ita saman madubi,ya dawo inda take yana kallonta ya kama hannunta ya sumbaci sama yana cewa "good night my dear baby na,sweet dreams,I love you"a hankali ya bude bakinta tace "I love you too my dear *haidar*"farinciki ya cikashi kamar ya taka rawa,tuni saboda kunya ta cusa kanta qasan pillow tana murmushi har ya fice Momin kawai ya tadda a parlour din yanzun ma ita da iftihal dake shimfide kan cinyarta tana baccinta abunta,a yatsine momin ta kalleshi "sannunka kaji?" Murmushi kawai yayi idanunsa na kan 'yar diyarshi,ya shafa kan iftihal din "ayi haquri momi zan tafi sai da safe" "kada naga qafarka da safe a gidan nan" da sauri ya dawo da baya ya taugunna gaban momin "yauwa momi na,Allah indai kika bani fadeelah ta ba zaki kuma gani na da sassafe a gidan nan ba,saima kin aika a nemo miki ni" dariya taso qwace mata amma sai ta kaba habarta yana cewa "o'o'o,sannu mara kunya,to anqi din har sai ta yarda da kanta" ya kama qafar momin yace "wallahi momi fadeelah ta haqura" ta dake dariyar dake cinta "kaga,mu bata gaya mana ba yallabai sai ka jira har sai ta gaya mana da kanta"ya marairaice "momi kunya fa kinsan take ji,ba zata iya gaya muku ba"momin ta tabe baki "ok,sai kai wato rasa kunga shine kazo kayi rashe rashe a gabana kake gaya min ko,don Allah tashi ka tafi gidanka ni na gaji da ganinka anan" Kai yake gyadawa kamar qadangare "shikenan momi,shikenan sai da safe"ya miqe ya fice cikin zuciyarsa yana fadin "zan shuka tsiya kawai,komai ta fanjama fanjan,su momi basu yanda nake ji bane"uncle abba dake can tsaye yana kallonsu yqna shan dariyarsa ba tare da sun sani ba ya qaraso "haba maimunatu,ayi haquri haka nan a bashi matarsa,tunda sun sasanta kansu,ni kam na fara tausaya masa,kinsan ciwon da namiji ma na da namiji ne"ya qarashe fada cikin zolaya,dariya uncle abban ya bata sosai"shikenan tunda abun wariyar launin fata ce nima ai ciwon 'ya mace na 'ya mace ne,sai na gyara diyata nima,idan yana so jibi ko gata sai a bashi ba don halinsa ba" Ya sunkuya yana qoqarin dauke mata iftihal daga kan cinyarta "mudai tunda za'a bamun ai shikenan godiya muke,bari in dauke miki amaryar taki,kije ki huta kema"ta saki murmushi tana cewa "godiya nake abba"ta miqe tabi bayansa tana barwa sumayya da rabi'ah dake kitchen auna wanke kwanukan da aka bata don basa barin wanke wanke ya kwana sallahun idan sun gama su kashe duk qwaya qwayai da kayan electronic na parlour da kitchen din Tunda ya zaunar da ita a gun ta bingire ta kwanta saboda kasala,juyi kawai take tana tariyar abinda ya farun a wunin gau gana daya tsakaninsu,babuabunda take saki sai murmushi,shi din ma koda ya fito daga wanka kasa hasala komai yayi,sai da ya zauna gefan gado ya dauki wayarsa ya kirata,tana tsaka da juyin nata ne kiran ya shigo mata,ta gyara kwanciyarta hadi da rungume pillow sannan ta amsa,sallama ta masa da muryarta mai sanyi wadda ke saka susuta shi "fadeelah bazan iya bacci ba sai naji muryarki" "But...."sai kuma tayi shiru "But what?,pls gaya min abu daya wanda zai sani samun nutsuwa idan nazo baccina" numfashi ta ja sosai sannan tace"i love you for all that you are,all that you have been,and all you're to be my haidar"kalaman sun tsaru sosai cikin kunne da zuciyarsa,ta kashe masa jiki da zaqin kalamansa,idanunsa na a lumshe yace "are you sure babe?" "Yes am sure,duk abinda na fada I mean it"dogon sumba ta bashi a wayar sanna ta kashe tana murmushi qasa qasa,shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar jikinsa ta zuba.......... *Mrs muhammad ce* [10/16, 2:16 PM] Salma *WA YASAN GOBE?....* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* Shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar jikinsa ta zuba Zaune take a nutse cikin office din,sanye take da shadda dinkin riga da zani rapper marun,sosai shigar ta yi mata kyau matuqa ta kuma dace da fatarta,hakanan take kullum ba dai tayi kwalliya a kushe ba,ta iya dressing sosai,hannunta dan madaidaicin cup ne cike da coffee tana dan kurba kadan kadan don babu abinda ta iya ci tunda gari ya waye,gaba daya hankalinta na gun aliyu tunaninsa take,amma idan ka kalleta a zahiri qata news paper dake gefan hannunta ta zubawa ido tamkar mai nazarin wani abu a cikinta Yafi minti goma a atsaye bakin qofa,sam baya gajiya da kallonta,baiqi su dawwama a haka ba,tsarin shigar tata yayi masifar tafiya da shi tayi wani das tamkar fure,sai kuma aka taki sa'a shi din ma marun din shaddar ce a jikinsa Har ya iso bata ankara ba,a hankali yasa hannu ya zare cup din coffeen dake tsakiyar tafukan hannayenta "irin wannan zurfi a tunani bai dace da kyakkyawa ba" ya fadi yana maida cup din gefe,yaja kujerar dake opposite dinta ya zauna yana cewa "nasan dai ji kike tunani ko....to gani na iso ai sai abar hasashe a koma zahiri"murmushi ta saki a kunyace tayi qasa da kanta,ya sake binta da mayun idanun nan nasa,gani yake tamkar kullum wayewar garin Allah kyau ake dada mata,ya jawo tattusan hannunta dake zube saman table din yana matsawa,ji tayi kamar wani sinadari yake zubamata cikin jikinta,ta soma qoqarin zame hannunta tun kafin yayi mata illa cikin kunya "no baby,your hand fits in mine like its made just for me,kada ki cire" Ta dan zame dag kan kujerar ta gaidashi,noqe kafada yayi "naqi,ni ban irin wannn gaisuwar nake so ba,let me show you irin wadda nake so"kafin tace komai ya zagayoda ita zuwa inda yake zaune yayi mata mazauni kan cinyarsa,qam ya matseta,sai da ya yamutsata son ransa sannan yace "irin wannn gaisuwar nake so ko a ina muke right?"gyada ka tayi cikin jin nauyinsa,ta bishi ne da haka amma itakam rashin kunyar aliyyun tafi qarfinta "a'ah dear,ki daina min rowar sweet voice dinki,ki dinga bude baki kina magana sannan ki dinga bude idanunki sosai kina kallona,zuciyarmu ta riga ta zama daya....dubi"ya fadi yana juna mata dressing din da suka yi "baki san me zansa ba nima bansan me zaki sa ba amma saboda zuciyarmu na manne da juna mukayi shiga iri guda" Murmushi ta saki tana kwantar da kanta a kafadarsa,"ok,I hope kin shirya,don daga nan sai asibiti,gwara muje kiga doctor sa'adah"ya fadi yana sunkutarta kamar wata bebin roba,wutsil wutsil ta soma yi da qafafunta "please my haidar,zan iya tafiya kada ka fita da ni a haka"dariya taga ya saka,ta dan saci kallonsa don bata taba ganin dariyar tasa haka ba,ya maimaita abinda tace cikin kwaikwayar muryarta sannan ya direta "matsoraciya,dama tsokanarki nake"duk da haka bai qyaleta ba sai da ya kamo hannuwanta,a haka suka isa bakin motar,ya bude mata ta shiga sannan shima ya shiga Ko a office sai da doctor sa'adah tayi masa wayo koreshi waje da qyar don ya hana fadila sakat ,kunyar doctor din fadilan keji shikam ko a jikinshi,da zarar fadilan ta bude baki zatayi magana sai yayi sauri ya rigata cewa "doctor rabu da ita,awo na kawo miki ita,na jefa qwallo a raga" mamaki da kunya suka kama fadila haka aliyyun yake?,tamkar ba wannan aliyyun nata ba,ita kanta doctor sa'adah din tayi mamakin yadda ya sake yana ta raha har irin haka kamar ba aliyu salim maitama ba,mintina talatin doctor sa'adah ta gama duk wani bincike da gwaje gwajenta,madaukakiyar fara'a da farinciki da ta gani kan fuskar doctor din shi ya bata mamaki "congratulations fadila,naji dadi da ya zamo nice ta farko da zan taya ki murna,Allah ya albarkaceki da samun juna biyu"ta fadi tana sanya tafin hannunta cikin na fadilan Sak fadilan tayi tanajin kunnuwanta kamar basu ji mata dai dai ba,ciki gareta da gaske?,cikin aliyyu a jikinta?,aliyyu masoyinta?, *alhamdulilahil lazi bini'imatihi tatimus salihaat*,wannan baiwa da ni'ima ta Allah da me tayi kama?,Allah kenan mai kyauta da qari,buwayi gagara misali,mai azurta bawa a duk sanda ya so,mai amsa addu'ar bayinsa,yau ga aliyyun Allah ya bata kuma ya bata dan aliyyun cikin cikinta,ya zabeta cikin matansa yace ita zata haifa,batasan lokacin da hawayen farinciki suka balle mata ba,a hankali bakinta ya soma salati ga fiyayyen halitta,sannan ta dora da godiya ga ubangiji, "na godewa Allah gwanin iyawa,doctor pls bana son ki sanar da aliyu batun cikin nan yanzu,nasan bazai
Chapter 67 · 0% Book details