← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 84

Sashe 62

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kawo mata madaidaicin gado da cupboard irin nasu rabi'ah aka sa mata duka adakin kasancewar dakin qato ne sosai,su suka taya ta shirya kayan suna ta rawar jiki zasu zauna tare,batasan lokacin da su ummunta suka tafi ba sai da anty hauwa ta hauro saman take sanar mata Cikin daren babu dan qaramin haukan da baiyi ba,kuka ma kasa zuwa masa yayi sai zafi da radadi da zuciyarsa keyi,daurewa kawai yakeyi yana sakar musu jiki don kada ya shiga haqqinsu,wani lokaci idan kewar ta isheshi dakinta yake tafiya yayi bacci cikin bargonta ya kalli hotunanta sannan yake samun relief (Qalubale a agareku iyayemmu mata har ma da mazan,da kuna ji kuna gani 'ya'ya yenku zasu dinga auri saki,babu kwaba balle hantara,wani lalacewar ma idan anyi sakin wai sai ya kwaso yaran ya kawowa uwar ita ce mai riqe masa kuma tana ziga shi har kina furta gwara da ya saketa,,to ahir din mu domin kuwa kada mu manta mun haifa ko bamu haifa ba an haifa mana,za'a yiwa taki 'yar ko 'yar 'yan uwanki kiji idan da dadi? Ai ko.matar ba ta gari bace akwai matakai da Allah s.w.a yace abi kafin akai ga rabuwar bawai rana tsaka daga an dan saba masa laifin da bai kai ya kawo ba ya karkace ya danqaro saki ba,to wallahi muji tsoron Allah,shi mai sakin dake mahaifiyar me goyon bayansa ina zato a cikin 'ya'yansa ko jikokinki ba za'a rasa mace ba,ya zakuji yayin da aka koro muku ita?,saki yayi yawa musamman acikin al'ummar mu ta hausawa,don Allah mu daure mu gyara ko ma samu gyaruwar al'ummar mu wadda wata tabar barewar tarbiyya daga an saki uwa ne shikenan sai gida ya tarwatse kowane yaro yayi nasa alqibla,babu mao saita siu kan hanya wato uwa ta gari,Allah kasa ku dace mufi qarfin zuciyarmu,ameen) Sosai ta koma bakin aikinta don uncle abba yace babu mai hanata,babu yadda aliyyu ya iya haka ya zubawa sarautar Allah ido,ina ma yaga bakin magana koda yana da ta cewar?,don ko yazo gidan iyakacinsa parlour ko kallon upstairs inda dakunan baccinsu yake momi ta shiga balla masa harara kenan,haka zatayi kicin kicin da fuska har sai ya gaji da muzurai ya qara gaba Ita kuwa uwar tafiyar tun daga lokacin da akayi hukuncin bao sake sanyata cikin idonsa ba,har addu'a yake Allah ya hadasu amma daidai da gilmawarta Allah baisa ya gani ba,tana sane ta sani,matuqar taji muryarsa to babu ita babu fitowa tana qule cikin daki ko kitchen idan a qasa take har sai ya bar cikin gidan Da yammacine suna zaune cikin parlour ita da sumayya da rabi'ah,momi bata nan ta tafi dubiyar yayanta da baya jin dadi alh datti ita da iftihal suka wuce,gidan sai su ukun,lokaci lokaci rabi'ah naeqa kitchen ta duba abincin dare da ta daura sumayya kuma na tsefewa fadila calabar din da take kanta,saboda tsawo da santsin gashi da hannu suke tsifar,yayin da fadila ta jawo wasu fuskarta tana tayata,wani film da suke masifar ao suke kallo a m.b.c bollywood,na soyayya ne sosai,jarumin film din na musu kama da aliyyu sosai hatta da halayya,don haka wani lokacin ma ya aliyu suke kiransa duk sanda aka sako film din,suna son film din don haka idan ana kallonsa ko hira ba'ayi,saidai idan anzo wani gun daya burgesu, A hankali aliyyun ya turo qofar falon with confidence don tun a gate ya tambaya aka sanar masaomin bata nan,basu ga shigowarsa ba sai sumayya kawai don rabi'ah na kitchen duba girkinta,fadila kuwa gashin da ya rufe mata fuska da yadda film din ya yafi da hankalinta sosai yasa sam bata lura ba Sumayya ta bude baki zata yi masa sannu da zuwa ya dora yatsansa kan labbansa,gum kuwa tayi shiru,ya bata umarni na gaba da ido alamun ta tashi a hankali ta haye samansu,ba musu kuwa cikin sada ta haura saman,gurbin da sumayyan ta tashi nan ya maye,harda dan jawota ya jinginar jikin gwiwoyinsa,fadila uwar 'yan son jiki kuwa ya jingina abunta harda cewa"yauwa sumayya dama baya na ya gaji,calabar ko ashirin bata kai ba amma taqi tsefuwa ta dadin rai?"baice uffan ba ya kama jelar kitson ya soma tsefe mata kamar yadda yaga sumayyan nayi,ita kuma bata damu da rashin amsawar sumayyan ba ta bayar duk film din ne ya dauki hankalinta,rabi'ah ce ta fito da sauri daga kitchen din don kada tayi missing wani gurin,turus tayi ganin aliyyun a gun da sumayya tasan ta bari,itama yatsan ya dora mata kan lips nashi,yayi mata nuni da ido kan ta koma kitchen,nan ne ma fadilan taga giftawar komawan rabi'an kitchen din "rabi'ah za'a wuce gun da kike son kalla fa" "ina zuwa anty ban qarasa hada miyar bane" Gaba daya ya shagala,wani irin farinciki ke ratsa shi,santsi kyau da qyallin gashin ya hanashi ganin wahalar tsifar,sai gashi sun kusa gamawa saura guda daya,yana ankare da yadda take bawa film din muhimmanci,murmushi kawai take zubawa hadi da sakw gyara zama,sai da aka zo wani gu da yayi masifar qayatar da ita ta saki murmushi tana cewa "hmmmm......soyayya" ta dan waigo tana cewa"don Allah sumayya basu burgeki ba yadda....."kasaqarasa maganar tayi ganin aliyyu zaune dare dare saman kujerar yaa mata tsifa,to sumayya ce ta rikide ta zama shi ko idanunta ke mata gizo?....... *Mrs muhammad ce* [10/16, 2:12 PM] Salma *WA YASAN GOBE?....* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* Sai da yasa bakinsa ya hure mata idon sannan ta dawo hayyacinta,da hanzari ta miqe sannan kuma a guje tayi sama tamkar wadda taga dodo,binta shima yayi a hanzarce yana kiran ta tsaya,ganin da gaske take ba tsayawa zata yi din ba ya sanya shi cafkota a matattakalar qarshe,cak ya dagata yayi dakinsu rabi'an da take son shigewa,cikin sauri sumayya dake zaune saman dressing chair ta fito ta bar musu dakin Tsakiyar gado ya direta sai haki suke dukkansu saboda gudun da suka kwasa a step din benan bugu da qari yadda zuciyar kowannensu ke bugawa,sun zubawa junansu ido cirko cirko da su kamar zakaru,a hankali yake hawowa gadon yayin da ta soma ja da baya har ya qureta,suka sake zubawa juna ido,shi nashi na tsantsar so da qaunace da suke sake huruwa cikin zuciyarsa take kuma aika saqonni zuwa sassan jikinsa,yayin da nata kuma na jin haushi tsoro da fargaba ne don bata manta wannan dare ba,kasa jurewa yayi sai da ya miqa hannunsa ya janyota ta fado jikinsa ya matseta gam a qirjinsa Cikin fusata haushi da mamakin aliyyun ta soma tureshi,saidai ko motsi baiyi ba don qarfin ba daya bane,a hankali ya soma sinsinar wuyanta cikin kunnuwanta zuwa gashin kanta,ya dago fuskarta a hankali ya tura harshensa cikin bakinta,tsotsa yake sosai tamkar wanda ya samu sweet yayin da ita kuma take turje turje hadi da yunqurin tureshi daga jikinta saidai sam ma shi baisan tana yi ba,ganin duk iya qoqarinta ta kasa barin jikinsa sai ta fashe da kuka,hawayen da ya gangaro fuskarta ya taba nashi fuskar shi ya ankarar da shi,ya zare bakinsa daga nashi ba tare daya bari ta bar jikin nasa ba,kukanta take sosai yayin da ya zuba mata ido,gaba daya ya marairaice ya koma kalar tausayi " *fadeelahhhhh*"ya kira sunanta cikin wani irin yanayi tamkar mai rada,da sauri ta dago kanta ta kalleshi don wannan shine karo na farko da ta taba jin sunanta a abakinsa, "fadeelah" ya sake kiran nata ta sake itama kallon nasa "please fadeelah forgive me,I know I hurt you I break your heart,babu wanda ya wuce kuskure,fadeelah I love you more than words can say,I can't do without you,na kamu da soyayyarki,pls kada,pls kada kice zaki hukuntani da tarin laifuffuka na,if bazaki iya yafemin ba ma na amince kiyimin kowanne irin hukunci zan dauka,amma bazan iya jure rashin ki ba" "Haka aliyyu ya shahara da yaudara?,haka aliyu yake?,taya mutumin da ya qika ya kuma sanar maka bazai taba sonka ba yanzun yace yana sonka?,bazai taba yiwuwa ba it can't"ta fadi hakan cikin zuciyarta tana girgiza kai,tayi wani kukan kura ta shammaceshi ta fusge daga jikinsa,jikinsa ya riga da ya mutu shi yasa ta samu nasarar qwacewar,tana yunqurin sauka shi kuma yana yunqurin sake cafkota aka turo qofar dakin,tuni fadila tayi amfani da wannan damar ta shige toilet "qaniyarka,qaniyarka nace" cewar momi dake watsowa aliyyu daquwa,sunkuyar da kansa yayi qasa yana Tsakiyar gadon da tuni ya bedsheet dinsa ya yamutse,ta qaraso cikin dakin tana riqe da murfin qofar dakin da daya hannun ta nunawa aliyyu waje "zo ka fice ka bawa mutane guri mara kunya,ka keta idanun qannenka ka biyota har kan gadonta" "kai momi kamar ba mata ta ba"ya fadi hakan cikin zuciyarsa yana ficewa daga dakin Momi ta qarasa bakin qofar toilet din ta qwanqwasa tana cewa "fito" fadilan kanta a sunkuye kunya da takaici na sakadarta ta fito,momin ta dafa kafadarta tace "ko wani bak gaya min ba na sani kina son ali,muma kuma bamu taba fatan aurenku ya rabu ba har a qiyama,munyi hakanne don ya sake sanin darajarki da qimarka ta yadda ko nan gana bazai sake wasarere da lamuranki ba,ki samu yi duk mai yiwuwa ki tabbatar da soyayyarki cikin zuciyarsa kin fahimceni?" Cikin gamsuwa ta gyada kai tana yabawa momin ta yadda son kai bai rufe mata ido ba,bata duba cewa aliyyu danta bane bare ta bari tana gani a cutar da ita ba,qaunar momin da qimarta suka dadu cikin zuciyarta *_1:30 am_* Qarfe daya da rabi na talatainin dare fadila na kwance rub da ciki tsakiyar gadon ta,gaba daya ta rasa bacci cikin idanun nata,duk juyin da zatayi qamshin turaren aliyyu take ji daga bakinta har kayan jikinta,har kaya ta sauya amma a banza man kare don bata daina ji din ba,tana kallon yadda su sumayya ke baccinsu hankali kwance sai take jin dama ita dince su,basu da wata damuwa,wayarta dake gefan pillow dinta ta soma haske wanda ke nuna alamun kira ne ke shigowa,cikin mamakinta daga wayra tana duban kiran baquwar numbace,ta zubawa kiran ido har ya katse,ba'a fasa kiran nata ba har sai da ta tashi da missed call bakwai ana takwas dinne ta yanke shawarar dagawa ko wani abunne ya faru,ta danna ok ta kara a kunannta tayi shiru ba tare da tace komai ba "Bakiyi bacci ba fadeelah?" Ya tambaya cikin wata iriyan sassanyar murya wadda har sai data sanya fadila runtse idanun ta,tana
Chapter 62 · 0% Book details