Sashe 70
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*PART 3* 2 Daga hutun sati sai aliyyu ya birkice Fadila bata komawa aiki,bata iya sa'insa da shi ba sai kunya da ta zauna tana rusa masa babu qaqqautawa,shu kuwa Abu guda dake daga masa hankali kenan,zama yayi dirshan yana clarifying mata dalilansa "Baby bana so ,duk sanda zaki fita baby na akwai mai kalle min ke,duk sanda na tuna hakan sai naji zuciyata na quna,pls my unique ko don babymmu da kike dau ke da shi ki haqura,ki gayamin nawa kike dauka a Wata nayi alqawarin zan miki multiplying nasa" Ta share qwallar dake shatata Duk da ba daina zubar tayi ba,"banaso ni aikina nake so,ka ganshi fita ko ina sai tare da kai,matanka su da yake kana sonsu fiye da ni ai gashinan babu inda baka barinsu suje,sai ni da nake fita aiki "ta fadi cikin fushi tana zumburo baki,Dariya ta bashi sosai,don ya lura gaba daya cikin nata yasa mata saurin fishi hasala da saurin kuka,kan cinyarsa ya dorata yana gorge mata Hawaye "Gaba maman biyu,kin manta ke din ta musammance?kin manta aliiyunki bashi da kamar yake?ko kuwa kin manta cewa kace mace ta farko da aliyyun ya mallaka mata komai nasa kam r yadda kika kasan e mace ta farko da ta mallaka wa haidar din komai nata?,hakanan ta farko da ya fara so da kangin kansa?" "Kiyimin rai ki raini yarona ba tare da yasha wuya ba,dama tun farko aikinki din nan ba Sonshi nake ba,idan ba zaki manta ba ran r farko da zaki fara zuwa irin sharudan da na dinga gindaya miki,wlh a lok zuciyata t fasa kawai take,bans an sink I da na boye ne yasa ni jin haka ba,banda Ahmad ne ya same ni kai tsaye da maganar da ba zakiyi shi ba,na roqeki kiyimin wan an alfarmar ki haqura"ya Jade hannunsa da nata yana Kallon qwayar idanunta,sai taji bazata ita wofantar da alfarmar da aliyyun ya roqeta ba,saboda haka a take ta rubuta letter din barin aikin ta damqa mishi, Aliyyu ya cancanci komai a gunta,tsananin kulawa da qaunar d yake nuna mata kadai ta isheta,abinda kullum ke dawwamar da ruhinta cikin farinciki da begensa,godiya ya dinga mata har sai da ta rufe masa baki Duk cikinsu babu wadda ta ankara da cikin d fadilan ke duke da shi,ba wa ni shiga sabgarsu take ba bare su ganta,don tuni aliyyu yayi mata maganinsu,iskancinsu na da suka so su dawo da shi,su shigo musu ranar girkinta a cinye abi ci da su,sannan kuma suqi tafiya suyi zamansu,bayan ita ranar nasu girkin da ta shigo ta masa barka d dawowa minti goma ta bar gurin ta koma bangarenta,duk nacinsa bata zama don bazata yi abinda idan ita akaiwa ba zata so ba To su kam basu s n hakanba,don haka da zarar sun wuce minti goman zai janyota jikinsa ya fara yamutsata,to yanzun nan zaka ga kow cce ta ja qafafunta ta wuce,dariya yakeyi abinsa yace tunda ke kin kasa maganinsu abun ni gashi nayi miki ko?"ita din ma wani lkc dariyar ke ka ma ta Wata hudu cikin amma idan ka ganshi sai Kayi tsammani yayi wata shida,sosai abun ke basu mamaki su duka,amma babu abinda fadilan ta fasa,mita da qorafi kam tana shansa,don wa su lokutan ma idan ranar girkinta ne idan zai fita gidan anty hauwa yake kaita tace"ga gajiya nan ya kawo kada a barta tayi koma,idan ya dawo sai ya biyo ya dauketa,da ya ajjiyetan sai fa ta faki idonsa ta masa girki ko da mai sauqine don tace ita kam ladan bai isheta ba Aliyyu tace"shi kam indai lada ne ya isa haka,don kuwa ko iya cikin jikinta ya isheshi,aljanna kuwa indai shi zai dage mata qafa ta shig to tuntuni tasa a rage take"dariya taci ranar cikin alfahari da jin dadin kalaman yabonsa a gareta Ya kaita gid n Anty hauwa yadda ya saba ita Kuma tace kausar tazo ta rakata gidansu nuratu ayi mata Jan lalle,anty hauwa tace"sannu Fadila da qoqari,ko wuya zaman lallen baya miki?" Tayi 'yar dariya "wlh Anty bana jin dadin batun hannuna ne haka,Kuma ma ya aliyyu naso" "A'h tunda ya aliyyu na so sai a bada himma,don na fuskanci kin gama shagwabashi gaba daya,mu nan duka yanzun ganin must yake bamu iya zaman aure ba"ta qarashe maganar cikin tsokana,dariya ta kama Fadila lkcn da take sanya hijabinta "wlh Anty ba haka bane" "Allah kin gama shagwabashi,idan yaso gidan nan ya dinga min fi'ili kenan"ta sake tuntsirew da dariya lkcn bilkisu ta shigo tace"Anty kamalu driver yace ya fito da Motar mu fito,tare suka tafi akabar antin a gida *Mrs Muhammad ce [12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed *WA YASAN GOBE?........* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 3* 2 Har aliyyu yazo daukarta basu dawo ba,nan ya dinga saukewa Anty hauwa kwandon mita ya dinga yi kamar zai ari baki,safe baki kawai Antin tayi tana kallonsa "To ni meye nawa aliyyu,kwalliya take son yiwa mijinta sai na hana?" Dariya taso ka nata ganin yadda yaketa safa da marwa kamar Wanda kace an saceta,ga wayarta Kuma na kan Kujerar falo ta manta ta Minti ashirin Motar su ta shigo,da suri ya qrasa ya bude mata qofar Gaisa miqa mata hannunsa ta Dora nata a kai,Jan lallen kam yayi dau ya haska idanunsa,Zara zaran yatsunta suka sake yin kyau,diba yasa ido ya sakar mata hararar wasa,ta saki murmushi idanunta cikin nashi tana langabar da kai cike da kissa "Zaki sani tunda kika ke kikayi zaman lalle kika wahalrmin da baby,punishment dinki na yau babu ke ba tafiya da qafafunki"kafin tace komai har ya sunkuceta ita da cikin jikin nata ba tare da jin nauyinsu ba,yasa kunya ce da ita bata son ya dinga daukarta haka cikin muta Cikin mitarsa ya sakata bayan ya kwantar mata da Kujerar,cikin shagwaba ta kalkeshi "Please my haidar,baby I fa sallama da anty ba" "Shshhhhh"ya dora yatsansa Dan man uni kan lebansa"ta yafe ba sai kin mata ba,mu tafi gida ki huta baby"ya zagayo side dinshi ya tada motar,ai kam kafin su isa gid har bacci yayi awon gaba d ita,murmushi ya saki ya Shadda fuskarta da daya hannun nasa yanajin wani sonta na shigarshi Yana tsaida motar ta farka idanunta fes bisa fuskarshi,sukayiwa Kuma murmushi yadda suka saba a duk yayin da suka kalli juna,ya fice ya zagayo ya bude qofar hadi da daukota cak "Wayyo my haidar ,don Allah ka saukeni"ta fadi tana wutsil wutsil da qafafunta gami da dan dukan qirjinsa kadan kadan "Kun manta punishment dinki kenan?" Samira dake manner da earpiece a kunnanta ta fito daga bangare ta,kamar umarni idanunta suka sauka a Kansu,riqe bakinta tayi a ahankali ta dinga takowa indai su ke ida unta qyar kan cikin fadilan,ashar din da ta lailayo ne yasa suka ankara da ita a gun,da hanzari Fadila taci gaba da mutsu mutsu ko zata samu ya sauketa ko don idon Samira "Kace tuni ka dirka mata mu ka barmu kara zube saboda tsabar iya cin Amana"ta fada sanda ta tsareshi d ido,girgiza kai yayi lokacin da murmushi ya subuce masa,shikam yana mam Samira idan tayi wa ni abu baiko kulata ba ya barta nan a tsayen ya nufi bangarensa don baisan me takeso ya gaya mata ba,qasa qasa Fadila ke cewa"bai kamata ba dear fa,ko nice ba zanji dadi ba" Baisan lkcn da ya tuntsure da dariya ba"mene bai kamata ba?,cikin naji?,ai bani na baki ba Allah ne ya baki,idan da sun so wataqil da tuni Allah yasa sun Samu tun kafin ke,ko Kuma sahun nata zaki ni?"ya qarashe cikin sigar tsokana Dirshan take zaune saman cinyarsa,ayabarta wadda ita ce abincin yake bare mata,sai zuba shagwabarta wadda take burgeshi take,qaramin wandone a jikinta sai Riga ta vest wadda ta fito d turtsetsen cikinta,Kanta ya sha gyara Wanda Aliyyu ne ya zauna ya gyare abunshi tsaf ya mata parking sonsa Salima ce ta shi go da sallama ,ragowar sallama ta maqale a maqoshinta,tashin ahankali wanda ba'a sa masa rana shi Salima ta shiga,ciki?ciki a jikin Fadila?yarinyar da ta tsana take adawa da ita fiye da duk Wata halitta dake bayan qasa?,kasa dauke idnunta Sam tayi saga kan cikin,hakanne ya bawa fadila tsoro tuni ta Dora hannun nata saman cikin nata idanunta a lumshe tana ta soma karanto addu'o'in tsari,aliyyu ke Kallon yadda Saliman ke wani numfarfashi kamar maras lafiya,tuni ya soma tambayarta menene ya soma yunqurin Ajjiye Fadila don ya isa gareta Tuni ta saki handle din ta juya ta five ba tare da tace koma ba,kuka sosai ta rushe da shi,matsananciyar qiyayyar cikin da uwarsa suka lullubeta,wani ts utsayi ne tuntuni ya hanata sakin jiki ta cika gidan aliyyu da 'ya'ya fiye da kowcce mace da da zaya ajjiye?,take ta ciwa kanta alwashin ko ta halin qaqa ba zata taba lamincewa cikin nan ya taka doron qasa ba,domin tana ganin ita t fi kowacce mace cancanta ta sake haifawa aliyyu yara ba Wata c n ba,nan shaidan da Zuciya suka ci gaba da tunzurata gamida shirya m ta sharri kala kala *Mrs Muhammad ce [12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed *WA YASAN GOBE?.......* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 3* 2 Doguwar Riga ce jikinta kamar yadda suka zamo sune shigarta na yau da kullum,sabida cikinta bai bari ta sake cikin ko wani irin kaya idan ba su ba,ita kanta girman cikin na bata mamaki,wayarta ce a hannunta tana tsarawq aliyyu tex na an wuni lpy kamar yadda yake al'adatarta kullum idan ya fita babu fashi koda sunyi Waya koda Kuma ba ranar girkinta bane Cike da mamaki ta dagi tana masa sallamar Salima wadda ta shi go hannunta dauke da wa ni madaidaicin food flask fuskarta qunshe da murmushi,Fadila ta boye mmakin nata ta Hawa Salima tayi gurin z ma,ta sauna din kuwa idonta na akan fadilan "Sannu uwar hudu"ta fadi cikin salon son nuna tsokana ,sai itama tayi qoqarin dora murmushin kan fuskarta "Yauwa sannu an wuni lpy?" "Lpy qalau"ta fada tana tunda flask din gaba fadilah "Wannan dama na kawo miki,nasa masu ciki akwaiku da kwadayi,Duk da ba'a gaya mana qaruwr da aka samu ba,ai dan aliyyu namu ne mu duka"ta fada kai ka rantse har zuciyarta,murmushin itama ta sake yi,t janyo flask din tana budewa Fasten dankali ne Wanda ya sha danyen kifi irin marar qayarnan,a zahiri abincin yayi don qamshin