← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 84

Sashe 17

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta tsinci kanta ne kwance bisa carfet din falonta Aliyu yabi inda ta wuce da kallo ganin bata tanka masa bailla ma ledar hannunta da ta saka ta wuce tana raba hanya,sai yaji wani iri a cikin zuciyarsa yake jin kamar bai yi abu mai kyau ba ya sunkuya ya dauki ledar da ta saki din ya bude mota ya hada da tasan ya wuce sashensa don ko kusa baiyi sha'awar neman samira ba don yasan bazai tainci komai ba illa qarin damuwa da koke kokenta na tsiya,kai tsaye ya wuce bedroom dinsa ya dora ledojin bisa center table din dake gaban gadon ya cire kayansa ya shiga wanka bayan ya fito ya ciro kayan bacci ya feshe su da turare su haka nan jikin sa,ya shimfida sallayarsa yayi shafa'i da wutiri sannan yayi addu'o'insa ya shafa,ya murzawa qofan dakin key yasa hannu zai kashe wutan dakin din kwanciya idanunsa suka fada kan ledojin da ya shigo da su,bayan ya kashe ya koma ya dauki ledojin ya koma saman gado ya kunna fitilar gefan gado ya zazzage kayan dake ledar farko,daya bayan daya yake daga kayan sannu a hankali yake binsu da kallo,sai yaji kayan aun nurgeshi kamar ta san zabinsa,kayan sun masa sosai ya maida su cikin ledarsu,ya jawo tata ledar ya bude wani dan qaramun murmushi ya saki hadi da wani abu mai kamar tausayi da ya kamashi,sam list din siyayyar da aka turo masa nata bai kai daya bisa biyar din siyayyar samira ba,ya tashi ya bude dan qaramin pridge din dake dakin ya debe ive cream din ya zuba aciki ya hade ragowar kayan ya dora bisa bedside Kwananta biyu kenan tana fama da matsanancin ciwon kai da yaqi saukar mata ta wani rame tunani biyu ne ya addabeta,yiwuwar qara masu abokiyat zama wanda take ganinhaka wabi babban qalube ne da zai qara nisanta ta da aliyu sai kuma raahin sauki na qiyayyar ta da take gani qiri qiri atsakiyar idanun Aliyu Mrs muhammad ce [10/16, 12:34 PM] Salma Wa yasan gobe?....... Written by safiyya Abdullahi musa huguma Yauma tana kwance saman carpet ta kanta bisa pillow kwanciyar rub ciki tayi saboda yadda take jin kan nata kamar zai tarwatse doguwar rigar bacci ce a jikinta iya gwiwa,gashin ta yayi dai dai kan pillow din,idanunta runtse suke ciki n haka ta jiyo sallamarsa,ta kadu sosai wanda hakan ya sake haifar mata da wani ciwon ko motsi ta kasa yi bare tayi yunqurin barin falon,tana jinsa har ya qaraso kanta yana sake maimaita sallamarsa,sai dai dif ta kasa amsawa sai wani bari da jikinta yake yi,yasa qafarsa ya dan bigi gefan pillow din da take kai ga zatonsa bacci take saidai nan ma yaji shiru,hakanne ya danso taba tunaninsa,ya sunkuya a hankali yasa hannayensa biyu ya birkitota gaba daya ta dawo rigingine fuskarta cikin tasa saidai idanunta na runtse don wani tsoron ne ya sake mameyeta,hawaye ya gani sharkaf a fuskarta ga wani dan banzan zafi da jikinta ya yi har haqoranta sun fara haduwa da juna"subhanallah "aliyu ya fada,surarta gaba daya ta bayyana har baisan sanda ya fadi hakan ba kyakkyawan gashinta ya sauko ya rufe fiye da rabin fuskarta,sai kuma yadda jikinta yayi zafi da yawa da yadda idanunta suka tasa,ya sunkuceta kamar wanda ya dauki tsinken sakace yana laluben bedroom dinta Saman gadonta ya ajjiyeta ya zuba hannayensa cikin aljihun wadonsa yana kallonta ya rasa mai ya kamata ya yi mata wane taimako ya kamata ya fara bata,don da gaske tanajin jiki rashin lpyr na damunta,a hankali ya bude labbansa yace"relieve ur self and stop d crying "sai da ya kwashi kusan minti biyar sannan yace"already dama baki da lpy?"ta gyada kai ya sake tambaya"meke damunki?"ta nuna masa kanta,bai sake cewa komai ba ya shiga toilet dinta ya hada mata ruwan wanka mai dumi a bathtub sannan ya fito "kishiga ki shirya kanki likita zata zo"daga haka ya fice,ta daddafa bango ta shiga toilet din ta sabe jikinta ta dawo ta saka doguwar riga ta atamfa mai dogon hannu ta fesa body spray ta hade kanta da band qarami ba tare da ta taje shi ba ta koma ta kwanta,bata dade da kwanciya ba taji ana knocking aliyu ne ya tura ya shigo bai dubeta ba taji yana bada umarnin a shigo Likitace sanye da kayan aiki,aliyu dama bai lamunci hurda da likita namiji ba akan matsalar iyalinsa tun usuli tun maman iftihal doctor sa'adah itace family doctor dinsa ta qware sosai akan aikinta tasan me take tamakar mayya haka take akan cuta da maganinta,da sallama ta shigo farar macace dirarriya wadda aqalla shekarunta ba zasu haura talatin da biyar zuwa arba'in ba doctor sa'adatu akwai ta da fara'a don.mawuyacine kaga fuskarta babu murmushi yanzun ma da fara'ar a fuskarta suka gaisa da fadila tana mata sannu yayin da Aliyu ya jawo dresaing chair dinta ya zauna hadi da zaro wayarsa ya soma danne danne,doctor sa'adah ta ajjiye kayan aikinta a gefan gadon ta fara fito da su tana tsokanar fadila"Allah dai yasa qaruwa muka samu madam "kunya ta kama fadila don a haife doctor ta haifeta,ta dan saci kallonsa sai ta ga ma sam hankalinsa bai kansu Cikin qwarewa ta soma aikinta tana gwaje gwajen tana hada mata da tambayoyi,tambayoyinta har suka so rikita fadila domin tamakar doctor na son karanto zuciyarta ne ,fadila tayi ajiyar zuciya lkcn da doctor ta tsagaita da tambayoyin ta zauna a gefan gado yadda zata iya fuskantar aliyun sosai tace"gsky a.s maitama damuwa ce fal a zuciyar madam wadda itace musabbabin wannan ciwon nata wanda Allah ya gani da ace tana fa qaramin ciki da tuni tayi miscarriage dinsa,aliyu ya maida wayar sannan ya kalli sa'adatu ba tare da yace komai ba tasan bazaiyi maganar ba don ba komai yake bada amsarsa ba saboda haka sai kawai ta dora da bayaninta"ya kamata ka binciki abinda ya sanyata damuwa mai yawa haka,ya dauke idanunsa daga kan likita yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yace"doctor iya sanina bata da wata matsala amma gaki gata ai u can ask her"ya dago kyawawan idanunsa masu tafiya da zuciyoyin miliyoyin 'yammata ya zubesu fes bisa fuskar fadila,tayi gaggawar yin qasa da kanta don kada tana fama da kanta ya baro mata wani aikin,tasan cewar a yadda take jinta dinnan matuqar ta yadda suka hada idanu to la shakka qaryarta ta qare domin daga shi har sa'adah ba zasu sja wahalar gano mai ke dawainiya da zuciyarta ba"meye damuwarki?,ya furta cikin dakakkiyar murya ba tare da ya dauke idonsa a kanta ba ,da zata iya ba shakka da tace masa kaine!,kishinka da qaunarka aliyyu sune damuwata!!!,sai fainkash ko kusa bata jin zata iya,abinda take jin zata iya kuma ahi yafi dacewar tayi din shine shiru kuma shi tayi din Shiru din kuwa ya ratsa dakin doctor sa'adah tace"mai tama ba haka ake ba,it can be d screat ne she dnt wanna share it with another person so ka bari idan na tafi ta gaya ma a nutse"ta qarasa maganar tana yago pepper daga memonta mai tambarin asibitinta a jiki ta soma rubutu bayan ta kammala ta ajjiye takardar kusa da fadila da har yau kanta ke sunkuye tace"to madam Allah ya qara sauqi but pls kiyi qoqarin rage damuwa"kai ta daga ta mata godiya,sa'adah ta kalli aliyyu tace ga magungunan da za'a siya mata a nemo.yanzu ta soma sha zata samu relief insha Allah amma ta dan ci wani abu before ta sha din,ta miqe tana hada kayanta tqna musu salllama aliyu yace"thanks sa'adah a gaida yara Mrs muhammad ce Wa yasan gobe? Fitarta da yan mintina aliyu ya dauki pepper din maganin ya fice ba tare daya ce mata kanzil ba,shima ba dadewa da fitar tasa wayarta dake qarqashin pillow ta dau tsuwwa alamun shigowar kira,a kasalance ta daga wayar tana duba mai kiran sister farida ce ta daga hadi da yin sallama farida tayi dan jim sannan tace sister ya naji muryarki ta canza ne?fadila cikin muryar marasa loy ta masa mata wlh bani da lpy ne farida ya gida ya kuma mubarak?cikin yar qaramar dariya farida tace duk muna lpy sister ko ta samu ne?,samuwa kamarbyaya? Ta tambayeta,farida tayi qasa da murya tace ian nufin fa juna biyu,ta dan basar tace abinda kika bugo ki tambaya kenan?,a'ah anty dama ina ceqa ne gibe ki duba haya ina nan zuwa harda result dinki tun last week ya samu,duk da bata jin da lafiya hakan ya mata dadi sosai har ta nuna zumudi,jin bata da lpy yasa farida qyaleta akan sai tazo goben,ta amsa don dama kantabhar ya soma sarawa ta maida kanta saman pillow ta kwantar tana addu'ar Allah yasa ta samu damar aiki Ya shigo hannayensa biyu riqe da ledoji ya shigo ya zubesu kan bedside ya maida hannayanaa aljihu kamar kullum,ji tayi kamar ya cika mata dakin wani kwarjininsa ya cika mata gu jikinta yayi sanyi tanajin kamar ko hannuta ba zata iya dagawa ba ta shiga satar kallinsa duk fa batayi niyyar yin hakan ba zuciyarta ce ta tursasata kansa na qasa ne yana kallon carfet kamar mai nazari,sai ya mata kyau sosai fuskarana fes kama ganinta kasan tasan hutu tabbas maza irin aliyu sai ka tara dari zaka samu biyu cikinsu ga tsawo da qaqqarfan gangar jiki mai murdadden damtse mai cike da qarfi faffadan qirji mai cike gargasa wadda ta bayyana har hannayensa yana da jiki amma ba zaka kirashi mai qiba ba domin tsawonsa ya shanye ta,kusan ko yaushe fuskarsa a haka take ba fara'a sam don ita a iya saninta da shi bata taba ganin haqoransa ba, Saura qiris ya kamata tana satar kallonsa tayi gaggawar janye idanunta daga kanshi a hankali taji yace dazun na tambayeki meye damuwarmk yanzun ma na maimaita karo na biyu"shiru ta sake yi.masa hakan yasa ya kausasa.murya yana sake tambayarta,cikin cool voice dinta tace babu komai,ya dago kamar zai kalleta sai kuma ya lumshe ido ya budesu kan.ledojin da ya shigo da su sannan yace idan tashin hankalinki da damuwarki sun ta'allaqa ne kema kan dawowar maman iftihal to kiyi saurin taimakawa kanki ki nemi sassuci a gun zuciyar ki don zata dawo ne amatsayin mata ta karo na biyu ba wata baquwa bace......sannan ki bawa zuciyar dai taki again shawara da kada ta cika kanta
Chapter 17 · 0% Book details