← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 84

Sashe 32

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

1
Sadiya ta dafa kadar salima tace to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace ashe dai kin fara gano gaskiya ta
Sanda ta shiga yana zaune gaban na'urar tafi da gidanka yana qarasa aikin sa da dazun yunwa ta hana shi yi,sallama tayi ya amsa kansa na kan allon computer din,kujerar dake gefansa ta samu ta zauna,kusan mintina sama da ashirin bai ce mata kanzil ba don haka itama ta bude wayarta ta soma register din watsapp saboda yanzu as journalists tana buqatar wadannan kafofin sadarwar,
duk da basu dameta ba don ba yadda farida batayi da ita tun a gida ta bude koda watsapp ne kawai ba amma taqi tafi ganewa karance karancen magazines da wasu rubuce rubucen
Cikin yan mintoci qalilan ta kammala da account dinta na watsapp ta soma qoqarin hada na facebook,falon yayi tsit kowa ya sanya na'ura a gaba,lokaci lokaci takan daga ido ta saci kallonsa,qayatacciyyar fuskarsa da hasken screen ya sake hasketa tayi fresh,ta zubawa hannayensa ido yadda yake sarrafa computer din cikin qwarewa da da gwanancewa typing yake cikin sauri tamkar shi ya qera computer din yasan madannin kowanne abu abun sai ya burgeta sosai
Wayarsa ta soma ringing ya dauke kai daga kallon fuskar computer din ya maidaa idonsa kan wayar ba tare da ya daga ba,baquwar numbace kuma bai dagawa,kira aka ci gabaa da yi akai akai har ya gaji ya danna ok ya dora ta bisa computer ya sanya ta a hands free
Muryar mace ce "hello ranka ya dade" "salamu alaikum wake magana?"ya fada hannayensa na saman laptop dinsa yana aikinsa,"daga daya bangaren aka sake maqe.murya"suna na nadiya ina kiranka ne daga unguwar rijiyar zaki kano"bai maida hankalinsa ba kan wannan yace"me kike nema?"aka danyi jim har yana shirin kashewa sannan akace "don Allah ka rufawa zuciyata asiri kada ka kashemin waya domin kashe wayar tamkar kashe ni ne"ya tsayar da abinda yake sannan yace "uhm go on" aka saki ajiyar zuciya sanna tace "maitama Allah ya jarabceni da tsananin qaunarka wadda tasa na kasa jure hakan cikin zuciyata har sai bakina ya furta maka,ina roqonka don Allah ka taimakeni ka so........" "hey!"ya daka.mata tsawa "stop that,rubbish!"tsit tayi,ya ware idonsa kamar tana gabansa yace"ke baki da ajine irin na mata?" Shiru ba amsa don haka ya dora "let me tell you baki da shi,and inason gargadinki wannan ya zama na qarshe da zaki kira numberta,I hope kin fahimta ko"ya katse kiran hadi da jan tsaki,fadila tayi saurin dauke kanta lokacin da ya dago kansa taga tamkar ita zai kalla zuciyarta na wani irin bugu,kishi ya tokare mata qirji,ta lumshe ido bugun zuciyarta na qara sauri.......
Mrs muhammad dinku ce
[8/25, 3:44 PM]
+234 812 673 9684
: 5:55 pm 16/8/2016
*wa yasan gobe?...*
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
*PART 2*
Chapter 32 · 0% Book details