Sashe 19
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daki wanda ta gauraye da qamshin freshner mai dadi idanunta na lumshe ne tamkar mai bacci saidai ba bacci take ba tayi nisa ne a wata duniya mai wuyar fassarawa duk da ciwon da kan yake mata das das das amma hakan bai dameta baqarar bude qofan falon da qamshim mayen turarensa dake rataye da zuciyarta shi ya dawo da ita,ta bude manayan idanunta akansa yayin da shi kuma ke qoqarin tura qofar tayi namijin qoqarin tashi ta zauna kanta na sunkuye a qasa don ba zata iya jurewa kallonsa ba,hannayensa ya goye a bayansa ya qaraso falin yana kallonta da qayatattun idanunsa ya lura kamar ta dan rame duk da ba sanin ainihin kamanninta ya yi ba"ina yini"tace still kanta na qasa,cike da qasaitarsa da izzarsa ya dauke kai ya maida mata gaisuwarta da tambayar jikinta,da sauqi ta fada cikin sassanyar muryarta data sanya yaji wani dan yam ajikinsa Bata zata ba bata kuma tsammata ba sai jinsa tayi zaune kan kunerar da take kai.kuma dab da ita ya sanya bayan hannunsa a wuyanta da niyyar jin temperatures din jikinta ba komai aransa,sai dai baisan illar da ya sake yiwa fadila ba a zuciya da gangar jikinta ba,kasala mai tsanani tashi guda da kuma wani irin shauqi taji ya saukar mata numfashinta ya tsaya cak na wucin gadi,sam bai kulaa ba yace"still jikinki da ragowar dumi ya kamata ki warke kafin isowar abokiyar zamanku right?ya qare maganar da sigar tambaya,ya.miqe yana cewa babu abinda kike buqata,tamkar ta ce masa"kai nake buqata aliyyu ka qarashe awoyin wannan daren naka tare da ni,maimakon haka sai ta sake gyada masa kai,yace " alright gudnyt"ta bishi da kallo idanunta fal cike da qaunarsa da kewarsa har ya fice daga part din nata ya rufe mata part din,ta koma da baya ta jingina jikinta da kujerar hadi da runtse idanunta hawayen dake maqale a idonta suka gangaro mata wani radadi da zugi zuciyarta ke mata lallai kishi masifa ne Cikin daren bacci gagararta yayi juyi take kawai akan makeken gadonta cike da sha'awar aliyu tunda take bata taba jin makamanciyar sha'awa arayuwarta irin wannan ba Sannu a hankali ta miqa dukkan lamuranta ga Allah cikin ikon sa kuwa ta fara samun sauqinsu saidai fa har yanzu babu sauqi ta bangaren soyayyar Aliyu dake maqare cikin zuciya ,cikin lokacin sam ta daina bari idanunta suga aliyyu duk da tarin zugi da zullo da zuciyar keyi na son ganin nasa amma ta danneta Cikin lokacin aikinta ya samu freedom da express din duk suka buqaci yin aiki tare da ita,ya ahmad dinne ya kawo.mata da kansa bayan ya sanar da aliyu da kansa ya kuma amince mata da fara aikin nata,tayi murna tayi tsallae tun a gaban ya ahmad din ya sha godiya sosai har da qwallar farinciki saboda yadda take masifar son aikin jarida shikam dariya yayi yace Allah zata godewa,bayan tafiyarsa ta kira farida dake fama da laulayi suka sha murnarsu tare,nan fa ta zauna ta soma tsarawa kanta yadda zata tafi da rayuwar aikinta Cikin satin Aliyu ya shirya musu fita wadda ta farko ce agun fadila don bata taba fita ba wani gu da sunan unguwa ba bayan shopping da suke zuwa duka qarshen wata za suje ne gaida hajiyarsa Tun rana fada ke zumudin fitar tana tunanin mai zata kaiwa momin,akwatunan lefenta dake shaqare da kaya wadanda kamar ba'a taba amfani da komai a ciki ba ta bude ta zabi turarurruka designers guda uku ta warewa abba,ta duba akwatinta da ta adana gift da ta samu na biki ta cirarwa momin atamfofi super Holland da England guda biyu,da kanta ta aiki yaron dake musu gyaran flowers ya samo mata kilishi mai kyau da zuma Tun magariba ta yi wanka ta shirya kanta cikin atamfa dinkin riga da zani kamar light grean da milk sai ratsin baqi dinkin ya mata cas kamar a jikinta aka qirqireshi yari da sarqa ta saka ma dutse masu kalan milk sai farin agogon hannu tq zuba awarwaro mai 24 farare takalmi da jaka milk sai laffaya data nannade jikinta da ita milk ce mai adon baqi ta debi tsarabarta ta dawo falo ta kunna arewa 24 tana kallon shirin matasa at 360,tayi wani masifar kyau ta fito sosai a babarbariyar ta Ya qarashe karin hular sa yana daidaita ta a kansa shaddace fara qal a jikinsa dinkin tazarce sai walwali take ta sake fidda sirrin kyawunsa mutum ne shi ma'abocin iya ado ta wannan fannin kam ko mace haka ta ganshi,komai nashi fari ya sanya hatta da agogo,ya sanya glass dinsa sanna fesa turarensa ya rufe sashen Bangaren samirah ya nufa wanda sai ta kama dole yake shigar sa,ga mamakinsa aai ya taddata sirshan tana zaune abinta zaninta da rigarta daban daban kanta da ta tsefe shi yana tsaitsaye kamar tabarya dama ita ba wani tsawon gashi gareta ba sai qarfi da gashin yake da shi,ba abinda falon keyi saiqarnin kifi sardine ta tara gwangwanayen a gabanta ua daurw yadda qarnin ke bugar hancinsa yana tayar masa da zuciya cikin bacin rai yace mata zaman me kikeyi baki shirya ba tun dazun?ta dan yatsina fuska tace qawatace wlh ta kiarani a waya ta kwasheni da jira ya gyara tsaiwarsa cike da qosawa da azababben qarnin kifin yace mata is ok sai ki nemi wanda zaku tafi tare kinsan bana jira yana kaiwa nan ya sanya kai zai fice yana jan tsaki cike da takaici ,ta yi saurin shan gabansa tana cewa haba sweet kayi haquri mana pls ka bani minti uku kaya kawai zan canza,ya kauce ya fice yana cewa wataqila idan kinyi sauri kin tadda ni kafin in ciro mota is ok,ya barta nan baki a sake ta bishi da kallo sai kuma ta zabura tayi cikin daki don ta shirya Knocking taji anayi don haka ta zira hill shoes dinta fari ta rataya jakarta ta dauki ledarta don jikinta ya bata aliyu ne shi dinne kam idonsa na bisa screen din wayarsa yana danne danne bai dube ta ba ya juya taja part din nata ta kulle tabi bayansa tana qare masa kallo"ya gaji da haduwa"ta zanta hakan a ranta,tana jingine da rumfar ajiyar motoce har ya gyara parking qa'idarsa ne indai tare zasu fita baya neman driver duk da dama nasiru ne kawai.ke driving dinsa,wanni dogon hirn ya ja da sauri ta daidaita nutsuwarta ta nufo motar tun kafin ta qaraso taji an bangaji kafadarta da mamaki ta dago don ganin waye samirah tana ta zuba sauri zani a hannu tana gyara daurinsa,duk saurin da take gidan gaba aahe takewa,abun ma sai ya baiwa fadila dariya ta saki murmushi Cikin mintuna da basu gaza talatin ba suka qaraso gidan,harabar gidan tsaf kuma fetal da haske ba kowa sai mai gadi shi da wasu mutum biyu zaune kan benci suna sauraron duniya tumbin giwa suna cin gyada jefi jefi suna taba hira,cikin girmamawa ya gaida aliyu sannan ya gaida su fadila ta amsa masa fuska a sake tunda dama da yar sanayya tsakaninsu ya samirabko kallo bai isheta ba bare tasan yana yi,ya dage masa get din ya wuce ya yafitoshi yayi masa ihsani kamar yadda ya saba shi da wadanda ke zaune a gun suka hau zuba godiya abinsa shi kuma baiso Samira da aliyu suka jera suka fara yin gaba zuwan falon gidan fadila bin bayansu tayi ,sumayya da rabi'ah ne zaune a falin da hijabai ajikinsu da alamar sallar isha'i suka idar,suka juyo suna amsa sallamar sannan suka miqe tsaye cikin farin ciki suna gaida su hankalinsu na kan fadila itama su take kallo suna gaisawa sabanin samirah da ta riqe qugu tana qarewa falon kallo tana yaba tsaruwa da dukiya da ya lashe kamar wadda aka bawa kwangila sannan daga bisani ta zabi kujerar da tayi.mata ta zauna akai,cikin dakiya irin ta babban wa yake tambayarsu ina momy sumayya tace tana sama ya nufi benan taku biyu uku sukayi kacibus da iftihal na saukowa kamar yadda ta saba ta tsugunna ta gaidashi sanna ta daneshi ya sabeta a kafada yana tambayarta momi Tare suka sauko shi da momin yana take mata baya iftihal na hannunshi ganin fadila ya sata ta zille ta diro ta nufeta a guje cikin murmushi fadilan ta tareta ta dora ta bisa vinyarya dukkaninsu suna dariya ta gaisheta,duskar momi washe da fara'a take.musu barka da isowa samira dake zaune dare dare bisa kujera kamar tata tave yauwa fadila dama.na qasa ne kan carpet ta duqar da kanta qasa tana murmushi cike da kunyar momin,gaisuwa aukai da samirah kamar qawa da qawa yayin da fadila ma ta kasa hada ido da ita a haka suka gaisa,ganin taqi sakin jiki ya sa momyn tace su rabi'ah su kaisu dakinsu itama zata gun abbansu yanzu ya shigo gidan,hira suke abinsu da fasika yayin da samirah ta zaro wayarta ta hau danne danne tana ganin duk ta girmesu tafi qarfin zama cikinsu ai,ga takaicin yadda aujewa fadila haba haba itq aunqi mata haka cikin ranta take cewa hmm dangin miji kenan tsinannu(kunji fa?) A haka bacci ya dauki iftihal akan cinyar fadila aliyu ne ya leqo hukarsa a hannu yace ke sumayya ku taho dining"samrah ce ta fara miqewa tana cewa dama yunwa nake ji ta fice,qememe iftihal taqi kwanciya dole iftihal na nishi ta sabota a kafada suka fito su sumayya nata dariyar yadda ta dauki ifrihal din da qyar,momy ce da abba sai aliyu bisa dining din kusa da abban abba na dariya yaceyau ban dawo da wuri ba bare a murqushen tsohon qashi na shine aka rama akanki ko? Duk sukayi dariya kowanne ya samu kujera daya ya ja ya zauna banda fadila dake tsaye sabe d iftihal wani baccin nason daukarta amma ta qi yarda tayi don kada a sauketa Mrs muhammad ce Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Momy ta kalli aliyyu tace alii rabata da rigi mammiyar yarinyar nan don idan ba kai ba ba wanda zata yarda ya sauketa,ya miqe ya nufesu yanayin yadda ya tsaya gab da ita yana yunqurin karbar iftihal ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta,ya sa hannu zai dauketa cikin rashin sani hannunsa ya shafi qirjinta wani abu taji ya tsirga mata tun daga kanta har tafin qafafunta hakanan shima yaji tsigar jikinsa ta